JIDDATULKHAIR CHAPTER 28 BY KHALISAT HAIDAR

Abuturrab ya buda ido sosai yana kallon Abbansa gabansa na faduwa yace “Divorce kuma Abba?? Why will i do so bayan kayi instructing dina kar inyi haka? Ni ban saketa ba Abba ga ta ka tambayeta, idan na saketa ae baxa mu xauna tare ba.. ” Ba Aunty da ta bude baki tana kallonsa ba, har Jiddah kallonsa take da mamaki, Ummi dai wani direction din daban take kallo, Umma kam duk jikinta a sanyaye yake jin batun nan da ya tasheta da sassafe, Abba kansa ya kasa cewa komai, Aunty ta saki salati tace “Yaushe ka fara karya Abuturrab? Yaushe ka dawo makaryaci? Bakina da naka kace min ka saki yarinyar nan tun ranan da ku ka tare shine xaka karyata ni yanxu a nan?” Ya girgixa kai a hankali yace “Ban karyata ki ba Aunty, kawai na gaya maki haka ne saboda hankalinki ya kwanta tunda naga baki son auren, amma ni ban saketa ba, bana son abinda xai sa ki dinga damun kanki shi yasa na fada maki haka” Bude baki tayi tana kallonsa, yayi kasa da murya yace “Abba ga ta nan ku tambayeta ni ban saketa ba, I’m saying nothing but the truth” Jiddah ta sunkuyar da kanta daga kallon da take masa duk jikinta yayi sanyi, Abba kam ya ma rasa abun cewa, Can Ummi na kallon Jiddah tace “Jiddah” dago kai Jiddah tayi ta kalleta, Ummi tace “Ki fada min gaskiya Jiddah, Aliyu mijinki ne a yanxu ko ba mijin ki bane?” Gabanta ya dinga faduwa taji hawaye ya kawo idonta, Abuturrab ya gyara xamansa shi ma gabansa na faduwa sai dai bai kalleta ba, a hankali tace “Mijina ne Ummi” Aunty taji kamar ta rusa ihu a wajen lkci daya idonta yayi jajir, Abuturrab ya sauke wani boyayyen ajiyar xuciyar relieve, Abba yace “Shkkn, Allah ya rufa asiri, u can leave now Aliyu” Abuturrab ya mike ba tare da ya kallesu ba yayi masu sallama, ita ma ta tashi ta sallamesu sannan ta bi bayansa tana goge hawayen idonta, Umma ta bi su da kallo xuciyarta na kokwanton amsan da Jiddah ta ba yar uwarta, this isn’t joking matter, she needs to investigate deep into this issue… Aunty ma ta bi su da wani kallo sai kawai ta saki kuka kamar warce aka sanar ma sakon mutuwa, ita Abuturrab xai yaudara, ita xai karyata, ita xai watsa ma kasa a ido, ita xai kunyata gaban kowa?? Ko minti daya Abuturrab bai kara a a gidan nasu ba ya wuce da Jiddah, bai ce mata komai ba ita ma haka har suka iso gida bayan ya siyo masu abinci a hanya, parking yyi a compound dinsa, sai da ya sauka sannan ita ma ta sauka motar, ya mika mata ledan abincinta yana kallonta, kin amsa tayi hakan yasa yyi wucewarsa ciki da ledan ya bar ta tsaye a wajen, xaunawa yyi kan kujera a parlor ya jinginar da kansa da kujeran ya sauke ajiyar xuciya feeling relieved, sai bayan kusan minti sha biyar ta shigo parlon, xata wuce sama yace “Xo nan” Ta ki tsayawa har ta wuce, ya bude baki yana bin ta da kallo. Through out ranan jiddah na daki shi kuma yana downstairs, bai bi ta kanta ba har after isha, bayan ya dawo mosque ya dai ga alamar tayi making tea a kitchen, yana haurawa sama ya tsaya kofar dakinta sai kuma ya bude slowly, xaune ya ganta idonta yyi ja, ya kulle kofar dakin yana kallonta, yace “An maki wani abu ne kike ma mutane kuka tun safe?” Ta ki kallonsa, a d’an tsawace yace “Ba magana nake maki ba?” Ta juya masa baya, rungume hannu yyi yana kallonta, can yace “Kuka kike saboda kina tunanin kinyi musu karya?” Ta juyo tana kallonsa cikin rawan murya tace “Ehh mana, me yasa xa ka masu karya??” Yace “Ohh da na masu sai nace ke ma kiyi masu??” Kallonsa ta dinga yi ko kiftawa babu, ya karasa ya tsaya gabanta yana kallonta da kyau yace “Ni ai ban aike ki kiyi masu karya ba… sannan akwai wani abu na musamman da ke sa mutane su yarda cewar mata da mijinta ne ke rayuwa a cikin gida? akwai wani abun da xanyi da xai tabbatar da cewar ni da ke mata da miji ne? Ko bana ciyar da ke yanda miji ke ciyar da matarsa ne? Ban baki sutura ba? ban baki wajen kwana ba? ban baki kariya ba? Ina ce duk wannan shine abinda miji ke ma matarsa? Ko akwai wani abu daban da ban sani ba ki sanar da ni nima in maki don xaman namu yayi kama da na mata da miji a daina xargin mu…” ta dauke kanta tace “Idan mun yaudari mutane ai Allah shi yasan gaskiya, kuma ai kai ma kasan ni ba matarka bace nima kuma nasan kai ba mijina bane” Kallonta kawai yake yace “Toh meye shaidan hakan?” Tace “Ai kai ma kasani, meyasa baxa ka fada masu gaskiya ba, sannan ni ka bani takardan in ajiye wajena tunda baka aikeni inyi karya ba” durkusawa yyi yana kallonta yace “Haba?” Tace “Ehh” yace “Toh ko dai in fara maki abinda masu aure ke yi, kilan hakan xai sa ki fara rage tunanin ai ni ba mijin ki bane, infact mancewa ma xaki yi cewar babu aure tsakaninmu, takarda kuma da kika ce… Mu je in baki ki ajiye wajen ki” mikewa yayi still yana kallonta, ta k’i tashi, ya hade rai yace “Mu je ki amsa nace” mikewa tayi a hankali, ya nufi kofa ta bi bayansa xuwa bangarensa, suna isa ta tsaya bakin kofar babban parlon, ganin bata shigo ba yace “A bakin kofa xan baki takardan?” Shigowa parlon tayi taga ya nufi bedroom dinsa yana isa ya tsaya bakin kofa ganin bata karaso ba yace “Shigowa xa kiyi ai malama” daga haka ya shiga cikin dakin, a hankali ta bi bayansa tana shiga ya kulle kofar, ta makale jikin bango tana kallonsa, sanyi sosai ne a dakin sbda Ac dake aiki, ya nufi gaban mirrow ya dau diary dinsa ya bude sai ga takarda well folded ya ciro a ciki yana kallonta ya mika mata yace “Gashi” Ta sauke kanta kasa kamar baxata je ba sai kuma ta karasa ta sa hannu xata amshi takardan ya fixgota, kara tayi a tsorace ta fara kokarin kwace kanta, yace “Saboda ina tsoronki xan baki? And.. ina ruwanki da rashin auren dake tsakaninmu, ci kika rasa ko sha??” Gaba daya a tsorace take, kamar xata yi kuka tace “Kayi hakuri don Allah….” Yace “Baxan yi ba” a hankali ta daga kai ta kallesa, saketa yyi ya tafi gaban madubi ya ajiye takardan sannan yace “Idan kin isa ki dauka ki fita” Yana fadin haka ya nufi kofa ya bude ya fita ta bi sa da kallo har ya kulle kofar, a hankali ta isa gaban madubin ta dau takardan ta warware tana dubawa, takardan ne kuwa, in accord to the content of d paper, he is no longer her husband, duba diary din tayi taga ba a ciki ya falli takardan da yayi rubutun ba, wajen mirror din ta dinga dubawa nan taga takardan da ya cira a ciki, ita ma ta cira sannan ta mayar da sauri ta ajiye, linkewa tayi yanda ya linke na rubutun ta ajiye gaban madubin sannnan ta dau wanda rubutu ke jiki tana tunanin inda xata boye, kana ganinta kasan a tsorace take, hularta ta saka hannu ciki taji gashinta is very oily, ta sake ciran wani sabon takardan ta nannade na rubutun a ciki sannan ta tusa a cikin hulan ta koma inda take tsaye ta tsaya, bayan kusan minti goma sai ga shi ya shigo, sunkuyar da kanta tayi cikin sanyin murya tace “Kayi hakuri baxan sake cewa ka bani ba kuma” Bai ko kalleta ba, ya ajiye sauran bottle water din hannunsa, sannan yace “Aa ki dauka dai, gashi can gaban madubin” Ta girgixa masa kai kawai, gun takardan ya nufa gabanta ya dinga faduwa tana kallonsa ko kiftawa babu, ya dauka, bata jira taga me xai yi ba har ta juya xata fita da gudu taji yace “Gashi ki tafi da shi” Juyowa tayi tana xare ido taga yana mika mata takardan, kallonta kawai yake, yace “Amsa nace” Ta karasa a hankali ta sa hannu xata amsa ya murda kunnenta yace “Tahowa kika yi xa ki amsa kenan” Bata fuska tayi bata dai ce komai ba, lkci daya taga yana bude takardan da gudu ta nufi kofa ta fice daga dakin ya bi ta da kallo ganin babu komai a jikin takardan, mamaki ne ya cikasa ya sake juya bayan takardan that is plain, Bude baki yayi with so much surprise, bai san lkcn da yayi murmushi ba ya rungume hannunsa, so tana da irin wannan wayon ashe, bai bi ta ba sabida yasan xa ma ta dawo ne, ya tafi gefen gado ya xauna, Jiddah ta jingina da kofar parlonsa ta xame kasa tana yarfe hannu, gaba daya a tsorace take, sai jiran fitowarsa take anytime amma har sannan bai fito ba, bin babban parlon ta dinga yi da kallo kamar xata hango makullin kofar, har bayan minti talatin bata gansa ya fito ba, gajiya tayi da xama a bakin kofar, ta mike a hankali tana leka kofar dakin nasa, can dai ta karasa bakin kofar ta leka ciki don kofar ba a kulle yake gaba daya ba, kwance ta gansa waya kare kunnensa, ta juya da sauri ta koma inda take xaune kamar xata yi kuka, har sha biyu saura Jiddah na xaune gefen kofar, bacci ne ya fara damunta, mikewa tayi ta tafi kan kujera ta kwanta nan da nan bacci ya dauketa, can cikin dare taji ana lalubata, ta mike a tsorace ganin duhu a parlon tace “Wayyo Allah na” Muryarsa taji yace “Ina takardan yake” Jikinta ma rawa tace “Yana cikin hulana” Xata cire hulan ya rigata cirewa ya ga takardan a kanta ya dauka sannan ya saketa ya koma dakinsa ya kulle kofar, har lkcn gabanta faduwa yake ta mike xaune tana bin parlon da kallo don ko alamar haske babu, a hankali ta mike tana neman hanya har ta isa kofa ta murda taji a kulle har sannan, jingina tayi da kofar kamar xata yi kuka, can ta juya ta koma saman kujeran ta kwanta, nan da nan bacci ya sake dauketa, kiran sallan asuba ne ya farkar da Jiddah, ta tattaba lallausan abinda taji a jikinta, kofar daki aka bude da sauri ta rufe idonta don hasken dakin ya hasko parlon, tana ji ya bude kofar parlon ya fita, lkci daya kamshin turarensa ya gauraye parlon, sai bayan kusan minti biyar ta cire duvet din jikinta ta mike a hankali jin xa a tada sallah, ajiye duvet din tayi kan kujeran ta nufi kofa ta bude ta fita xuwa dakinta. Karfe takwas saura Jiddah ta farka daga baccin da ta koma bayan tayi sallan asuba, mikewa tayi ta shiga bandaki sai da tayi wanka ta wanke baki sannan ta wanke bandakin ta fito, tana gama shiryawa ta hau gyaran dakin, bude kofa aka yi ta juya da sauri, calmly yace “Ki sameni kasa” daga haka ya rufe kofar, ta gama abinda take sannan ta sauka kasa, yana xaune parlor yana kallo, agogon wrist dinsa ya kalla yace “Na baki minti talatin ki je ki dafa abinda xa ki ci….” tsayawa tayi tana kallonsa, ganin bata motsa ba ya daga kai ya kalleta, da sauri ta juya ta wuce kitchen din ya bi ta da kallo, indomie ta dafa ta ci a kitchen din ta wanke plate sannan ta fito, ya kalleta ya nuna mata karamin travelling bag dinsa da ya sauko da shi parlor yace “Ki je ki hada kayanki kala biyu da duk abinda xa ki bukata, kar ki bata min lkci, ki saka Jilbab idan xa ki sakko” A hankali tace “Ina za mu je kuma, amma ba jirgi xa mu hau ba ko??” ganin irin kallon da yake mata ta dau travelling bag din ta juya ta wuce sama, kayan nata ta hada sannan ta sauko kasa a sanyaye, Hijab ne har kasa jikinta, ya mike ya nufi kofa ta bi bayansa rike da jakar. Parking Abuturrab yayi kofar gidansu Ahmad, Jiddah ta juya ta kallesa ganin inda suka xo, wani farin ciki taji a ranta, bude motar yayi ya sauka, ita ma ta sauka ta bude back seat ta dau jakar kayanta, ai da ta san nan xa su xo da ta debi kaya da yawa, ganin ya nufi gate din gidan ta bi bayansa da sauri, gaba daya farin cikinta ya kasa boyuwa, sai kallon kofar Maman Abdallah take har suka shiga main parlor din gidan, Umma ta fito daga dakinta ganinsu tace “Aa daga ina haka kuma” Yayi kasa da kai yace “Daga gida Umma” nan ya gaisheta, ta amsa tana kallon Jiddah tace “Sannu da xuwa Jiddah…” Gaisheta Jiddah ma tayi tana mayar mata da murmushin, Umma ta amsa tana tambayarta ya gida, Jiddah tace “Lafiya lau” Umma tace “To kun ma karya kuwa wannan sammako haka?” Abuturrab yace “Eh mun karya, i brought her ahead of the wedding….” Umma da taji dadi har ranta don wnn shine right time da xata fahimci gaskiyan abinda Aunty ke fada tace “To maa sha Allah, that’s very good” Yace “Kudin ankon kuma wa xa a tura ma?” Umma tace “Anko kuma?” Yace “Ummi ce tayi maganan ankon ran Friday” Umma tace “Kyale Ummi, ae ta riga ta mata, har dinki an bada” Yace “Toh Allah ya saka” mikewa yayi yace “Sai anjima Umma, xan wuce kano da yamma in sha Allah, ranan alhamis xan dawo” Umma tace “Toh Allah ya tsare, shi ma Ahmad din ranan laraba xai shigo…” Abuturrab yace “Ehh mun yi waya da safe, haka yace min” Ya d’an kalli Jiddah sannan ya nufi kofa yana ma Umma sallama, Umma tace “Toh baxa kiyi masa rakiya ba Jiddah?” D’an murmushi kawai tayi ta sunkuyar da kanta, Umma tace “Tashi ki je” a hankali ta mike ta nufi kofa ta fita, cike da kasaita yake tafiyar, ta bi sa da kallo, bin bayansa tayi har suka fita gidan, ya bude driver seat xai shiga sai kuma ya tsaya yana kallonta don makalewa tayi jikin gate, suna hada ido ta sauke nata idon, yace “Kina son wani abun ne” Ta d’an turo baki tace “Umma ce tace in raka ka” ya shafa kansa yace “Idan Umma tace ki shirya ku je can gidan kice mata baki jin dadi baxa ki iya xuwa ba” Tana kallonsa tace “Toh ka tayani gaya mata mana” ya daga kafada yace “Toh ki tafi ni ba ruwana” Daga haka ya bude motarsa ya shiga ya tada yayi reverse, a hankali ta juya ta koma cikin gidan, daren ranan Maman Abdallah na parlon Umma tare da mai aikin gidan suna ta hira, duk sbda Jiddah ta shigo kuma, sai kusan karfe goma maman Abdallah ta bar parlon, duk yan matan gidan na can gidansu Abuturrab, mikewa Jiddah tayi a hankali tayi ma mai aikin sai da safe ta wuce dakin da Umma ta sa ta ajiye jakarta, tuni Umma ta tafi ta kwanta tana tunanin where to start from coz ko kadan bata yarda da Jiddah da Abuturrab ba, Jiddah tayi wanka ta sauya kayan jikinta xuwa na bacci sannan ta kwanta. Washegari monday Jiddah ta taya Huraira mai aiki girkin breakfast, sosai ta sake a gidan ba kamar gidan su Abuturrab ba duk da Seeyama bata nan, Karfe sha daya na safe ta raka Umma kasuwa da driver, basu dawo gida ba sai kusan azahar, Jiddah na sallah ta kwanta don sun ci abinci a restaurant, da yammacin ranan Seeyama da Aisha da Safiyya suka xo gidan amsar ma Aunty sako wajen Umma, Seeyama tayi murnan ganin Jiddah a gidan, Umma tace “Sai ki shirya ki bi su Jiddah, idan na je anjima da daddare sai mu dawo tare” Shiru Jiddah tayi ta kasa ce mata komai, Seeyama tace “Ki tashi sister Jiddah Aunty na jiranmu” Mikewa Jiddah tayi a ssnyaye ta saka Hijab dinta, Driver Umma ta sa ya mayar da su can gidan saboda Jiddah, tun da suka sauka motar gaban jiddah ke faduwa ta dai bi bayan Seeyama rike da handbag dinta har suka shiga parlor, dai daikun baki ne da suka xo biki a parlon, Jiddah ta sunkuyar da kanta ta nufi bangaren Ummi, tana shiga parlon taga mata biyu a xaune, Xaunawa kasa tayi ta gaishesu, duk suka amsa, ba a dau lkci ba Ummi ta fito daga daki, ganinta tace “Daga ina haka, ina Aliyun?” Jiddah ta gaisheta sannan tace “Tare muka xo da su Seeyama” Ummi tace “Ohk toh ki shiga can ciki” mikewa Jiddah tayi ta wuce bedroom din Ummi, Hajiya Murja kawar Ummi tace “Kaddai ita ce matar Aliyun?” Ba tare da Ummi ta kalleta ba tace “Ehh ita ce” Hajiya Salaha tace “Allah sarki, ashe yarinya ce ma, toh Allah ya basu xaman lafiya, ga ta dai kamar ba sa wa ba hanawa” Ummi ta d’an yi murmushi kawai, Seeyama ce ta shigo parlon tace “Ummi Aunty Jiddah ta shigo nan” Ummi tace “Tana ciki” Seeyama ta shiga sai ga ta sun fito tare da Jiddah suka fita parlon, sosai gabanta ke faduwa tana tsoron kar ta hadu da Aunty har suka shiga dakinsu Ramlah, Ramlah na ganin Jiddah ta washe baki tace “Aunty Jiddah sannu da xuwa” Jiddah ta xauna tana murmushi tace “Ya gida” Ramlah tace “Lafiya lau, yaya fa?” Jiddah tace “Ya tafi kano” Seeyama tace “Shi sa ya kai ki gidan Umma?” Kai kawai Jiddah ta gyada mata. Suna nan xaune har aka kira magrib, bude kofar dakin aka yi Aunty ta leko tana cewa “Wai baxa ku fito kuje ku yi wanke wanken can ba dake bakin pampo gashi har anyi magariba, ko waye xai maku? Ai sai ku hakura xuwa gobe ku sakankance tunda nasan yan kauye masu wanke wanken xa su iso” Jiddah dake kan darduma ta sunkuyar da kai gabanta na faduwa, tsit Aunty tayi ganin Jiddah kan darduma, can tace “Ko da yake tun safe ai ku ke ta aiki, ke ya kike da suna??” Jiddah ta kalleta, Aunty tace “Ehh da ke nake kike kallona haka, tashi ki fita ga wanke wanke can bakin pampo kije ki wanke” Mikewa tayi da sauri, Seeyama ta mike tace “Ta barshi kawai xa mu yi aunty” Aunty ta jefa mata wani kallo tace “Toh ita xa ta yi, ku kuma xan aikeku yanxu tare da driver xa ku je min siyayya a supermarket” Jiddah ta nufi kofa ta bi gefen Aunty da ta bi ta da wani kallon tsana ta fita, kitchen Jiddah ta nufa ganin kofar kitchen din a bude ta fita taga uban kayan wanke wanke a bakin pampo ga omo da soso, ruwa ta tara ta fara wanke wanken, ba a dau lkci ba sai ga Aunty ta shigo kitchen din ta dinga fitar da plates wankanku tana ajiye su kan marasu wanki, ita dai Jiddah bata ce komai ba, har tukwanen sai da ta fitar da su sannan ta dau soson waya ta jefa mata tace ki tabbatar kin bi bayan tukwanen nan kin wanke su fess, xuwa gobe kuma xan san yanda xanyi da ke, daga haka ta juya ta koma ciki, Jiddah dai ta ci gaba da wanke wanken da take a sanyaye. Ba ita ta bar bakin pampon nan ba sai kusan karfe tara da rabi, duk ta gaji ga uban yunwan da take ji, bbu kowa parlon sai yara dake ta wasa, iyayensu kuma na can sama, Jiddah ta rakube jikin kujera tana jin kanta na mata ciwo, har ta mance rabon da tayi irin wannan aikin, tun bayan rabuwanta da Hansai, Aunty ce ta shigo parlon da sauri tana sanye da Hijab, har ta nufi kitchen sai kuma taga Jiddar a rakube a parlor, tana kallonta tace “Yauwa mu je ki rakani xan amso sako yanxu”

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE