INA DA HUJJA CHAPTER 3 BY Ayshat Ɗansabo Lemu
*Misalin ƙarfe tara na dare su na zaune ne gaba ɗayan su a waje,su na shan iska kasancewan sun samu sun kunna maganin sauro a ɗakunan su,wanda Ahmad ne ya siyo shi ganin yau ɗin sun samu wadatan da suka aje komi na kayan abinci,ɗan kuɗin daya dawo dashi ne ya siyo maganin sauro ya aje ragowan zuwa safiya sai ayi anfani da sauran kuɗin wajen karin kumallo.
Cike da nishaɗi su ke hiran su banda Aliyu da akai ma shinfiɗa yana kwance,yana sauraron su da alamu bakin surutun ya mutu murus sabida raunin da yaji dake damun sa.Ƙaraman wayan Malam data gama jin jiki ne ta ɗauki ruri,ya miƙa hannu ya ciro sa daga aljihun gaban rigan sa,yana duba sunan me kiran, Karimatu shine sunan daya gani a rubuce kaman yadda a kai saving, hakan yasa shi danna ok ya kanga wayan a kunni bakin sa ɗauke da sallama,bayan sun gaisa ne ya miƙa wayan ga Inna yana faɗin “Gata nan kusa dani ma ungo Salamatu,Karimatu ne.”
Ya ƙare maganan yana ƙarisa miƙawa Inna wayan,ta amsa fuskan ta ɗauke da fara’a jin cewa yayarta ce me kiran,ta kanga wayan a kunni tana faɗin “Salamu alaikum Yayah Karimah.”
Daga haka suka shiga gaisawa ni dai ba na jin me Karimatu ke faɗi,tun da ba’a hands free aka saka wayan ba,na dai ji Inna ta saki salati, kafin su cigaba da maganan da zai kai minti biyu.Su kayi sallama da juna ta miƙama Mallam wayan,yana yin fuskanta na sauyawa zuwa damuwa,Malam ɗin ya amsa wayan idanun sa akanta yana karantan tsantsan damuwan dake shinfiɗe bisa kyakykyawan fuskan ta,cike da kulawa yake faɗin “Ince dai ko lafiya naga fuskanki da damuwa?”
Inna ta dube sa cike da damuwan tana faɗin “To lafiyan kenan Malam wai ɗan wajen Zainabu ne ya rasu yau kwana uku kenan amma an rasa me sanar dani,sai yau Yayah Karima ta tuna da ni ta kira don ta sanar min,wannan wace irin rayuwa ce muke ciki ace ɗan ƴar uwanka ciki ɗaya ya rasu amma akasa sanar dakai,har ayi kwana uku sabida dai kawai baka da shi,anya zumuncin wannan zamani zai gyaru kenan? In dai aka ce baka dashi shikenan kai da babu duk ɗaya ne cikin ƴan uwan ka,har da wanda kuka fito ciki ɗaya da su,ina takaicin yadda ake wofintar da zumunci ake nuna sai da me shi za’a dinga zumunta mara shi kuma shi da banza duk ɗaya su ke,Allah kasan da zaman mu kuma baka mance damu ba,ina roƙon ka daka bamu juriya da haƙuryn cinye wannan jarabawa da muke ciki.”
Inna takai ƙarshen maganan hawaye na sauka bisa fuskanta,wanda ko kaɗan ta kasa riƙe su ta bar su suna sauka ɗaya bayan ɗaya,zuciyanta na mata ciwo matuƙa idan tace bata ji zafin abinda akai mata ba tayi ƙarya domin uwa ɗaya uba ɗaya ya wuce wasa.Shiru ne ya ratsa na tsawan mintoci dukkan su babu wanda zuciyansa bai motsa ba,tausayin kan su da kan su na sake ratsa zukatan su,sosai abin ya doki Malam Lawal shi ma yana sake jin tsananin mamakin yadda ɗan uwa ke gudun ya raɓi ɗan uwan sa sabida talauci,haka nan shi ma yaji hawayen na sauka masa tunawa da yai da nashi dangin da yadda ƴan uwa suka juya masa baya har hakan ya zamo silan baro mahaifansa da yayi ya dawo Zaria da zama duk saboda gudun wulaƙanci da gudun zuciya.Cike da rarrashi yake baiwa Inna haƙury da kalamai na kwantar da hankali,ya ɗaura da faɗin “Idan an samu hali na kuɗin mota sai ku shirya ke da Ummul-Khairy ku je kiyi ma Zainabun gaisuwa,kin fita har a wurin Allah domin zakiyi sabida shi da kuma ƙarfin zumuncin dake tsakanin ki da ita.”
Inna ta share hawayen ta tana gyaɗa kai,daga haka sai Malam ya ɗakko wani hiran don kawar da damuwa a zuciyan Innan,Ahmad shi ne ya fara tashi yai musu sai da safe yana nufan hanyan ɗakin sa,zuciyan sa cike da tausayin iyayen sa da takaicin yadda dangin su suka wofintar da su duk don kasancewan su wanda basu da shi.
Khairiyyah wacce tai lamo tamkar bata wajen,itama ta miƙe tana ma iyayen nata sai da safe ta nufi ɗakin ta,zuciyan ta cike da tarin tunanika iri-iri,duk da ƙarancin shekarunta tana jin ciwan ganin iyayen ta cikin damuwa,tare da jin haushin yadda babu wasu dangin su dake zuwa wajen su sai tsiraru shima sai ƴan uwan su na ƙauye ne marasa shi irin su,amma mawadatan da suke ganin sun sama duniya sam babu ruwan su da su daga dangin Innan har na Malam ɗin.Lokacin data shige ɗakin sai Malam da Inna suka kalli juna tare da girgiza kai cike da damuwa,domin sun gane zuciyan yaran nasu ya sosu suma duk da ƙarancin shekarun su,Inna ne ta tashi Aliyu daya fara bacci suka nufi ɗaki don ta kwantar dashi.Shima Malam Lawal ɗakin sa ya nufa don ya sha maganin sa na dare ya kwanta.
Washegary da ƙyar Khairiyyah ta iya tashi tai sallan asuba,ta koma bisa katifan ta ta kwanta tana jin yadda maranta ke murɗawa,ga wani Zazzaɓi da take ji yana barazanan rufe ta,sannu a hankali ciwan ke ƙaruwa sosai,maran ta yai tsananin ɗaurewa yana murɗa mata da wani irin azaban ciwan da yau ne ta fara jin irin sa,juya juye ta fara bisa katifan ta tana salati tuni hawayen azaba sun fara wanke mata fuska,wani irin murɗawa maran nata yayi hakan yasa ta sakin ihun azaba da iya ƙarfin ta,wanda ihun nata Inna ta jiyo tana daga kitchen ta gama ɗaura musu ruwan da zata dama musu koko kenan a murhun gawayi,cikin sauri ta saki botikin hannun ta ta nufi ɗakin Khairiyyah,hango ta da tayi tana faman juyi bisa katifa hannun ta dafe da mara ya sata ƙarisawa gare ta cikin sauri tana tambayan “Lafiya Khairiyyah me yake damun ki ne?”
“Inna marata da ciki na,wayyo Inna zan mutu…!”
Cewan Khairiyyah a galabaice tana dafe da maranta dake katsawa da azaban da bata taɓa jin irin sa ba,sam ita bata ciwan ciki sam bata cika rashin lafiyan daya wuce ɗan Zazzaɓi ba sai ko mura,amma yau ciwan da take ji daban yake.Da sauri Inna ta isa gareta tana faɗin “Sannu Khairy kiyi ta faɗin Lahaula walaquwwata illah billah,Allahummah laa sahlan illah maja’altahu sahlan wa’anta taj’alul haznah izah shi’itah sahlan!Allah xai kawo miki sauƙi kinji.”
Khairiyyah dake faman kuka tana murƙususu ta kama nanata addu’an,har zuwa lokacin hannunta na dafe da maranta hawayen azaba na zuba daga fuskanta,Inna ta fice cikin sauri ta nufi ɗaki zuciyanta cike da tausayin halin da Khairiyyah ke ciki,domin tuni ta gane inda ciwan Khairiyyah ya dosa,alamu na cewa zata fara jinin al’adah ne yazo wanda ta daɗe tana hasashen zuwan irin wannan ranan tareda addu’an kada Allah yasa Khairiyyan ta gaje ta Don ita ma haka tai fama da matsalan matsanancin ciwan mara a duk lokacin da xatai jini,wanda har tayi haihuwan fari bata daina shan wahala ba sai da tai haihuwan Khairiyyan ne ta nemi ciwan ta rasa sai kaɗan,sai gashi da alamu addu’an ta bai amsu ba Allah yai nufin sai Khairiyyan ta gaji irin azaban da take sha,shigan ta ɗaki ta tadda Malam zaune bisa gado yana ganin shigowan ta ya furta “Salamatu ihun wa na jiyo kaman na Mamana?”
“Ba kama bace Malam itace,ta tashi ne da matsanancin ciwan mara da alamu girma yazo jini xata fara,tayi gadon irin ciwan maran da nake fama da shi ne,bari in haɗa mata wannan maganin tasha muga ko xata samu sauƙi.”
Inna tayi maganan tana nufan drawern da take ajiye ajiye,ta ciro kullin wani magani da ake kaɗawa da ruwan ɗumi a sanya zuma a ciki,ta fita Malam na faɗin “Ki mata sannu bara nima na fito naga jikin nata idan kin bata maganin abun bai lafa ba sai suje da Ahmad chemist ɗin Ustaz ya bata magani koda bashi ne,idan Allah ya hore sai abiya shi.”
Inna dai ta fice ba tareda tace komi ba,kitchen ta nufa don jira ruwan da ta ɗaura ya tafasa ta haɗa maganin.Lokacin da ta koma wajen Khairiyyah ɗauke da maganin cikin cup samun ta tayi ta durƘushe tana yinƙurin yin amai,cikin sauri ta isa gare ta tana aje cup ɗin a gefe ta dafa kan Khairiyyah tana mata sannu,a haka Malam ya shigo ɗakin ya same su cike da tashin hankali yake ma Khairiyyah sannu,kaɗan tai aman kasancewan babu komi a cikin ta,sai faman sauke numfashin wahala take,idon nan ya kaɗa yayi jajir sabida azaba lokacin da maran ya sake katsa mata saita cakumi zanin Inna tana fasa ihu tana birgima a tsakar ɗakin,faɗi take “Inna zan mutu,wayyo marana rai rabe biyu Inna…!”
“Kiyi salati da addu’a ne Mamana ba ihu ba zaki samu sauƙi da izinin Allah.”
Cewan Malam cike da tsananin tausayin ta,Inna ce ta miƙa mata cup ɗin maganin tace ta shanye maza ta bata cup ɗin,da yake ita bamai gudun magani bane cikin sauri ta shanye maganin tana dire cup ɗin,tare da kwanciya bisa cinyan Innan da tai xaman dirshan a tsakar ɗakin,tamkar an sake kunno wutan ciwan maran haka Khairiyyah taji bayan maganin ya fara aiki,haka ta dinga birgima tana salati har ihun ta ya fito da Ahmad daga ɗakin sa shi ma yazo ya ga halin da take ciki,cike da tausayin ta ya dubi malam yana faɗin “Malam ko xa’a kaita asibiti ne wahalan yayi yawa.”
“A kaita asibiti da wani kuɗin Ahmad? muyi haƙury dai insha Allah xai lafa mata maganin dama haka yake yi dole sai ta ji azaban ciwan ya taso,da zaran ta sake yin aman aka ci sa’a zaka ga ya faɗa mata ciwan,don dai karon ta na farko ne dole sai tayi haƙury.”
Cewan Inna kenan tana shafa bayan Khairy dake faman juyi a jikinta tana faman kiran xata mutu ,kafin wani ya sake cewa uffan Khairiyyah tayi saurin tashi daga jikin Inna tana yinƙurin sake yin wani aman,riƙe ta Innan tayi har ta gama amayar da ruwan maganin data sha ɗin,kamata tayi Ahmad ya taimaka mata suka fita da ita tsakar gida ya ɗibo ruwa yana zuba mata ta kuskure bakin ta,duk Inna na riƙe da ita don sam taƙi yarda ta miƙe sosai ma tace tana ji tamkar maran ta zai rabe ne gida biyu ne,haka Inna ta sake kama ta zuwa ɗaki ta kwantar da ita suna haɗa baki da Malam wajen mata sannu,gyaɗa kai kawai tayi tana lumshe idanun ta tare da sake kudundunewa,Inna ta gyara wajen da tai aman tas suka fita daga ɗakin ganin kaman ciwan ya lafa,kitchen Inna ta wuce don dama gasaran kokon da suka siya tun yamman jiya,a gidan me koko cikin sauri ta dama kokon ta zuba sikari ƙadan ta juya,a ƙaramin kofi ta zuba ma Khairy ta sake komawa ɗakin tana tashin Khairiyyah akan ta daure ta sha kokon da zafi-zafinsa ko hakan zai taimaka wajen sa jinin yazo cikin sauƙi,bayanin da Inna ke yi ne ya ankarar da Khairiyyah meke shirin faruwa,wani tsoro da kunyan Innan ne ya diran mata ta saki kuka tana juyawa Innan baya,bayan ta amshi kofin kokon tana kurɓa a hankali.Murmushi Innan tayi tana ficewa daga ɗakin cikin zuciyan ta take addu’an Allah yaba Khairyn lafiya yasa ciwan maran ya lafa kenan…✍
Ina masu son a tallata hajar ku muna maraba daku,sai ku tuntuɓeni ta wannan line ɗin don neman ƙarin bayani 08167768704
Wanda zasu yi payment tun yanzu zaku tura kuɗinku ta wannan asusun 0504192664 aisha ibrahim ɗansabo GTbank.
Shaidan biyanku ta nan 08167768704.
Kaman yadda kuka sani tsarin biyan kashi biyu ne,masu son samun updet sau biyu a rana zasu biya 500,sau ɗaya a rana kuma zasu biya 300 kaman yadda aka saba.
Masu turo katin waya zaku turo katin MTN ta wannan line ɗin 08167768704 shaidan biyan ku ma ta line ɗin zaku tura.
Shatu Ɗansabo ce
DANNA DOMIN KARANTA CI GABA