JIDDATULKHAIR CHAPTER 27 BY KHALISAT HAIDAR

Jiddah ta langwabar da kanta tace “Ai ban sani ba, in dai mata na xuwa sai mu dinga tafiya tare” That wasn’t were Abuturrab wanted the conversation to end, but because of how cautious he was with time sbda sllhn juma’ah, ya kalleta kawai yace “Kafin in dawo masallaci ki tabbatar kin sake wanka kin shirya cikin atamfa, sannan ki karya…” Sae kuma ya hade rai, Ta sauke idonta kasa tace “Ni na karya da asuba ai” Daga sama har kasa ya kalleta sannan ya juya ya fita ta bi sa da kallo…. Ko da ya dawo juma’ah har ta shirya kamar yanda yace mata, Hijab ya sa ta daura kan atamfar, bayan ta sauko ta tsaya tana kallonsa, sau daya ya kalleta ya dauke kai yace “Fita ki jirani a waje” Ba musu ta nufi kofa ta fita daga parlon, sae a sannan ya tashi ya kashe appliances din gidan ya dau makullin motarsa da hulansa ya fita, the ride was silent har suka iso gidansu, gaba daya he was absentminded, yau da safe ma kiran Aunty ne ya tashe sa, har sannan kuma ya ki daukan kiranta, then is he even suppose to go home now? bai yi parking a kofar gidansu ba in case of necessity, ya juya yana kallon Jiddah yace “Ki jirani” Bai jira tace komai ba ya bude motar ya sauka…. Da murmushi Abuturrab ya amsa gaisuwan mai gadinsu ya shiga cikin gidan, sosai ya ji hankalinsa ya kwanta da kanninsa suka ce Aunty ta fita, Yana kallon Ramlah yace “Ina ta tafi?” Ramlah tace “She left for Abuja this morning” Shiru yyi yana kallonta, can ya nufi parlon Umminsa, ganin bata parlon ya fito, ganin ya nufi kofar fita Ramlah tace “Ummi na bedroom fa” Bai tanka ta ba har ya fita, tare ya dawo cikin gidan da Jiddah, murmushi kawai tayi ma su Ramlah da suka gaisheta, ta bi bayansa xuwa parlon Mahaifiyarsa, kafin yace mata komai ta xauna a kasa, ya karasa cikin bedroom din Ummi da sallama, gaisheta yayi da ladabi, ya shafa kansa yace “Ummi xa ku gaisa da ita a parlor” Ummi tace “Ohkk” Mikewa yayi ya fito parlon, ya xauna kan kujera, ba a dau lkci ba Ummi ta fito, jiddah ta sunkuyar da kanta ta gaisheta, Ummi ta amsa da murmushi fuskarta tace “Ya ku ke?” jiddahh tace “Lafiya lau” Ummi tace “To madallah, sannun ku da xuwa” Ummi dake kallonta kasa kasa ta ga ta canxa mata sosai, haskenta na ainahi ya fito ga wani glowing da take yi, Shi dai Abuturrab danna wayarsa kawai yake, jin Umminsa bata kuma cewa komai ba ya daga kai ya kalleta yace “Ummi wai Aunty ta tafi Abuja?” Ba tare da ta kallesa ba “Ai na xata xaka fi kowa sani tunda kun fi kusa” Ya sunkuyar da kansa yace “Aa bamu yi magana ba” Ummi tace “Ayyo” yace “Yaushe tace xata dawo?” Ummi tace “Baka da lambarta ne?” bai kuma cewa komai ba kuma bai dago ba, Jiddah dai sai kallon Ummi take, Bayan few seconds Abuturrab ya dago yace “An kawo lefen Ramlah ne?” Ummi tace “Bakwa magana da Ahmad din ne?” Yace “Shekaranjiya mun hadu a Abuja da na sauke jirgi a airport din can” Da sauri Jiddah ta kallesa, suka hada ido ya hade girar sama da ta kasa yana kallonta, turo baki tayi, Ummi dai tv kawai take kallo, Ya dauke kai yace “Amma yace min xai shigo kadunan yau, kilan xanje daukosa a tashan jirgi anjima” Ummi tace “Allah ya kawosa lafiya” yace “Ameen” Ummi tace “Idan kaga xaka iya sai ka bar ta nan har bayan bikin, tunda ranan talata xa su fara shagalgulansu” Abuturrab ya d’an yi shiru, can ya daga kai ya kalli Ummi yaga kallonsa take, suna hada ido tace “Ranan bikin sae ka kawota” Da sauri yace “Aa Ummi gobe xan kawota tunda bata xo da kaya ba” Ummi tace “Aa a bari ranan bikin dai” Yace “Uhn xan kawota goben in sha Allah” Ummi tace “Baxa ka siya mata ankon bikin ba?” Ya d’an yi shiru, sai kuma yace “Nawa ne?” Ummi tace “Kala uku ne, daya na family, sai general one da xa a saka ranan yini, sai kuma na dinner, although naji yan matan sun fidda wani da xa su saka ranan talata” Yace “Nawa ne duka” Ummi ta hada masa kudin gaba daya tace “Gaba daya 40k ne” Yace “A dinke xa a siyo kayan?” Ummi tace “Ehh, da yake kayan dama a kyauta aka samosu daga kasuwa, iyakar kudin dinkin ne dubu arba’in” Abuturrab ya bude ido ya fara dariya yace “Ummi tambaya fa kawai nayi” A takaice tace “Nima amsa na baka” Ya shafa kansa yana murmushi bai ce komai ba” Ummi na kallon Jiddah tace “Su Ramlah na can daki kije ki samesu tunda naga baki son magana” Tayi murmushin karfin hali ta mike ta nufi kofa, Abuturrab ya mike yace “Ai bata san dakin ba, i will back Ummi” Da ido kawai Ummi ta bisa da kallon mamaki har suka fita. Dakinsu Ramlah ya kai ta, Ramlah na xaune da Siyama sai wata kawarta da Aisha step sis dinta, tana ganin Jiddah ta mike tana welcoming dinta da fara’a, bai amsa gaisuwan yan dakin ba banda na kawar Ramlah da bai sani ba, sannan ya juya ya fita ya koma bangaren Umminsa….

Karfe hudu saura yace da Ummi xai je dauko Ahmad a train station, Ummi tace “Toh Allah ya tsare” Yace “Ameen” Daga haka ya fita daga parlon, dakin su Ramlah ya nufa, Jiddah na xaune tana ma Siyama tsifa, su Ramlah suna ta labari a dakin ganinsa duk suka yi shiru, yana kallon Siyama yace “Ke tsifan sai an maki??” Tayi dariya tace “Ita tace ta xata min Yaya” Yana kallon Jiddah yace “Kinci abincin ko baki ci ba?” Ramlah tace “Yanxu muka gama cin abincin fa yaya” Wani kallo ya jefa mata yace “Nayi da ke?” Bata kuma cewa komai ba, yana kallon Jiddah fuska daure yace “Tambayar ki nake” Tace “Mun ci” juyawa yayi ya fita, Sai da Ramlah ta tabbatar ya tafi don har sai da taje ta d’an bude kofar taga babu kowa wajen sannan ta dawo tana kallon jiddah da murmushi tace “Yaya yana ji dake kamar yanda yake ji da profession dinsa…” Jiddah dai bata ce komai ba ta ci gaba da tsifar da take…. Bayan kusan awa daya da tafiyar Abuturrab Aunty ta dawo gidan, alamar dai ita ma train din ta biyo daga Abuja ta dawo, tun da ta kyallara ido taga Jiddah taji kamar taga mugun abu a gidan, ko gaisuwar Jiddah bata amsa ba, bata sake shiga damuwa ba sai ganin wani haske da kyan da Jiddah tayi alamar kwanciyar hankali, ita Abuturrab xai raina ma wayo?? Ta kusa minti ashirin xaune gefen gado a dakinta, ta saka wannan ta kunce wnn, ita Abuturrab ke son kunyatawa gun aminiyarta? Takanas ta shirya yau ta tafi Abuja ba mahaifiyar Aneesah hakuri bayan sun sanar mata abinda Abuturrab din yyi ma Aneesah a airport kamar yanda Aneesan ta gaya ma uwarta… Wani murmushi Aunty tayi tana gyada kai. Jiddah na ta xaune parlorn Ummi ita kadai don su Ramlah da yan matan gidan sun fita xuwa gun tailor, Ummi kuma ta hanata bin su tace mijinta bai sani ba, Jiddah na ta juya furucin Ummi a kanta, wai mijinta, ai ba mijinta bane Aliyu, tunanin hakan kawai sai taji jikinta yayi sanyi sosai, Ummi ce ta fito daga dakintaz ganinta xaune ita kadai tace “Ki shiga kitchen kiga ko aunty na ciki ki tambayeta abinda xa ki kama mata Jiddah” Jiddah ta kalli Ummi a hankali tace “Toh” Mikewa tayi ta fita bangaren Ummi, tayi hanyar kitchen din, jikin kofa ta tsaya tana lekan kitchen din don ita har taji tana tsoron matar nan da ake ce ma Aunty, ganin Auntyn a ciki, cikin sanyin murya tace “Aunty me xan kama maki wai?” Juyawa Aunty dake yankan cabbage tayi tana mata wani irin kallo tace “Me xa ki kama min?” Jiddah ta gyada mata kai gabanta na faduwa, Aunty ta ajiye wukan hannunta ta kunduma mata xagi tace “Ke a wa xaki kama min aiki?? Yanda kika samu wajen xaman yin iskanci gidan Aliyu kin xata nan ma haka ne, toh bari kiji… Wllh ki saka a ranki cewar xamanki ya xo karshe a gidan Aliyu, sai dai ya dinga bin ki can kauyen naku yana iskancin da yake dake, yau xai san ni mahaukaciya ce wllh” Jiddah dai kallonta kawai take a ranta tana kara nanata kalmar da ta jefa mata wai iskanci, tana nufin iskanci suke yi da Aliyun kenan? Muryar Aunty ya sake dawowa da ita, ciki tsawa tace “Baxa ki fita ki bar min kitchen ba mayya….” Cikin sanyin murya Jiddah tace “Ni ba iskanci muke yi ba wllh….” Aunty ta fixgi roban cabbage din gaba daya ta watsa mata ranta bace ta kunduma mata xagi tace “Kina shige da karuwar xaki ce min ba iskanci ku ke ba, dama mace da namiji na xama gida daya tare babu aure? Fita ki ban waje kada in fasa maki ido algunguma” Jiddah da ta rufe idonta da hannunta taji kuka ya taho mata ta juya da sauri ta bar kitchen din jikinta duk cabbage da suka makale, dai dai nan Abuturrab ya shigo parlon, durkusawa tayi nan parlor ta fara kuka kamar an aikota, kallon hanyar kitchen din yayi yaji muryar Aunty tana cewa “Sai yanxu na ke sake yarda cewar da gangan yayi komai da ya faru, har sabida ke xai walakanta min Aneesah, to in dai nice wllh xai sha mamaki, ba mu xai kawo ma gayyar tsiya family ba…” Karasawa yayi gun Jiddah ya dagota, kuka kawai take ya kakkabe jikinta ya kama hannunta suka fita parlon, nan balcony ta saka takalminta sannan suka fita compound xuwa gun motarsa, har suka bar layin kuka take kamar xata shide, ya hade rai yace “Ya isheki haka nan, me yasa baki tsaya kitchen din kin mata kukan sosai ba?” Bata ce komai ba ta hade kanta da gwiwa tana shessheka, har suka isa gida hawaye na xuba idonta, bayan yyi parking yana kallonta yace “Baki ji ki daina kukan ba?” Ta dago kai cikin rawan murya tace “Ce min tayi wai muna yin iskanci fa” Ya dinga kallonta kafin yace “Da wa ku ke yin iskancin” Cikin kuka tace “Wai kai” Dauke kai yayi da farko, can ya juyo yace “Ai ban san wani irin iskanci take nufi ba” Tana hawaye tace “Tace iskanci muke yi da kai a gida” Ya buda ido sosai yace “Toh fa, ni iskancin da na sani shine ace mutum bashi da kirki ko baya jin maganan mutane…” Da sauri Jiddah tace “Ba shi bane” Yana kallonta yace “Toh wanne ne?” Cikin rawar murya tace “Kilan ta xata kana ta6a ni” kallonta ya dinga yi, can ya kai hannunsa ya kamo nata yana caressing dinsa gently yace “Haka take tunani?” Da sauri Jiddah ta janye hannunta ta saida kukan tana kallonsa, ya daga kafada yace “Don an kama hannun mutum shine iskanci?” Ta girgixa kai tace “Tayi tunanin muna kwana a daki daya” Yace “A kano ba a daki daya muka kwana ba? Sai ace wannan iskanci ne” wasu hawayen suka sauko mata tace “Aa ba haka ba” Yace “Toh ya ne?” Tana goge idonta tace “Tana tunanin muna kwana waje daya” Yace “Toh me ake yi idan an kwana waje daya da ake kiransa da iskanci” Kin cewa komai tayi, ya bude motar ya sauka, ya nufi cikin gidan, bude motar tayi ita ma ta bi bayansa tana goge idonta, Tun da ta shiga dakinta bata fito ba har bayan isha, ita iskancin da Aunty tace take yi ne ya tsaya mata har da ce mata karuwa, wanka kawai tayi tasa rigar baccinta ta shige cikin duvet da ta tuna sai taji hawaye ya taho mata. Karfe tara ya bude kofar dakinta, duk da tana ji bata motsa ba, ya isa inda take ya bude bargon, suka hada ido hawaye ya gani idonta, yace “Ohk kukan kike yi har yanxu kenan” ta gyada masa kai wasu hawayen na taruwa idonta, yace “Saboda ance kina iskanci kike kuka har yanxu” ta mike xaune ta hade kanta da gwiwa tace “Toh ni ae ban ta6a iskanci da kowa ba” yana kallonta yace “Toh ae gwara kawai kiyi ki san kinyi ko?” ta dago kanta da sauri tana kallonsa, ya rungume hannunsa shi ma yana kallonta, tace “Inyi iskanci fa kace” yace “Ehh, ko hakan xai sa abun ya daina damunki, kinga kinsan kinyi kenan ko an fada baxai maki ciwo ba” Ta wani ja gefe daya ta hade rai tace “Allah ya kiyaye ni ba yar iska bace” Dariya ta basa, amma bai yi ba, yace “Amma ko jiya kin kama hannuna ai” da sauri ta juyo a tsorace tace “Ni??” Yace “Ehh” ta hade rai ta hararesa tace “Ni ban ta6a haka ba wllh” karasawa yayi daya side din da take yace “Ni kike harara haka?” Saukowa tayi da sauri ganin ynda ya hade rai tace “Ni ban harareka ba wllh” Ya fixgo hannunta tana ganin haka ta rufe fuskarta a jikinsa tace “Don Allah kayi hakuri ni ban harare ka ba” daga sama har kasa yake kallonta, ya d’an rufe ido sae kuma ya rungumeta tightly to himself yace “Yanxu me ake kiran wannan?” Kwace kanta take son yi amma ta kasa yana jin ynda xuciyarta ke bugawa kamar yanda nasa ma ke bugawa, lkci daya kuma ya saketa, ta juya da sauri ta bar wajen, a mugun tsorace ta juyo tana kallonsa, ba tare da ya kalleta ba yace “Kinga maganar Aunty ya fito, don haka idan tace kina iskanci kada ki sake damun kanki tunda gashi har rungumeni kika yi ynxu, ko bayan wannan akwai wani abu da ake kira iskanci?” Juya masa baya tayi xuciyarta na bugawa sosai, daga sama har kasa ya dinga kallonta, riga ne da wando red color na bacci a jikinta rigar ce kadai barrier din skin dinta, dauke idonsa yyi ya nufi kofa ba tare da ya kalleta ba yace “Ki sakko kasa ki dau abincin ki, kuma kar ki yrda in dawo baki sakko ba” daga haka ya fita, ta bi sa da kallo har sannan xuciyarta na bugawa, bayan kusa minti goma sbda tsoron kada ya dawo kamar yanda yace, ta dau Hijab dinta a sanyaye ta saka har kasa sannan ta sauka, kanta a kasa ta shigo parlon, ta durkusa jikin kujera taki kallonsa a hankali tace “Ni ba yunwa nake ji ba, naci abinci a can gidan” Yace “Koh?” Bata ce komai ba, kuma bata dago kanta ba, ganin ya mike ita ma ta mike da sauri tana kallonsa, da alamar ta tsorata da shi, dariya ta basa amma ya fuske yace “Ohk, da ni mijinki ne haka xaki dinga yi idan na ta6a ki??” Ta kasa ce masa komai, yace “Ki bani amsa” Ba tare da ta kallesa ba tace “Toh ai kai ba mijina bane” Kallonta kawai yake yi, can yace “Toh amma mijin na ki baxa ki dinga yi masa haka ba ko” A takaice tace “Nima ban sani ba” yace “Dauki abincin ki” tace “Na koshi” yace “To tafi” juyawa tayi ta wuce sama, ya bi ta da kallo, xaunawa yyi ya jinginar da kansa jikin kujera, daga karshe ya dau wayarsa ya kashe wutan parlon ya wuce sama xuwa bangarensa ya kwanta, Aneesah ya shiga kira, sai da ya kusa katsewa ta daga amma bata ce komai ba, yyi lumshe ido yyi kasa da murya yace “I know i did what is uncalled for, but… I hope u aren’t among d set of pple that believe ban saketa ba ko?” Tace “How will i believe you Aliyu bayan abinda ka min a kanta jiya?” Ya kwantar da murya yace “What if na auroki kika shigo gidan kika gani ma idonki cewar ba matata bace?” Tace “Then i will believe u 100%” Yace “Ranan juma’ah daurin auren Ahmad, kafin uncles dinmu su koma xa a kawo gaisuwa da kudin saka ranan gidanku ranan lahadi in sha Allah” Kamar xata yi kuka tace “Are you for real Aliyu?” Yace “Sure” Farin cikin da Aneesah tayi a lkcn baya misaltuwa, lkci daya duk ta mance abinda Aliyu yayi mata jiya, amidst d joy yace “I am missing you seriously, vid call?” Tace “Sure, amma kar ka wani kashe wuta” yace “I have to” bai jira cewarta ba ya katse wayar ya kashe switch din dake kusa da gado sannan ya shiga kiranta vid call…. Washegari Abuturrab na dawowa masallaci ko azkar bai tsaya yayi ba ya dawo gida a stairs suka kusa cin karo da Jiddah xata sauka kitchen, da sauri ta juya masa baya don bata sa hijab ba, bata yi xaton shigowarsa a lkcn ba, ta koma sama da sauri ta shiga dakinta, bangarensa ya nufa ya shiga daki ya kashe wuta ya kwanta. Kiran Ummi ne ya tashesa wajen karfe takwas da rabi, ya jawo wayar a hankali ya daga coz she’s been calling him since yesterday har ma da Aunty, ya kai kunne hade da sallama, Ummi tace “Don walakanci Jiya ka dawo ka tafi da Jiddah babu sallama??” Ya mike xaune da sauri yace “Ummi yau xan kawota dama, bak’i nayi a gida…” ummi tace “Good!!!Abbanka na nemanka, kuma ka taho tare da Jiddar, ba jiran ka xai yi ba, karfe goma xai fita yace” Daga haka ta katse wayar, sosai ya ji gabansa ya fadi, Abba calling him for what? Kallon agogo ya sake yi sannan ya ajiye wayar ya lumshe idonsa yana jin xuciyarsa na bugawa, bayan minti goma ya mike ya shiga bathroom. Tara da minti goma ya fito daga bangarensa cikin kananun kaya, ya tsaya bakin kofar jiddah for some seconds kafin ya bude kofar a hankali, gyaran daki ya sameta tana yi, ta sunkuyar da kai, ganin ta shirya yace “Dauko hijab din ki” Daga haka ya juya ya fita, karasa gyaran dakin tayi sannan ta sa hijab din ta fito. Throughout the ride hankalinsa baya jikinsa, sai da yaga sun kusa gidan ya kalleta rasa abinda xae ce mata yyi har suka shiga gidan, parlon Abba ya nufa direct tana biye da shi a baya, yana sallama aka yi masa izinin shigowa, shi ya fara shiga sannan ta shiga, Aunty na xaune parlon tare da Ummi da Umma, kamar dai xuwansu ake jira, ya ji gabansa ya fadi sosai, xaunawa yyi kasa, jiddah ta xauna side dinsa a hankali, ita ta fara gaishesu cikin sanyin murya sannan shi ma ya gaishesu, Abba gaisuwanta kawai ya amsa, yana kallon Abuturrab babu yabo babu fallasa yace “For how long have u divorced her Aliyu??”

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE