KUNDIN KADDARATA CHAPTER 20 BY HUGUMA
Duban sumayya cikin shaqaqqiyar murya yace
“Jeki ki rufemin qofar gidan” tsayawa tayi tana dubansa jikinta na rawa,ta fuskanci me yake nufi,wato don kada ma ihun fa’iza ya sanya ta samu masu kawo mata dauki kenan
“Jeki ki rufemin qofar gida nace” ya maimaita cikin tsawa ganin bata da niyyar tafiya,jikinta na rawa ta wuce taje ta rufo,bata kai ga dawowa tsakar gidan ba kuwa taji ana bugun qofar gidan,daga inda yake ya bata umarnin kada ta bude ta dawo ciki.
Ga mamakinta fa’iza ke bawa mukhtar haquri hannu bibbiyu take roqonsa,bai ko dubeta ba sai sumayya da ya kalla
“Shiga kitchen ki dauko min cooler dinki wadda take zuba miki abinci” babu musu wannan karon ta shiga ta fito da ita,ya nuna maga gaban fa’iza da ido ta dire anan din ta koma gefe ta tsaya jikinta na rawa.
“Maza bude ki cinye abincin dake ciki yanzu yanzun nan” wani rugugin aradun tashin hankali ya rufto mata,tirqashi,ai data ci abincin ciki gwara mukhtar din ya kwana ya wuni yana jibgarta,domin cin abinci koda shinkafa qwaya tak dake ciki ne dai dai yake da ban kwana da duniyarta,sai ta zube a qasa tana sake roqarsa yayi haquri kuskure tayi kuma ba zata sake ba,wani murmushi mai tauri da d’aci ya saki
“Ko baki fada ba ai dama har abada ba zaki sake aikata irn wannan mummunan aikin ba cikin gidan mukhtar,afuwa daya da zan iya yi miki idan kina da buqatarta shine ki dauki abincin nan ki cinye salun alun”
“Wallahi muntari bazan iya ci ba,zan iya rasa rayuwata,kayi haquri”sai yayi turus ya zuba mata idanu cike da fargaba da kuma bacin rai
” kice ma niyyar kisan kai kika yi?,sumayyar tawa zaki kashemin?”ya fada cikin wani irin zafin rai,da sauri ta girgiza kai tare da sake debo wata rantsuwa don gyara baran baramar da take gab da sake tafkawa,ganin taqaddamar take qarewa har muntarin na nade hannu zaiyiwa fa’iza dure ya sanya sumayya dake gefe kamar mutum mutumi magantuwa,ta tabbata tunda har fa’izan ta toge kan bazata ci ba komai zaya yi mata ya nuna akwai wani mummunan abu da ta qulla cikin abincin,wanda su kansu basu san meye ba,ba kuma su san sakamakon da hakan zaya haifar ba idan taci din
“Ya mukhtar,ka qyaleta don Allah,koma meye tunda Allah ya kubutar da ni bayan muna da masaniyar ba wayon mu bane sai mu gide masa ko?”
“Ok,haka ne fa” ya fada yana gyada kai tare da duban sumayyan,saidai kallo daya tayi masa ta fuskanci bawai yana nufin ya haqura din bane
“Shikenan ki bar cin abincin” ya fada yana juyawa zuwa dakinsa.
Murmushin nasara da farinciki fa’iza ta saki tana duban sumayya duba na wulaqanci
“An gaya miki haihuwa kayan banza ce?,ni na sani ko darajar cikinsa dake jikina kawai ta isheni,banza mara amfani ke zaki ci gaba da diban kayan takaici juya kawai wad………..”.
Fitowar mukhtar dauke da belt ita ta maqale sauran zazzafar maganar da take da burin ci gaba da yabawa sumayya,tsayawa yayi gabanta yana gyara belt din tare da fadin
” babu batun cin abinci amma wallahi baki ci banza ba,sai na fanshe wahala da baqinciki rashin zaman lafiya da rashin kwanciyar hankalin da kika shigo kika haddasawa gidanmu,kinga gobe sai ki koyi darasin zaman duniya”kafin su ankara ya fara jibgarta tako ina,tsoro da firgici ya hana sumayya tabuka komai,abinda iyatsawon rayuwarsu bata taba gani mukhtar yayi ba,duka duka koda ga qaramin yaro bare ga matarsa ta aure,lallai babu shakka fa’iza na shirin koyawa mijinsu mummunar aqida idan bata tashi tayi da gaske ba,don daga haka miji ke farawa idan ba’ayi wasa ba.
Ta nufeshi da hanzari da niyyar dakatar da shi saidai tuni ya hankadata gefe cikim zafin rai ba tare da ya san yayi ba,a rashin sa’a ta fadi kuwa kan hannunta wanda sai da ya bada wani sauti ta saki kalmar wash! Cikin azaba,bata sake yunqurin tashi ba ta zubawa sarautar Allah ido.
Sai da ya tabbatar ta daku sannan ya dakata yana dubanta
“Ki tatattara duk wani tarkace naki da kika san kin shigo gidan nan da su ki koma inda kika fito,na sakeki saki biyu” wani ihu ta kurma kamar zautacciya tana shirin miqewa tsaye
“Wallahi baki isa ba muntari,zama daram wallahi sai na haife abinda ka qusa min ma rainshi sannan” wata dariya ya saki sannan ya miqa hannunsa ya fincikota tare da fusge zanin jikinta.
Idanu sumayya dake zaune dirshan kan sumunti ta qwalalo ganin abinda ya fado jikin fa’iza wanda da shi ake canza tafiya ake burga ake kira ciki ne,cikin ma kuma wai na mukhtar dinta,tarin zannuwa ne aka hadasu aka qulle cikin zani daya fa’izan ke daurawa
“Indai ciki ne gashi nan yau kin haifeshi ko,rainonsa kuma sai ki ajjiyemin kayana ko ni zan raini abu na” ya fada yana qyalqyalewa da dariya,gaba daya wani muzanci ya kama fa’iza,me kenan?,meke shirin faruwa?,dama mukhtar yasan ba ciki bane shi yasa ya qyaleta,shi yasa bai nuna farinciki ba da result din bogi data bashi,bata kammala karanta wasiqar jakin ba maganar mukhtar din ta kuma katseta
“Kin maida mukhtar wawa shashasha jaki irinki ko?,don kinci sa’a na qyaleki tun lokacin ban hukunta ki ba kan raina kin wayo da kikayi ba?,to wallahi kada ki yadda na fito a wanka na taddaki cikin gidan nan,idan ba haka ba kowanne laifi da kika aikata cikin gidan nan iya tsawon zaman da kikayi cikinsa sai na miki hisabinsa tare da hukunci akansa daya bayan daya” ya fada yana yarda belt din ya dauki sabulunsa da ya watse gefe ya shige wankansa.
Cikin tsananin radadin ciwukan da taji ta miqe ta shige dakinta,bata yi ko minti biyar ba ta fito dauke da jaka da hijabi,har ta gota ta dawo da baya ta dubi sumayya
“Wallahi wallahi kada ki dauka kinci nasara a kaina,yanzu aka fara wasan” ta fada tana mai ficewa da sauri jin motsin mukhtar na niyyar fitowa saga bandakin.
Bin qofar data fice din yayi da kallo domin yaso ya taddata,sai a lokacin ya maida dubansa ga sumayya
“Me take gaya miki?” Bata amsashi ba sai niyyar miqewa da take amma ta kasa,ganin haka ya sanyashi qarasa gurinta da sauri yana nufin riqe mata hannu ta saki qara da sauri sabida gun ciwon ya taba
“Subhanallahi,hannu kuma sumayya?” Ya tambayeta yana duban gun,banza tayi da shi cikin son yunqurin tashi yayi niyyar taimaka mata da sauri tace
“Barni,bana so” ta tattara qarfinta ta miqe ta nufi dakinta.
Binta yayi a baya da sauri,tana shirin shiga dakin ya cafkota,qara ta saki saboda hannun ya riqe,sosai ya murde hannun har sai da ya bada qara alamun inda ya gulle ya koma dai dai,kafin ya kammala ta gama hada gumi,jikinta yayi laushi ya jata cikin jikinsa yana goge mata hawaye da gumin da ta hada.
Cikin kujera ya ajjiyeta yana maida ajiyar zuciya ya fice zuwa dakinsa.
Cikin qanqanin lokaci yayi wankan ya shirya cikin shadda sea grean,sosai tayi masa kyau,itama sabuwa ce cikin sabbin dinkunan da yayi shima,ya kulle gidan suka fito.
Sai daya bude mata gidan gaba ta shiga sannan ya zagaya shima ya shiga daya bangaran yana duban ta,yadda fuskarta ta cika da farinciki tana masa addh’a,sosai yaji dadi cikin zuciyarsa shima,yayi bismillah ya tada motar suka fice daga layin a hankali.
Suna tafe suna hirarsu cikin nishadi da walwala har suka iso qofar gidansu sumayyan,cikin zumudi ta bude ta fice mukhtar ya bita da kallo yana murmushi,tamkar yau ne ta fara zuwa gidan sai murna take.
A tsakar gida ta tadda maman zaune saman tabarma sai fitilar qwai dake kunne a gefanta kasancewar babu wutar nepa,ba kowa tsakar gidan sai ita kadai
“A’ah,sumayya da kece haka da daren nan?” Mama ta fada tana sake bude tabarmar da take kai,gefanta ta qaraso ta zauna bakinta yaqi rufuwa
“Wallahi mama nice,ke kadai ce?”
“Eh duka sun tafi makarantar dare,amma gab suke da dawowa”
“Malam fa?”
“Sun tafi dubiya asibitin murtala shi da abubkar,maqwafcin mu malam sule ba lafiya”
“Ayyah baba sule,Allah ya sawwaqe……bari na yiwa yaya mukhtar din magana to ya shigo ku gaisa”
“Au tare ashe kuke……maza shigo da shi” inji mama tana janyo hijabinta dake gefanta ta zura.
Cikin girmama juna suja gaisa sannan ya fada mata motarsa ya kawo su sa mata albarka,tayi kuwa addu’a sosai don babu damar ta leqa malam din baya nan,nan ya fice qofar gida ya barsu.
Bai jima da fitar ba mama ta matsa mata ta shi su tafi tunda zasu gidan yahanasu,ta miqe suka yi sallama da maman ta fito.
Sai ta tadda mukhtar din da su zainab da halima ya bude musu motar suna ciki,malam kuma yana gefe da alama isowarsa shi kenan don gaisawa ma suke,ta qarasa cikin girmamawa itama tabi sahun mukhtar ta duqa ta gaidashi sannan ta gaida ya abbakar,ya shiga tsokanarta ta hanyar cewa tayi qiba ta zama lukuta me mukhtar ke dura mata ita kadai,ta kasa tanka masa sai dariya da takeyi kanta a qasa saboda kunyar malam da takeyi.
“Ai sai ku wuce ko kada dare ya muku” cewar malam yana shigewa gidan bayan sunyi sallama,mukhtar ya fidda dubu biyu ya bawa su halima yace su sayi kayan kwalliya,qin karba sukayi sai da sumayyan ta sanya baki sannan suka amsa auna godiya suka shige gidan.
Shiru ya biyo baya cikin motar,mukhtar ya sauke ajiyar zuciya sannan yace
“Tarbiyyan gidanku na birgeni sumayya,naso a ce ina da wani dan uwa namiji da babu shakka sai na aura masa halima ko zainab” murmushi kawai sumayyan tayi sabida tasan koda yana da dan uwan babu ta yadfa su yaya yahanasu su yadda su sake hada zuri’a da ‘yan gidansu.
Mintina qalilan suka isa gidan,ya kashe motar ya fice ta bishi a baya bakinta cike da addu’a.
Dukansu suna tsakar gida zaune kan tabarma suma saboda zafin dake dan busawa a ‘yan kwanakin,ga matsalar rashin isashshiyar wutar lantarki da muke fama da ita ta kowanne bangare na qasar nan.
Da fara’ar ta ta amsa sallamar amma jin muryar sumayya yasa ta gintse ‘yar fara’ar data yo tsaraba,jamila dake gefen tabarmar ta matsa ma mukhtar,yayin da sayyada taqi motsawa ko su samawa sumayya wani abun zaman,hakanne ya sanya mukhtar din dubanta fuska a hade
“Ke,tashi ki bata guri” tuni ta miqe saboda tana shakkarsa kuma tasan halinsa sarai,daki suka shige ita da jamilan baki daya.
A girmame yake gaisheta ta amsa sannan sumayya ta gaidata,sama sama ta amsa mata suka shiga hira da mukhtar din.
Jamila ta fito da ruwan pure water mai sanyi guda biyu ta cup ta ajjiye gaban mukhtar din sai ya turasu duja gaban sumayyan yana cewa
“Bude kisha,kince min kina jin qishirwa dazu” zuciyar yaya yahansu ta tunzura,ta dinga jifansu da harara tana qwafe da su,ya maida dubansa gun yaya yahanasun
“Mota na kawo miki ki gani yaya,ta iso dazun da safe” sai ta harareshi
“Au shine sai yanzu kaga damar kawo min na gani kenan sai da ka gama nunawa duniya”
“Ba haka bane,data iso din ma a gareji na wuni ana mata service,ina dawowa gida kuma nayi wanka naci abinci muka taho kawo miki”
“Sai kace makaho da baka iya tahowa kai kadai,kai Allah ya kyauta,ya warware mana wannan masifar” ta fadi cike da haushi da tsana,don ya kauda zamcan don kada yayi nisa sai ya miqe yana fadin suzo su ga motar,haka suka miqe suka fice suna hayaniyar murna,tana zaune gun burinta kawai yace ta taso su tafi,Allah ya taimaketa sayyada ta leqo tace ta fito su tafi.
Tana zaune gaban motar shima haka amma sai zuba zance yayan taje wanda ya hana musu tafiya
“To Allah ya tsare ya rabaka da sharrin masu sharri,Allah ya qara budi ya kawo masu yi maka addu’a ya rabaka da wannan matsiyacin zaman kadaicin” bai amsa ba ya ciro dubu uku ya miqa mata yana fadin
” ga wannan ku qara”hannu tasa ta karba zata sake barkewa da wani surutun ya samu yaja motar suka wuce.
Duk yadda taso boye damuwarta amma sai da ya fuskanta,kan dole yake zuwa da ita gidan saboda yaya yahanasun dolensa ce,amma banda haka da tuni ta bar zuwan gidan,da tuni ya yanke alaqar dake tsakaninsu,kan hanya ya tsaya ya siya musu yoghourt manyan roba biyu masu sanyi da tsire mutumin sumayyan don duk ya faranta mata,a hankali ya dinga janta da hira da labarukan ban dariya,sosai ta sake sake masa jiki tana qyaqyata dariya wanda hakan shima ya masa dadi.
~TSUGUNNE BATA QARE BA~
Shi da ita duka suna zaune cikin falon nata da ya sake gyara mata shi,sanye suke da kayan barci saidai sai banbanta gun zama da ayyukan yi,shi yana zaune kan qaramar kujera ta zaman mutum daya dauke da computer yana aiki,yayin da ita ke kwance saman doguwar kujera tana kallo a tashar mbc inda suke hasko film din ashqui,kusan bata taba zama ta kalli film din complete ba sai yau.
Dakin ya dauki shiru kasancewar kowa ya bada muhimmanci kan abinda yakeyi,wayar mukhtar dake saman jakar laptop dinsa ta dauki tsuwwa,ya dubi wayar sai yaga baquwar lamba ce,kusan ya jima da daina daukar ire iren lambobin,to amma sunyi da wani costumer dinsa zaya kirashi kan wasu kaya da zai siya a shagonsa,sai yayi zaton shine saboda haka ya daga
“Assalamu alaikum” mukhtar din ya fada,kana yayi jim kusan daqiqa talatin sannan ya sake cewa
“Wacce zainab?,daga ina?” Ya sake yin shiru na sakan biyar sannan ya ja tsaki ya kife wayar yaci gaba da binda yakeyi.
Ba’a cika minti biyar ba wani kiran ya kuma shigowa,ya dubi wayar ba tare da yayi niyyar dagawa ba,lambar dazun ce dai sai ya sake dauke kansa yaci gaba da abinda yakeyi din ransa na quna.
Kiran da aketa maimaitawa a kai akai shi ya dami sumayya har ya ja hankalinta,tana daga kwancen ta dubeshi
“Don Allah yaya mukhtar ka daga,wallahi ta dameni” ta fada a shagwabe,bai dubeta ba yace
“Bazan daga ba,barta kawai” sai ta maida kallonta din batason ko gu daya ya wuceta.
Bai haqura ba mai kiran yaci gaba da nacin kiran har sai da sumayyan ta sake tankawa ya bata amsa irin ta dazun,sai ta tashi zaune tana gyara wuyan rigar barcinta da ya salube tare da fadin
“Shikenan,bari ni na daga maka ko a bar kunnuwanmu su huta”
“Kema ba zaki daga ba” ya fada bayan ya dago idonsa wannan karon ya dubeta,dariya ta saka tana tunanin wasa yake mata,dai dai lokacin da kiran ya sake shigowa ta sanya hannunta da sauri ta suri wayar ta daga ta kara a kunnenta tana masa gwalon taci nasara ta daga ba tare da wafce ba kamar yadda yayi niyyar yi da farko.
A hankali ta cire wayar daga kunnenta qirjinta na bugawa jin muryar macace tana gaya mata mukhtar take nema,miqa masa wayar tayi jiki a sanyaye.