KUNDIN KADDARATA CHAPTER 9 BY HUGUMA

Mukhtar!,mukhtar!!,hmmmmm” haka ta fadi sannan ta maida murfin food flask din ta rufe tana ci gaba da dariyarta cike da nishadi da jin dadi. A hankali ya zare jikinsa,cikin tafiya ta sand'a kamar yadda yazo haka ya koma,bakin gado ya zauna ya dafe kansa da dukkan hannayensa biyu,zuciyarsa na rawa saidai baiso ya bata dama,oh Allah!,tun yaushe?,tun yaushe ya fara turawa kansa wannan qazantar?,me ya samu yaya yahanasu ne har udanunta suka rufe ta kai ga nannade hannu zata jefashi ramin halaka?,me ta gani ne wai gun fa'iza ya burgeta har ta nemi suyi tarayya wajen hada zuriyya. Sallamarta ta katse masa zaren tunaninsa,ya daga kansa wanda idanunsa suka kada jazur ya dubeta,tayi ado yau cikin shadda koriya sgar,bakin nan ya sha jan jambaki tamkar ya digo,zai iya rantsewa da Allah yau ne karo na farko da zai iya cewa ya ganta tayi wata aba mai suna kwalliya tun bayan qare kwanakinta bakwai na amarci. Wani kwarkwasa na musamman yau din take masa,wanda dai dai da qwayar zarra bata qara farashin qaunarta cikin zuciyarsa ba face rageta ma da tayi,haushi takaici da baqinciki suka cika shi amma yayi namijin qoqarin dannewa

“Sannu da zuwa yaya mukhtar,yau kam ka jima baka shigo ba,Allah ya sanya lafiya” ta fada tana zama dab da shi tare da kashe masa ido,tausar zuciyarsa yayi don yana son ya ga gudun ruwanta,don idan baka iya kama b’arawo ba shi sai ya kamaka,tsawon zamansu duk iya inda ya kai darensa indai ba a dakin sumayya bane to shi ta shafa bata da damuwa,koda wasa bata taba tambayarsa ba
“Lafiya lau” ya fada yana miqewa tsaye,sai ta dubeshi gabanta na faduwa tana fatan ba asarar aikinta zai mata ba yau ma dai
“Ina zuwa yaya mukhtar gashi na shirya maka abinci?”
“Wanka zan shiga nayi” ya fada bayan yayi kamar bazai amsa mata ba,ta miqe tana fadin bari ta hada masa ruwan wanka sai ya dakatar da ita kan ta jirashi. Kai tsaye dakin sumayya ya shiga,tana kwance saman doguwar kujera hannunta riqe da wayarta tana kallon wani film 'DAN KUKA,dariyarta take mai sanyi a hankali cikin nutsuwa,ya jima tsaye kanta yana dubanta cike da qauna da burgewa har sai da ya sanya hannunsa ya zare wayar sannan ta miqe a firgice tana ambaton

“Bismillahi,hasbunallahu wa ni’imal wakil” sai suka hada idanu,ta shagwabe fuska cikin muryar shagwaba tace
“Kai yaya mukhtar wallahi ka tsoratani” girarsa qwaya daya ya dage mata
“Eh amma naji dadi da kika ambaci sunan Allah yayin da kika tsorata din,haka akeso” murmushi ta danyi,duban screen din wayar yayi ya tsayar da film din,cikin shagwaba shima yace
“Wato yau ko ki nemeni ko my sumy?,hala ma kin daina damuwa da ni,kina nan kina kallonki kina ta dariya abinki bayan bakiji shigowar sahibinki ba ko?”idanu ta zaro tare da dafe baki sannan daga bisani ta hade hannayanta guri guda alamar roqo
” ka yimin afuwa don Allah,wallahi kewarka ce ta dameni shi yasa ma kaga ina rage lokaci da kallon,ai kasan yaya kallo ba damuna yayi ba ko?”ta qarasa maganar da sigar yarinta,idanu yasa yana kallonta sosai,babu shakka yana daya daga abinda ke sake rura qaunarta cikin zuciyarsa wannan shagwaba da quruciya tata,murmushi ya sakar mata
“Na miki sumayya ta,ai baki laifi a gurina” ya fada yana miqa mata wayar tate da cewa
“Zan shiga wanka”
“A fito lafiya ranka ya dade”
“Allah yasa my sumayyata” ya fada sannan ya juya ya fice yana murmushi. Kai tsaye sif dinsa ya wuce ya fidda jallabiya ya saka tana ta faman zuba masa surutu,ko daya bai kula ta ba sai sabgarsa ma da yake,har ya kammala ya zauna. Cikin hanzari ta jawo abincin gabansa tana fadin bari ta zuba masa,idanu ya zuba mata harta kammala ta dago ta dubeshi suka hada idanu,signa ta masa sannan tace

“Gashi ya mukhtar sai ci ko”
“Qwarai kuwa” ya fada yana janyo abincin gabansa,fatanta daya kawai taga ya sanya koda loma guda bakinsa ne,hakan ya sanya ta bata dukka lokacinta yau ko girkin rana batayi ba cikin gidan ta tsara masa abincin da tasan yafi so. Kamar ta sume don dadi sanda taga ya kai loma guda bakinsa sai kuma ya dakata ya ajjiye cokalin ba tare da yaci din ba,ya dubeta ya sakar mata wani murmushi

“Yau tare da ke nake sha’awar muci abincin,matso bismillah” tamkar an sanya guduma an doki qirjinta haka taji amma tayi hanzarin mazewa ta girgiza kai
“Haba ai ba girmanka bane,baka ne kai kadai” idanu ya zaro
“Au bakison samun matsayi kenan irin na sumayya bayan naga shi kike ta fafutukar samu maza matso,na saba tare muke cin abinci da ita duk ran girkinta” sai ta wani kamme ido a dole sai ta ja ra’ayinsa
“Haba muntari wannan ai ba tarbiyya bace,miji na diba kema na diba,kaci kawai ni a qoshe ma nake” kafada ya daga alamun rashin damwa daman ya san da kwanan hakan
“To shikenan,ba damuww,bari na kira sumayyan ta tayani ci” kamar ta tashi ta riqo shi haja taji amma don kada ta bada kanta sai ta dake. Daga bakin qofar dakinsa ya coge ya kirata don kada ma ta samu damar sauya masa abincin,cikin mintuna qalilan sumayyan ta shigo dakin,kallonta yayi cikin salo na burgewa

“Yayarki ta qi tayani cin abinci shi yasa na gayyatoki ki tayani” sai ta danyi jim duk da murmushin da ta sanyawa fuskarta,ta sani cewa suna hada kwanon cin abinci ne kadai idan ranar girkinta ce. Matsowa yayi da kwanon da sauri gabanta don kada ma ta musanta masa

“Oya,matso mana” da sauri fa’iza tayi tsallen albarka ta dira gabansu,ta sanya hannu ta rufe abincin,cikin daurw fuska tace
“Nifa gaskiya bana son haka,wannan ai bai kamata ba,ni ina shiga sha’aninku ranar kwananta ne,to nima ban lamunta ba girki kai daya na yiwa shi kuma kai zakaci” kallonta yake a nutse tsaf riqe da habarsa kamar yadda sumayyan ke kallonta,murmushi ya aje cikin nutsuwa
“Ikon Allah,to aikam nima ban yarda ba cikin biyu dole ki zabi daya,ko ki tayani ci ko my sumy ta tayani” ya fada yana sareta da idanunsa. Take gumi ya yanko mata,ta fuskanci idan batayi da gaske ba wankin hula zai iya kaita dare,kafin ta kai ga cewa komai nepa suka kawo wuta,haske ya wadaci dakin,ba bata lokaci fuskar fa'iza ta bayyana,wadda tuni gumi ya yiwa jikinta sharkaf,ganin yadda suke kallon gumin ya sanya ta fara nade tabarmar kunya da hauka,wadda ta sake tonawa kanta asiri tsaf a gun mukhtar din ba tare da ta sani ba

“Lallai muntari,to me kake nufi?,kana nufin baka yarda da ni ba kenan?,ko kama nufin wani abu na zuba maka a ciki?”
“Ni bance kin zuba wani abu ba,amma tunda kika fada din akwai qamshin gaskiya cikin lamarin” miqewa tsaye tayi zata nade tabarmar kunya da hauka
“Lallai ma muntari,sharrin da zakamin kenan,sharrin d’a namijin da ake fada kenan yau yazo kaina,eh lallai ba shakka” tsawa ya daka mata ganin zata masa hauka ya miqe tsaye. Kallon fuskarsa tayi ta tabbatar babu rahama a cikinta,take tsoro ya dirar mata abu ya hadu kuma da rashin gaskiya,sai taja da baya ganin yadda yayi dab da ita har tana jin hucin numfashinsa,tana niyyar guduwa ya damqi hannunta har da taji azaba har tsakiyar kanta

“Fa’iza!” Ya kira sunanta a matuqar kausashe,hantar cikinta ta kada tamkar zata saki fitsari a wandonta
“Basai na bata lokacina nayi doguwar magana da ke ba,wallahi wallahi duk ranar da kika sake yunqurin zuba min wani abu mai kama da sihiri ko surkulle sai kin raina kanki,ki kuma tabbatar daga ranar sunanki SAKAKKIYA!” ba qaramin dukan qirjinta kalmar tayi ba,sam bata koda sha'awar jin wata kalma makamanciyar haka daga bakin muntarin,don ko kusa bata marmarin komawa gidansu wanda yake mata daidai da gidan kurkuku,gidan da talauci yunea babu masifa da rashin tarbiyya ya yiwa katutu. Sakar mata hannu yayi cikin rawar jiki ta juya zata fice don baya da abun cewa,yanayinsa kadai ya tsoratata,balle ko shakka bata yi tasan cewa ya ganta ne muntarin,tsawa ya kuma daka mata ya bata umarnin ta dawo ta kwashe abincinta tasan yadda zatayi da shi baya da buqatar sa,haka ta kwashe kwanukan jiki na rawa ta fice.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE