ARNE CHAPTER 18 BY Surayyahm.s
Komawa ciki raphael yayi dakinsa ,amma sai dai tun dayake bai tabajin abun Hajiya mariya ya taba masa zUciya kamar na Yau ba,,,,
jingina kansa yayi hawaye na tsilala a idanunsa…..
tunanin iyayensa yadda suka mutu agaban idonsa ya hadu ya chakudu masa da wulakancin da haj mariya ke masa……kuka sosai yafashe dashi a dakin nasa
Abunda Abba ya gaya masa ne ya fado masa arai yasa ya tsagaita kukan nasa ya lalubi laptop din dake dakin
Dan wani paper ya zare daga drawer sa wanda aka rubuta….the merciful servant, yaseen media production,the daily reminder,da kuma I lov u Allah production
Youtube ya shiga ya
rubuta the merciful servant, nan videos kala kala suka fara budo masa
,karanta wa ya tsaya yi yama rasa wanne zai Shiga yafara kallo…domin kuwa duk abunda yake nema na ilmi akan addini akwae a site din…..series by series
Masha Allah tunda kaamil yafara kallo duk wani tunani ya kauce masa
Ba abunda yamamaye zuciyarsa illah burin ya kara shiga Neman ilmin sanin ubangijin sa
Duk da ma malm mamman ya dauki nauyin karantar dashi qur’ani kullum in yadawo daga schl
amma bai daddara ba sanda yayi downloading dinsu cikin wayarsa saboda tun dama yana sa masa nitsuwa idan zafar yana yi a gabansa..
Da safe karfe goma Sha daya Hajiya ta shigo site din alhaji,ya idar da sallar walaha yana zaune yana tasbihi
Da sallamarta ta shigo ta zauna a kan kujera ,bayan ya kammala tace alhaji gani…..jiya bansamu na shigo ba gajiya tai min yawa
Bakomai mariya,gwanda ma da kika samu nitsuwa domin kuwa magana ta nitsuwa nake so muyi tsakani na dake
Toh alhaji ,gani ai bisimillah
Akan maganan yaron nan ne kaamil
Nan ta bata rai kamr wanda ya ambaci mutuwarta
Nasan kinada lavarin allah ya nufe sa da Shiga inuwar muslunci
Ko ba haka ba
Eh nasani Alhj…amma duk da hakan bashi ya fitar da shi ba,Alhj kai harka yadda yaron nan tsakanibda Allah ya karbi musulunci?ni dai na tabbata kwadayi ne da munafurci yasa shi, makirin yaro
To ya Isah haka ,ni bani da niyyar daga murya yau mariya
A matsayi na na mijinki na kiraki nan ne domin na tunatar da ke akan fadin Allah da manzonsa.
Ko kinsan cewa bayan biyyayya wa iyaye,abunda allah ke matukar farinciki yaga bawa na aikatawa shine taimakawa wani ,?tsoho,miskinai nakasassu,yara kanana,marar lpya,matafiyi,wanda aurensa ta kare sanadiyar mutuwar mijin,
da marayu sune mafi kauri ajerin wannan sahun
,daga bisani Allah bai kayyade mana ga wanda zaka masa ga wanda bazaka masa ba,,….har dabbobi,saboda shida Kansa yace “WALLAHU YUHIBBUL MUQSIDIN,Allah loves the doers of good……
Ko so kike kifada acikin mutanen da shaidan ke alfahari dasu wajen Sanya musu tsana,da kishi, da bakin cikin dan uwansu ne,kamr yadda Allah yafada mana a (Q35.06)
Kowa da kika gansa a duniyan nan hallitar Allah ne,kuma Allah bai halicce mu don ya sa mu a wuta ba,infact yana son mu ne ya halicce mu…..
jarabawa kawae Muke dauka a duniya sakamakon ka shine gidan da kazaba a lahira da hannunka,domin yace
#”wamayya amal misqala zarratan khaiiray-yara ,waman yaamal misqala zarratan sharray-yara.#”
..ba zalunci komai zaka gani kuma zaka karbi hisabi…komin kankantar sa.
Naga kin bada karfi akan kiran yaron nan Arne ko? Toh mariya bari kiji
“Manzon Allah tsira da aminci sutabbata agareshi ya Fada mana acikin sunnan Abu dawud vol 3 page170 hadisi na 3052) annabi yace “ku kula’ domin duk wanda ya muzguna ko ya tsananta ma wanda ba musulmi ba,ko ya karbe masa wani Abu na hakkinsa,ko ya sashi bakin cikin da bazai iya dauka ba,ko ya karbe masA wani Abu batare da yardansa ba
“ZAN YAKI WANNAN MUTUMIN RANAR TASHIN QIYAMAH”
Hadisai dayawa sun bayyana mana akan mu kira mutane ga addinin Allah da kyawawan halayen mu,,,,ba zallan kira da baki ba.
Kin manta ne,tarihin lokacin da annabi ya shiga tsanani da mabiyansa a garin Makkah,jafar bin Abu talib ya tura yayi jagora zuwa (Habasha)garin ARNE sarki AnnajasHi ,akan suje zaa karbe su……kuma hakan akayi ,,,,,sarkin ArNA Annajashi ya karbi musulmai ya tseratar da su ya kuma basu cikakken yanci a kasansa…..ke wacece da zaki tsananta harshenki akan su har haka mariya?
Tarihi ya nuna akwae kykkwar alaka tsakanin mu tun zamanin manzon Allah saw…..
Tawakkali da Amana ne kawae basu dashi..musamman ma arnan karshen zamani…saboda haka kar ki nuna musu yarda fiye da dan uwanki musulmi…koma ya yake
Kiyi bishara da kkywar dabia a matsayinki na musulma ko dan su sami rabo ta dalilinki,
Kar kimanta har muddin kinyi kira ga alkhairi ladanki dai dai take da wanda kika kirashi ya karba batare da an rage masa NASA ladan ba
Daga karshe ina jan hankalinki mariya, raphael yanzu kaamilu ne ,yazama dan uwanki a musulunci
Kinsan kuma hukuncin wanda ya kira dan uwansa musulmi da sunan Kafiri a musulunci….
.
Inaji miki,tsoro mariya ki sassauta halayenki mana
inada fa labarin duk abunda kike ma yaron nan,duk lokacin da na sa kafa na fita a gidn nan…..
Haba mariya ta,yanzu ke baki tunanin mu mutu su zafar su Fada cikin wannan yanayin rayuwa? Duniyan nan fa ba tabbas
Kayi alkhairi ta mayar maka dashi hakama idan ka shuka sharri zai dawo maka wata rana
Kiyi hakuri mariya,mu zauna tareda kamil ,mu karfafa masa gwuiwa musamar da qaruwa ma addinin Allah….
Abun mamaki hawaye ne cahf a idon Hajiya mariya,kuka sosai takeyi
Takasa cewa komai….
Karasowa yayi kusa da ita ya shiga bata baki,
Daganan ya jagorance ta zuwa dakinta ta ya kwntar da ita
Sannan ya fice