ALLURA CIKIN RUWA BOOK 2 CHAPTER 6 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA

Inuwa mai dafa musu abinci ya shirya mani abinci bisa tebir, na ci na yi hamdala, sannan nabi lafiyar gado. Ban tashi ba sai zuwa karfe biyar.

Na sami Mama a falo muka gaisa, ta ce,

“Wai! Yau dai za mu huta da wayar Aliyu, kusan kullum sai ya bugo”

Na yi murmushi na ce, “Wallahi ban gane kan makarantar bane shine dalilin rashin zuwa na kamar yadda.na ce Mama Inki ta yi dariya ta ce, “Kin san halin kayan naki shi ba haka zai dauka ba, gani yake kina son mantawa da shine”

Na ce, “Kai Mama”

Ta ce, “Ya ya kina ganin Abubakar ko?” Na ce, “Na ganshi kamar sau biyu”

Mun dade muna hira sai ta ce, “Gara ki kira

*Aliyd ko hankalinsa ya nutsu”

Yan mintoci kadan na sami Aliyu, na ce,

“Hello!”‘Sai na ji muryar Aliyu nan da nan na canja

” múrya na make ta na kuma riqa magana cikin harshen Turanci.

Aliyu ya ce, “Wa ake nema ne?”

Na ce, “Aliyu”.Ya ce, “Daga ina ne?” Na ce, “Daga Kaduna”. Ya dai ci gaba dayi mani tambayoyi na neman sani, da na tabbatar bai gane ba yana neman ya yi sallama ya aje sai na kyalkyale da dariya na ce,

“Aliyu Asiyarka ce”.

[the_ad id=”5409″]

Shima ya yi dariya ya ce, “Asiya kin latsa ni na latsu, ya ya makaranta?”Na ce, “To sai a ce babu laifi.”

Ya Ce, “Come on my baby, kar ki yi saurin

karaya mana tun yanzu”Na ce,

., “Gaskiya na fara karaya, amma kuma

ba wai karatu ne ke- ban wahala ba, sai dai tunanin gida da rashin aboki. Har yanzu ba ni da Kawa wadda jininmu ya hadu balle in ji sanyi-sanyi rashin Hadiza”

Don Allah kada ki damu, wadannan

abubuwan haka suke, amma idan kin gane rayuwar Jami’ a abu ne mai dadin gaske da zarar kin sami aminiya shi ke nan, haka nan kuma har yanzu karatunku bai fara zafi ba” Na ce, “Eh haka ne”

Ya rika bani labarin abubuwan da ke faruwa a bangarensa, har ya ce ya yi “yar rashin lafiya, amma® bai kwanta asibiti ba. Muka yi dan barkwancinmu na masoya, a karshe muka yi sallama.

Ya ce,Insha Allah zai aiko mani dasu”. Ya

kawo kudi ya ce, in bai wa Yaya Abubaka. Muka yi sallama suka nufi cikin gari.

Bayan dawowa ta Kaduna kamar da kwana tara, wata rana mun fito aji da safe, ina zaune bisa dogon benci a wajan cin abinci da kwalbar fanta a hannuna ina sha, na harde kafata daya bisa daya, a wannan rana atamfa ‘yar Holland ke jikina da aka yiwa dan dinkin mai shef, ga takardar gwadawarmu ina dubawa, na ci maki takwas da rabi cikin goma (8/10%), sai na ji wasu hannuwa masu sulfi da kamshi sun rufe mani ido ta bayana.Mamaki tare da jin dan tsoro ya kama ni, na yi tunanin ban san wanda zai yi mini wannan aikin ba, na daure na ce, “Ko wane ne na ba da gari” Sai aka kyalkyale da dariya, ta ce,Madam Asiya”

Na yi sauri na waiwaya, na ce, “Ranki shi dade Zahra’u, sai yau Allah ya hada mu’ Ta ce, “Wai ma ke za ki ce haka, sau nawa ina yada zango dakinku ba ni samun ki sai wata miskilar mata, ke kuwa ko kallo dakinmu bai ishe ki ba”

Na yi dariya na rasa amsar da zan ba ta,

 

domin a nawa ganin Zahra’u ta fi karfina. Ina tsoron kada gaba in yi dana sani, amma sai na daure na

kawo mata rashin lafiyar da na dawo na sami Yaya

Abubakar a ciki, kusan ita ce dalilin rashin ganina

dakinsu.

Zahra’ u ta zauna daf dani yayin nan ne ta amshi sauran fantar da ke hannuna tana sha tare da duba•

takardata, a nan na kara saki da al’amarin Zahra’ u.

Ta ce, «To in saurare ta anjima idan mun tashi

da la’asar don mu je duba jikin Yaya Abubakar”.

Na amsa mata “To”

Mun gama “yan ciye-ciyenmu sannan muka

rike hannun juna muna tafiya zamu azuzuwanmu, ita

Zahra’u tana karanta fannin koyarwa ne.

A wannan satin kam ayyuka sun cunkushe

mana cikin ajinmu kusan mu talatin da shida, mu mata daga ciki goma ne sauran maza ne, a cikin goma din

nan kuma mu uku ne Hausawa.

A ture ta yabon kai jahilci, ina ganin a yadda

abubuwa ke gudana na dauki kwas din da ya yi daidai dani, har yanzu ban ga abin da ya tayar mini da hankali ba balle abin da ya gagare ni.

Na yi wanka na kwanta ina sauraron zuwan

Zahra’u, zuwa can sai ga ta, na tashi zaune ita kuma ta zo ta zauna tare da dora hannayenta bisa cinyata, ta dubi Mary John wadda ke zaune tana linke kayanta tare da rera wakar da ta saba, Zahra’u ta gai da ita, amma ba ta amsa ba sai dai kawai ta daga mata hannu.

Zahra’u ta duba gefen dirowata tana kallon wani hoton Aliyu da na lika, ta ce, “Kai Asiya kina faman zama da wannan mata”

Na ce, “Kema dai kin gani Zahra’u, duk ba wannan ne damuwata ba irin wakokin, idan ita bakinta ba shi gajiya, to ni kunnena na gajiya”.

: Zahra’u ta ce, “A bamu hotuna mu sha kallo”.

Na fiddo mata album dina, tana kallo ina shaida mata mutanen ciki, ta ga Zainab autarmu da Yaya Abubakar, sannan Yusuf, sar Hadiza da sauran Kawayena.

Yayin da ta tashi magana sai ta fara da nawa da na Aliyu, ta ce, “Kai wannan dai shi ne angon ko? Ana dai ji da shi, ina sunan shi?”

Na ce, “Aliyu kuma danki ne, saboda sunan mahaifiyarsa Fatima Bintu”.

Ta ce, “Yauwa na ji dadi, kin ga yanzu duk

‘yan ayyukana ke zan rika bai wa*

Hmmm

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE