Trending

BURINA COMPLETE BY Amnah El yaqoub

BURINA COMPLETE BY Amnah El yaqoub

BURINA COMPLETE BY Amnah El yaqoub

 

KARAAM !

Cikin sauri yadago golden eyes dinsa, wanda kallo daya zaiyi ma dasu ka rikice, kafita hayyacinka, musanman yanmata saboda tsabar kwarjininsa da kyau irin nasa, meyasa Abba zai kirashi da wannan sunan? Koya manta da matsayin mai sunan agareshi ne?

Ka tsareni da ido kana kallo na inayin magana, cikin sauri ya sunkuyar da kansa, saboda girma da tsananin biyaiyar dayakewa iyayen nasa

Hajiya juwairah dataga kamar alhajin yanajin shakkar yiwa karaam magana nan da nan tayi gyaran murya, taga alama alhaji kunyar sa yakeji, ita kuwa har gobe ganinsa take Kar, to me zaisa taji shakkar yiwa danda ta Haifa acikinta magana, akoda yaushe kallan yaro take masa

Kafin tayi magana Sai Abba yabata mamaki wajan fadin

Karaam ko bakada lafiya ne in shiga duniya da kaina in nemama magani? Kokuma insa anema Maka? Meyake damunka ne?

Kallan mahaifan nasa yayi, alamar bai Gane inda maganar tasu ta dosa ba

Ganin haka yasa hajiya juwairah tace, yau shekarka shida da aure, inban manta ba kana 28 years mukayi Maka aure, gashi har kun shekara shida har yanzu bamuji wani labari ba

, shine muka yanke shawarar yima ka magana muji idan bakada lafiyar Tarawa da iyalinka ne, sai mu bada umarni anemo Maka magani karam

Taqarasa maganar idonta cikin nasa

Ya Allah, Wai meyasa suke kiransa da wannan sunan ne? Bayan sunsan dacewa bai saba dashiba

Cikin sauri yasauke Dara daran idanunsa qasa daya Gane inda zancan nasu yasa gaba

Keyarsa yafara sosawa da key din hannunsa, cikin qasaita da birgewa yafara yiwa iyayen nasa magana

“Am… Abba ni lafiya ta kalau, kawai Allah ne bai kawo ba, Amma Ina bakin kokari na, Abba BURINA a duniya shine inyi abinda kukeso “

Yanda yake maganar cikin shagwaba hakanne zaisa mai karatu yaji aransa cewa kode shi kadai ne awajan iyayensa? Kokuma tsabar hutu ne da Jin dadi yasa shi wannan maganar

Abba ya daga Kai sama, kawai de yana jinsa ne, Amma maganar tasa ta kunnan sa na dama take shiga tafita Ana hagu

Domin shi har yanzu aransa bai yarda karaam yanada lafiya ba

Hajiya juwairah aranta tace ga mutum har mutum, Amma ace har yanzu tsawon wannan lokacin bashida magaji

Itafa dande tasan babu yanda za’ai mace tabawa kanta ciki ne, tasan dole wannan aikin danta ne, daba hakaba da tuni tasashi ya yankarwa matarsa red card

Haba wannan masifa har Ina

Jijjiga kafarta takeyi, wanda ta kasance daya Akan daya

Tace shikkenan tashi kaje, zamusan abin yi

Cikin gentle yatashi ya tattara wayoyinsa da car keys dinsa yafita, iyayen nasa suka bishi da kallo

Gumi Abba yafara, duk da esin dasuke zube acikin qayataccen falon nasu, yakai dubansa ga hajiya juwairah itama hakan take awajanta, yagane hakanne ta hanyar wuyanta, domin kuwa hamshaqiyar sarqar gold din dake wuyanta ruwa ne ya mamayeta

Yace hajiya Yaya zamuyiwa yaron nan ne?

Nannauyar ajiyar zuciya ta sauka tace alhaji kawai inaga agwada nema masa maganin, Dan Naga alamun in muka daka tatasa har jaki zaiyi qaho bamuga result ba

Abba yace hakan za’a yi

    ***     ***     ***

Garin bauchi qaramar hukumar ALKALERI

Mai girma Abdallah karaam, Dan asalin Garin ne, anan yataso yayi karatun sa dakomai, inda yasamu tarbiya daidai misali daga wajan iyayen sa kafin Allah yayi musu rasuwa, har Allah ya hadashi da hajiya juwairah sukai aurensu na soyaiya, ta kasance itace danginsa, domin kuwa Bayan rasuwar iyayensa kowa watsi yayi dashi, government school yayi, Bayan ya kammala digirinsa na farko, mahaifan hajia juwairah suka tsaya masa kaida da kafarsu yafada harkar siyasa

Yariqe maqamai da dama ta fannin siyasa

, wahalar daya fuskanta a rayuwa itace tasashi yin adalci Akan harkokin siyasar sa, domin kuwa yaji abin babu dadi

Sosai yake da temakon talakawansa, hakanne yasa yayi farin jini afadin nigeria  baki daya

Bai Bata lokaci da fara mulki ba, yakoma cikin bauchi da zama, har Allah yabashi muqami na governor of bauchi state, yanemi iyayen hajia juwairah dasu dawo bauchi dazama, Amma sukaqi amincewa, acewarsu sunyi masa temako ne saboda Allah

Ahaka harda gama tenure sa, inda suka ci gaba da zama abauchi shida iyalansa,

Bayan wani lokaci iyayen hajia juwairah suka rasu

Hakan yasanyasu acikin damuwa, ganin basuda wani gata Sai Allah, wannan dalilin ne yasa suke da mutuqar San yara, Allah Allah suke Allah yabawa karaam yara nagari

Saide kudin da maigirma Abdallah yake wadaqa dasu yasa hajia juwairah daukar ita din wata ce, ta manta da baya, mace ce mai izza da son nata, inde Akan yaran tane to fa zata iyayin komai

Amma a bangaren maigirma Abdallah bahaka abin yakeba, shi mutum ne na mutane, kowa nasa ne, talaka Dame kudi duk Abu daya yake daukarsu, wannan dalilin ne yasa jama’ar Garin bauchi har yau basu dena mararinsa ba

Basuqi ace yadauwama yana kan karagar mulki ba

Yayansu uku rak adunia, Anty mufeeda, tana aure agarin Abuja, inda ta auri Dan wani attajirin Dan kasuwa, suna kiranta da anty mufy, batada matsala da kowa halinta kamar na ubanta, kowa natane, tanada faram faram da jama’ah, shekaru dayawa dayin auren ta, Amma danta daya, tasa masa sunan qaninta karaam Ana kiransa da junior

Sai karaam, wanda yaci sunan kakansa, suna kiransa da daddy, miskili ne na gaske, saikayi Zaman 30 minutes dashi Amma maganar sa batafi biyu ba, hadaddan gaye ne nabugawa ajarida, bayasan qazanta, Koda yaushe yana cikin qamshi

Sumar kansa kullum tana sheqi saboda tsabar kudin dayake kashe mata

Karaam ya hadu qarshe, dangaye ne na gaske ,fatarsa mai kyau ce, wankar tarwada ne, Amma hutu da Jin dadi yasa yazama fari, yanada dogon hanci, da Dan qaramin baki, idanunsa daidai misali ne

Yayinda yake da yalwar gashin Gira, bangaren tsawo kuwa karaam ba gajere bane, yana tsayi, haka hannayensa a mummurde suke, Koda yaushe idan yana gida safe da yamma to gym yazame masa wajibi

Kullum cikin motsa jiki yake

Yayi karatu sosai, yataka matakin masters degree saida yahuta sannan yayi phd dinsa a fannin medicine

Cikekken doctor ne, but  baya aikin komai, kawai a zaune yake yana hutawa

Hakan ne yasa mahaifinsa yasakashi cikin har Kar siyasa Shima, Amma tunda yayi sanata

Bai qara marmarin siyasa ba, daga nan ya watsar yake hutawarsa, domin kuwa shi bayasan hayaniya, Shide barshi yazauna yana daddanna waya abinsa

Kuma iyayen basu yi masa maganaba Akan hakan, ko me ne dalili oho

tun yana 28 years iyayen sa, suka hadashi aure da wata yar minister mai suna salma

Suna San junansu sosai babu laifi

Yanzu yana  34 year’s Amma Ba haihuwa babu alamar ta, hakan ne yasa hankalin iyayensa yatashi, saboda su Allah yadora musu kaunar yara, tunda basu dasu gaba dayansu familyn bawani yawa ne dasuba

Shima yana zaune acikin bauchi shida matarsa salma, but gidansa yana kusa da gidan iyayen sa, wanda idan kika shiga bazakice anahiyar Nigerian kikeba

Sai yar auta Shahida,batajin magana, tsaf takwaso halin momynsu hajiya juwairah, duk samarinta manyan guy’s ne, kullum tana cikin yawo da qawayanta, Bata ganin mutuncin mutum taka kowa take son ranta, kuma hakan yasamo asali ne da daurin gindin data samu awajan momy juwairah

Farace sosai, tanada doguwar face, hips dinta yan dede, batada kayan Sawa daya wuce Riga da wando, da wahala ka ganta da atamfa

 

DANNA DOMIN SAUKEWA AKAN WAYOYINKU👇
BURINAHH CMPLT

 

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE