Ayshat Ɗansabo LemuINA DA HUJJA CHAPTER 2 BY

Lokacin da Khairiyyah ta dawo tun daga ƙofar shiga gidan na su ta ja ta tsaya.Tana sauke manyan idanun ta akan ƙatuwar motan da ta gani fake a ƙofar gidan su.Tsana nin mamaki take yi tare da jin bugun zuciyan ta na sauyawa,tsora da fargaba na mamaye zuciyan ta.Ta shiga jan ƙafafun ta da taji sun mata nauyi tana takawa zuwa cikin gidan na su,zuciyan ta na ayyana mata wasu irin baƙi ne su kai da su ka zo a cikin irin wannan ƙatuwar mota haka?

Tana sanya kanta cikin zauren su ta fara jiyo maganganu ƙasa-ƙasa na baƙin muryoyin da bata sani ba,hakan ya sa ta ɗaga ƙafa ta shiga cikin gidan bakin ta ɗauke da sallama,idanun ta suka sauka akan dattijon mutumin tare da wata mace a gefen sa wacce ita ma da alama shekaru sun fara tura mata,Inna ce ta amsa sallaman da tayi yayin da mutanan duk su ka waiwayo su na sauke ganin su akan Khairiyyah,wacce tayi saurin risinawa tana gaida su cike da ladabi.Suka amsa da tsananin sakin fuska bata sake jiran komi ba ta nufi ɗakin Inna ta shiga,da Aliyu ta fara yin tozali kwance bisa kuzajjiyar doguwan kujeran da suka mallaka a ɗakin,kansa naɗe da bandeji fuskan sa ya haye yayi suntum da kumburi.Wani faɗuwan gaba ta ji ya same ta ta isa kusa da shi da sauri tana faɗi a fili “Subhanallah! Aliyu me ya sa me ka haka?”

“Tsautsayi ne ya sa me sa Khairy,waɗannan mutanan da kika gani ne suka kaɗe sa abakin titi akan hanyan sa ta dawowa gida,Allah ma yasa mutanan ƙwarai ne da har su ka tsaya su ka dubi raunin da yaji har su ka kai shi asibiti.”

Inna ce me wannan maganan tana isa kusa da inda Aliyu ke kwance tana sake duba shi,Khairiyyah cike da alhini da tausayin ƙanin na su ta dubi Inna Salamatu tana faɗin “Allah sarki Aliyu Allah ya baka lafiya,kaman na san ba lafiya ba ina ganin mota a waje naji gabana ya faɗi.”

Sallaman Malam Lawal da shigowan sa cikin ɗakin dogare da sandar da yake doddogarawa ne ya hana Inna sake magana,ya dubi Khairiyyah yana faɗin “Mamana kinga tsautsayin daya sami qanin ki ko?Allah ma ya taƙaita da iya rauni ne kawai yaji babu karaya,kuma Allah yasa mutanan kirki ne suka kaɗeshi,da wasu ne yadda zasu gansa mara galihu sai suyi tafiyan su ba tareda sun tsaya ba.Amma wannan dattijon arziƙi ne da alama daga shi har me ɗakin sa sun san darajan ɗan adam.”

“Hakane Malam nima mutanan sun birgeni,dubi yadda su ke ta faman bamu haƙury,Allah dai ya saka musu da alkhairy ya kiyaye gaba.”

A tare Khairiyyah da Malam su ka amsa da “Ameen.” Malam ɗin na sanya hannun sa cikin aljihu ya zaro kuɗi masu yawa yana faɗin “Kinga abinda Dattijon ya bayar Salamatu yace a sake siya masa magani.Hakika Allah me rahama ne ga bayin sa ta hanyoyin da ba su yi zato ba,tabbas wani tsautsayin sai ya janyo maka alkhairy.Ungu Mamana irga kiga nawa ne kuɗin.”
Yaƙare maganan da miƙawa Khairiyyah kuɗin wacce tuni ta cire Hijab ɗin jikin ta tana zaune a ƙasa kusa da kan Aliyu,ta amshi kuɗin fuskan ta na bayyana farin cikin ta ita ma da samun waɗannan kuɗi.

“Laaah! Malam wallahi har naira dubu goma ne kuɗin.”

Khairy tayi maganan cike da tsana nin mamakin yawan kuɗin,murmushin farin ciki na sake bayyana akan kyakykyawan fuskan ta,suma dukkanin su da alama sunyi mamakin yawan kuɗin,Malam ya amsa yana me zama a bisa ɗaya kujeran one seater dake ɗakin yana duban Inna yake faɗin “Masha Allah,Allah mun gode maka da wannan ni’ima daka kawo mana,abinda za’ai yanzu Salamatu zaki tashi kuje nan kasuwan tudun wada ke da Mamana ku gwado mana kayan abinci dai-dai misali da duk wani ɗan abin da mu ke da buƙata.”

Inna ta gyaɗa kai cike da ƙaunar mijin ta,daya kasance ba shi da wani buri irin ya gansu cikin wadata da walwala,shiya sa har gobe ba ta nadaman kasancewan sa miji kuma uban ƴaƴan ta duk da babun sa,domin tayi imani talaucin da suke ciki jarabawan su ne ita da shi domin da zafin nema yana sa a fita daga ƙangin talauci tabbas da tuni sunyi hannun riga da ba bu tunda daɗewa,domin Malam mutum ne shi me zafin zuciyan neman na kansa da yin duk wani aikin ƙarfi don yaga ya rufa musu asiri sunfi ƙarfin ci da sha da sutura zuwa karatun yaran sa bakin gwargwado,amma da yake haka Allah yaso ya gan su babu yadda su ka iya.Ta sauke a jiyan zuciya tana faɗin “To shikenan Malam bari mu hanzarta da ma gashi rana ta fara yi ba tare da mun san abinda za mu ci ba,amma ka ɗauki koda naira dubu biyu ne ko dan siyan maganin ka.”

Yadda tai maganan cike da narke murya alamun magiya yasa Malam Lawal sakin ƙayataccen murmushi,ƙaunar matan sa na sake huda jinin jikin sa,tabbas ya sani samun mace haƙurarriya me ɗinbin tawakkali da haƙuri da ba bu irin Inna Salamatu sai an tona cikin wannan xamanin,bata taɓa nuna masa gajiyawa da halin da su ke ciki ko tai masa gorin talauci ba,sai ma yadda take aiki da jikin ta da lafiyan ta don a taru a rufawa juna asiri.Ya dube ta cike da ƙauna yana faɗin “Karki damu Innan su ku je da kuɗin duka ba sai na ɗauki komi ciki ba,sai dai Khairy ta ɗauki kwalin maganin can sai ku siya mun kwali biyu,sauran kuɗin ku siyo duk abinda ya dace,zaman mu babu abinci ba ƙaramin ɗaga min hankali yake ba,ina baƙin cikin mu wayi gari ba mu da abinda za mu ci,amma bakomi Allah na sane damu kuma ina da yaƙinin zai kawo mana mafita cikin rahaman sa da tausayin sa ga bayin sa,kuyi maxa ku je ku dawo ɗin.”

Kusan a tare Inna da Khairiyyah su ka miƙe don cika umurnin sa,su kai masa sai sun dawo su ka fito sanye da Hijaban su a jiki,tafiya su ke su na tattauna matsalolin su da yadda rayuwa ke gara mu su,Inna na sake kwantar ma Khairiyyah da hankali tana nuna mata muhammancin haƙury akan duk halin da bawa zai tsinci kansa a ciki watarana zai wuce,ya zama tarihi har su ka tari a dai-daita sahu su ka shiga kafin su kame bakin su bayan sun sanar da ɗan sahun inda xasu sauka.

Bakin gwargwado sun siyo kayan abincin da zasu ci,wanda a ƙallah zai mu su kaman kwana huɗu zuwa biyar,cike da farin ciki su ka dawo gidan su ka ajiye komi a inda ya dace bayan sun zube kayan Malam ya gani ya sama siyayyan albarka,tare da yin addu’an fatan alkhairy ga wanda ya basu kuɗin.

Koda Aliyu ya tashi daga bacci Inna ce tai masa wanka ta gasa masa jikin sa,Jallof ɗin taliya da suka dafa ta kawo gaban sa ta aje bayan ta sanya masa kaya,da kanta ta ciyar da shi Khairiyyah dake gefe riƙe da magungunan sa da ta ɓallo ta miƙa masa tana masa sannu,bayan ya shanye maganin sai Inna tace ya ɗan zauna har abinci yabi jikin sa sai ya sake kwanciya.

Ƙarfe huɗu Khariyyah ta fito cikin shirin tafiya islamiyyah,ta sanya Maroon ɗin Hijab wanda shi ne matsayin uniform na islamiyan,sosai kalan yake mata kyau matuƙa,kafaɗan ta rataye da jakan littafan ta,taima su Inna sallama ta fice su na mata fatan dawowa lafiya, a ƙasa take xuwa islamiyan kasancewan basu da nisa can ƙasan layin su ne,tafe take tana jin nishaɗi a cikin zuciyanta,tana tsananin son karatu(Both) boko da islamiya kuma Allah ya bata ƙwaƙwalwan ɗaukan karatun,tana da masifan ƙoƙary a hadda da islamiyan na su,shiya sa malaman ke alfahary da ita,lokacin da suka fuskanci matsalan school fees na son kawo ma karatun Khairiyyah matsala sai suka yafe mata biyan kuɗin makarantan baki ɗaya,hakan ba ƙaramin faranta ran Khairiyyah da iyayen ta yayi ba,Malam da kansa ya je har makarantan yai ma malaman godia.Yanxu matsalan dake damun Khairiyyah yana cin xuciyanta bai wuce matsalan rashin cigaban karatunta na boko ba,gashi har ana dosa shekara guda,wannan tunanin da tayi ne ya rage walwalan ta,haka dai ta ke takawa sannu a hankali har ta karya kwanan da zata ɗauki hanyan makarantan direct,idanun ta ta sauke akan ƙaton gidan da aka gina cikin watanni uku kacal,gini ne na gani na faɗa wanda kaf anguwan dama sauran layukan dake gaban su babu gida kwatankwacin sa,tun da ake ginin duk wanda ya zo wuce wa sai ya tsaya ya kalla bare kuma yanxu da aka kammala komi tarewa acikin sa kawai ya rage wa ma su shi,gini ne da ta sha ji mutane na faɗin irin na ƴan Abuja ne,idan tace gidan baya birge ta to tabbas ta yi ƙarya shi ya sa duk sanda zata wuce ta gaban gidan sai ta tsaya ta morewa kallon sa,tana tasbihi ga Allah daya yo ma su arxiƙi da marasa shi,tana cikin ƙarewa gidan kallo ne taji an dafa kaɗun ta ta baya,cikin sauri tayi saurin waiwayowa idanunta na sauka akan Ruƙayyah Sulaiman.Wacce ta kasance Qawa a gun ta kuma maƙotan juna da suke abin arziƙi,kuma aji ɗaya suke a Hadda da Islamiyya baki ɗaya.Ganin Ruky ce hakan yasa Khairiyyah sakin bayyanan nen murmushi cikin muryan ta da yake a narke cike da ƴar shagwaɓa ta ke faɗin “Kai Ruky Sulaiman kinfa so tsorata ni.Ina nan ina kallon aljannan duniya sam bana gajiya da ƙarewa gidan nan kallo,da alamu mamallakin gidan nan ba ƙaramin dukiya ya tara ba.”


Ruky ta dubi Khairiyyah itama tana sakin murmushi,tare da kallon gidan tana faɗin “Tabbas kam yana da kuɗi sosai a yadda naji su Yah Kamal na labari,sun ce ma wai nan da sati biyu masu gidan zasu tare anan za su yi azumi har zuwa sallah shi da iyalin sa.”

Khairiyyah ta jinjina kai tana faɗin “Masha Allah to Allah sa su zame mana maƙwabta na gari,don ni lamarin masu kuɗin yanzu yana bani tsoro yadda sam babu tausayin talaka da sanin darajan sa a zukatan su inba za su bautar da shi bane.”

Yadda Khairiyyah tayi maganan cikin tsananin raunin murya,yasa Ruky sake jin tausayin su ya kamata.Ta sani duk da suma talakawan ne amma sau dubu sunfi su Khairiyyah wadata tun da su dangin mahaifin su suna taimakon su akai-akai,ba kaman su Khairy bane da basu da kowa a garin sai Allah sai wanda ya dubi Allah ya tallafa musu.Har su ka jera su ka isa islamiyan na su ba su daina tattaunawa akan halin masu kuɗin yanxu ba waɗanda da yawan su basa son taimakon talakawa.

Ƙarfe Six na yamma aka tashe su still tare da Ruƙayyah suka jero zuwa gida,gida uku ya raba tsakanin gidan su Ruky da na su Khairiyyah,sun zo daf da ƙofar gidan su Ruky su ka tsaya su na sallama da juna,Ruƙayyah ta dubi Khairiyyah tana faɗin “My Khairiyyah idan an taso skull gobe zan zo ki ɗan kwashe min kaina,daga nan kawai sai mu wuce Islamiyyah tare zan taho da shiri na.”

Khairiyyah ta zabgawa Ruƙayyah harara tana faɗin “Ai tun da na ji yadda kika karya murya wajen kiran sunana na san zancen kitso ne,to shikenan Allah ya kaimu goben lafiya ki gaida Guggo.”

“Zata ji Khairy ke ma ki gaida min Inna.”

Cewan Ruky tana shigewa gida ita kuma Khairy ta kamo hanyan zuwa gida,zuciyanta cikeda kewan karatun ta na boko data rasa,wasu hawaye taji na son taruwa mata tayi saurin maida su tana tuna nasihan Malam a gare ta “Khairy ki miƙa lamuranki ga Allah tare da gode ma ni’iman sa gare ki,ki sani kinfi wata gara ke kin kai matakin aji a aakandiri ɗin,sannan kika tsaya.Kin iya rubutu da karatu hatta ɗan turancin nan kina ji kin kuma iya shi bakin gwargwado,wasu na nan cikin duhun jahilci na babu Arabi ba Bokon,ke kuma duka Allah yai miki ni’ima da samun su bakin gwargwado,don haka ki gode masa idan da rabon zaki cigaba sai ki ga Allah ya kawo wani hanyan.”

Tunanin ta ya katse ne a lokacin da ta iso ƙofar gidan su,ta sauke ajiyan zuciya tana jin zuciyan ta na yin sanyi a duk sanda take tuna irin rarrashi da Nasihan Malam a gare su,tana sake jin ƙaunar sa na sake ratsa zuciyan ta.

Da Yah Ahmad suka kusa gwabza karo zai fita,tayi saurin ja da baya tana faɗin “Sorry Yah Ahmad.”

Ya balla mata harara yana faɗin “Allah ya shirya ki Khairy mutum yai ta tafiya baya kallon gaban sa.”

Tasaki dariya tana raɓa shi ta wuce zuwa cikin gidan…..✍

Muna maraba da masu son a tallata hajar su sai ku nemi wannan line ɗin don neman ƙarin bayani 08167768704.

Ga masu son yin payment tunda wuri zaku turo kuɗin ku ta wannan asusun 0504192664 Aisha Ibrahim Ɗansabo GTbank.

Shaidan biyan ku tanan line ɗin 08167768704.

Tsarin biyan kaman yadda na sanar kashi biyu ne,masu son samun updet sau biyu a rana zaku biya 500,masu son updet kaman yadda aka saba sau ɗaya kune zaku biya 300 only .

Masu turo katin waya zaku turo na MTN ta wannan line ɗin 08167768704 shaidan biyanku ma ta line zaku tura.

Shatu Ɗansabo ce 

DOMIN KARANTA CI GABA DANNA

https://arewabooks.com/book?id=62b735ad7f7fce1c0ba4d533

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE