BA SONTA BAKE BA TAUSAYI NE CHAPTER 1 BY AUTAR MANYA

Da sauri ta sunkuya tana mai dafe tarin takardun dasuka watse zuwa ƙasa wanda hakan yayi dai dai da shima sanda yakai nashi hannun zuwa ƙasan cikin rashin sa’a kuma hannunsu ya sarƙe dana juna atake anan taji wani baƙon yanayi ajikinta mai wuyar ta fassara shi.
Saɓanin shi dayay saurin ɗauke hannunsa daga saman nata gefe guda kuma yana jefa mata kallon raini da ƙasƙanci.
Sam bata lura da hakan ba face ƙarasa tattare mai takaddun nashi datai tana sakin wani irin lallausan murmushi.
Hannunta har yanzu rawa yake sakama kon baƙon lamarin daya faru agareta yanzu.
Seda ta kammala tattara mai sannan ta ɗago fuskarta cike da murmushi mai ƙayatarwa ta dube shi da matsakaitan idanunta.
Wanda kallo guda tayi masa takasa cigaba da kallon nashi murya na rawa kamar zatai kuka ta furta!
“Afuwan yallaɓai ban kula ba”
Tafaɗa tana mai janyo maganar da kyar tsintar kanta tayi dajin wata irin wawiyar faɗuwar gaba marar misali acikin kirjinta zuciyarta kuma kamar zata fasa kirjinta ta faɗo dan tsabar rawan data keyi.
Bai amshi takaddun ba kuma bai dena kallonta ta ƙasan idanunshi ba yarinyace wadda batafi shekaru goma sha takwas ba sanye take cikin ɗamammun kaya waɗanda suka bayyana baiwar kyan surar da Allah ya bata gawani dogon gashi data zubo dashi har gaba da dokin wuyanta kallo ɗaya yayi mata yagane ainihin itan wacece.
Tayi mai kama da karuwa marar aji kokuma tantiriyar ƴar iska marar aji! Abin da ya faɗi kenan aranshi yana mai lumshe kyawawan idanunshi.
Totaly batafi sa’ar ƴar ƙaramar ƙanwarshi ba to mai yasa zata ɓata rayuwarta ta nakasa kanta.
“Yallaɓai ka amsa hannuna”
Taja maganar cikin ƙosawa.
Tana mai tsareshi da nata idanun wannan lokacin ta ɗan ƙare mai kallo kaɗan.
Ataƙaice Shiɗin dogon namijine ƙaƙƙarfa baƙi mai ɗauke da manyan idanu da yalwatacciyar gira kallo ɗaya zaka masa kasan yana cikin jerin maza masu aji tare da izza da taƙama uwa uba kuma hutu gayu da ƴaƴan banki sun sami muhalli atare dashi.
Har yanzu hannunshi na naɗe a saman kirjinshi idanunshi lumshe wanda shi kallonta yake batare data farga da hakan ba.
“A’a ya subuhanallahi A’A yana ga baka ƙarasa ciki ba”
Maganar wani magidancin farin namiji daya karaso wajansu yanzu wanda hakan yasanya yarinyar zube mai takaddun ajikinsa ta ƙara gaba cikin sauri tabar wajan.
Cikin sauri yarinyar take sauka ƙasa har tana haɗawa da ɗan gudu kafin ta fita compound na hotel ɗin wata baƙar mota ta buɗe da sauri ta shiga taja murfin tana maida numfashi.
“Ke Ummul lafiya naga duk babu nutsuwa atare dake kodai…?”
Bata bar wadda ke mazaunin drivern tai magana ba tai saurin tarar numfashinta.
“Ameera ja mota mutafi yau nai gamo da ƙaddarata”
Wadda ta kira da ameerah itake mazaunin driver wadda daga gani zata girmewa ummul da sauri tai revars haɗi da nufar gate ta fita a hotel ɗin baki ɗaya.
Titi tahau tare da kunna redion motar.
Seda suka bar arean sannan Ameera dai ta kuma juyowa ta dubi ummul ɗin haɗi da ce mata.
“Ina mukai can ko nan?”
Lumshe idanu ummul tayi tare da cewa.
“muje rufaida ki mana order babu wani target yau kam mu tara gobe insha Allahu”
Tafaɗa har yanzu kirjinta bai dena rawa ba wanda tun haɗuwarta da A’A kamar yadda taji ɗayan ya faɗi ta tsinci kanta tare da hakan.
Gangara motar ameera tayi zuwa Rufaida fita tayi zuwa cikin wajan ta siyo musu ta dawo har lokacin idanun ummul suna lumshe haka ameera taja motar tare da ɗaukar hanyarsu kai tsaye hotoro ta nufa da motar tafe da ƙwarewa.
“Ameera yau naso shiga cikin gari amman hakan baze samu ba”
Tafaɗa tana mai cije lips ɗinta ameera batai magana ba sabida wayarta datai ringing ɗauka tai tana magana cike da barikanci still idanunta yana bisa kwalta.
Hotoro tsamiyar boka dai dai rakat ameera tasha kwana layi na uku ta shiga wanda yake tsit babu alamun jama’a awajan.
Abakin wani dogon gate ta tsaya tare da kashe motar ta ɗauki ledar data siyo musu rufaidan tayi waje itama ummul cike da sanyi ta balle nata murfin ta fita.
Gate ɗin suka karasa ameera taja kofar ta shiga itama ummul taja ta shiga ciki wanda tundaga farkon gidan har zuwa ciki matane zaune wasu na lido wasu na karta wasu tabar sigarice agabansu wasu kuma shisha gefe ɗaya kuma dogayen ɗakuna ne masu layi layi kallo ɗaya zakama gidan kasan gidane na karuwai amman na haya.
Kowani ɗaki akwai number ajikinsa hakan yasa ameera nufar ɗaki mai lamba ta hamsin ta buɗe da key suka shiga ita da ummul.
Ɗakine madaidaici domin babu tarkacen komai aciki daga gado se wadrobe na kaya se gas karami da frij babu toilet sabida gaba ɗaya bayi yana can waje kowa da kowa shiga yake.
Ameera ta aje ledar tare da faɗawa gado tana furta.
“washh kawata yaufa naci ubana na gurzu babu karya komai na jikina ciwo yake lallai Alhaji motar daya bani ba abanza ba”
Murmushi ummul tai kafin tayi magana wata mace kakkaura baƙa ta shigo ɗakin nasu.
“Yau akwai gayu zasu zo da daddare acikinku idan da wadda bata da M point sedai magana domin babbar fita ce”
Ummul batai magana ba sema tashin datai zuwa gaban wadrobe tana kokarin ɗaukar zani ta ɗaura Ameera ce ta kada baki tace.
“nikam yau naci azaba sedai ummul”
Tafaɗa tana mai kallon ummul dake tube kaya tare da zira hijab akan zanin data daura.
“Nima bana jin fita yau bana jin daɗi sam”
Murmushi matar tayi tare da cewa.
“Haba keko ina hasko alkairi atare da fitar nan taki gaskiya kiɗan daure sabida sunfi son irinku ƴan yara shakaf sekinfi kawo light”
Tafaɗa tana mai kashe idanu irin na ƴan duniya.
Rabeta ummul tai haɗi da ɗaukar boket tabar ɗakin.
Da kallo ameera da matar suka bita.
“Rabu da ita Anty ladi lafiya lau muka fita amman duk tai wani iri kamar wadda akama sukuwa”
Ameera ta faɗa tana dariyar iskanci.
Taɓe baki anty ladi tai tare da cewa.
“Ki shawo kanta ami sabida wannan fitar mai lasisi ce ok sena jiki yadda kukai”
Tafaɗa haɗi da ficewa daga ɗakin gaba ɗaya.
Da sanyi jiki ta ƙarasa gaban famfo ruwa ta tara haɗi da nufar toilet ɗinsu dake tsakiyar gidan……….

Da sanyin jiki take watsa ruwan ajikinta batare data sanya sabulu ko soso ba,har ta kammala ta ɗauro zani tare da saka hijab a samanta ta ɗauki bokitin datai wankan dashi ta fito zuwa waje.
A bakin famfo ta ɗaura alwala ta wuce ɗakinsu.
Zaune ta tarar da Ameera ta baje Shisha a gabanta tana zuƙa.
Lumshe idanu tayi haɗi da raɓewa ta isa gaban wadrobe ta ɗauki doguwar riga mai sauƙin nauyi ta sanya ajikinta sallaya ta shinfiɗa ta soma gabatar da sallar la’asar.

Tajima tana addu’a acikin sujjadarta ta ƙarshe kafin ta ɗago tana share hawayenta haɗi da sallama tai addu’a sosai acikin tafikan hanna yenta, ta shafa batare data zare hijabinta ba, Ta kwanta a saman sallayar idanunta lumshe tana hasko Kamannin A’A kamar yadda taji abokinshi ya faɗa.

Hannunta dafe da saitin zuciyarta ita kaɗai tasan mai takeji game dashi.
“Kekam lafiyan ki duk kin sauya kuma ba haka kika tashi ba ko furar rufaidar ma da kikace nayo miki order baki shaba?”
Ameera ta dafe mata kafaɗa cike da kulawa.
Daga kwancen ta furta magana cikin sanyin jiki kamar ba ita ba.
“Ameera kaina ke ciwo sannan ina son naje city star,naga wannan guy ɗin?”
Da sauri Ami ta zabura tana washe bakinta tare da cewa.
“Kardai Bangis wayyo kice mutumina ya taki sa’a kinsan kwa bai jima da turon sakon kuɗi akan nasha mai kanki ba”
Ami tafaɗa da saurin ta cike kuma da murna marar iyaka.
Tashi tayi zaune tana girgizama Ameerah kanta.
“Ami bafa bangis ba, wallahi ɗazu naje city star wajan Alhaji mudi kwatsam nazo zan sauka na haɗu da wani Haɗaɗɗan mutum wanda atake anan naji ya tafi da dukkan tunanina sedai kallo ɗaya nai masa nasan ba harkarmu guda ba don naga kallon rainin da ƙyamar daya kemin, Ameera yaya zanyi zuciyar data tashi da tsanar ɗa namiji sabida tabon dayay mata ayau ta afka ga son wanda bai son tana yi ba ƙilama bazan kuma ganinshi ba har abada”
Tafaɗa tana mai sakin marayan kuka.
Baki da hanci Ameera ta saki yau UMMUL-KHAIRI mai sa maza jinya itake kuka akan wani namiji? lallai so makahon zuciya ne inji bahaushe.
Cikin tattausan lafazi mai daɗi ameera ta janyota jikinta.
Tana mai share mata hawayenta.
“Dena kuka Ummul babu wani ɗa namiji daze ganki baiji wani abuba idan bai soki dan komai ba yasoki dan baiwar kyau da sura da Rabbi ya baki ina ji ajikina zaki sami soyayyarshi domin nasanki babu wasa”
Tafaɗa cike da ƙarfafa gwiwa.
“Baze soni ba kallon tsana yake min ba ajina bane”
Tafaɗa tana wani taɓe baki kamar wata karamar yarinya.
“Dena faɗin haka babu wani ɗa namijin daze fi karfin ɗiya mace muddin tasan lagonshi tofa magana ta ƙare maza share hawayenki ƴar ƙanwata dena kuka insha Allahu komai zezo mana cikin matiƙar sauƙi”
Ameera ta faɗa mata hakan cike da kulawa tare da kwantar mata da hankalinta.
Kamar sokuwa tahau goge hawayen sedai Batajin zata iya kai komai cikin bakinta a halin data ke ciki a yanzu Seda ameerah taga ta dena kukan sannan ta mike zuwa mazauninta tana cigaba da zuƙar shishar ta.


Tsaki yaja ƙasa ƙasa tare da tattare takardun nashi masu matiƙar mahimmanci agare shi.
Batare daya yima Abokin nashi magana ba ya wuce Ɗaki mai number ta biyar abin mamaki ƙofar room ɗin abuɗe take sannan da alamun anyi amfani da ɗakin sedai ba’a ɓata shi ba sannan ma’aikatan Hotel ɗin basu gyarashi ba da alamun yayi mistake ɗakin daze shigane, agajiye ya zube takardun dake hannun shi tare da zama akan stool ɗin gefen gadon ɗakin yana dafe kanshi dake mai ciwo ya gaji over domin tuƙi daga abuja zuwa kano akwai ɗunbin gajiya wayarsa dake aljihun gaban rigarshi ita ke ringing da lumsassun idanun shi ya ke kallon screen na wayar bayan ya zarota.
My Baby aka rubuta a saman da wani tsadaddan murmushi ya ɗauka yana karawa a saman kunnen shi.
Daga cikin wayar.
“Hellow nawan nika ɗai ina ta jera maka kira baka ɗauka ba?”
Daddaɗar muryar matarshi abar sonshi Basmah ita ke dukan cikin dodon kunnen shi.
Miƙa yayi daga zaunan alamun gajiya taci karfinsa alamun bai saba dogon driving ba kana yace.
“I’m sorry my love ina driving ne ban lura ba yanzun nan na sauka kano ko kayana ma ba’a kawo min ba”
Yafaɗa cike da nuna mata kulawa.
Shagwaɓe mai tayi tare da cewa.
“Ayyah baby sannu bara na barka hakan amman pls kayi wanka seka sha tea nasan ze rage maka gajiya”
Tafaɗa kamar zata mai kuka!
Lumshe idanu ya kumayi tare da mannawa wayar hot kiss batare dayay magana ba ya katse tare da jefa wayar shi tsakiyar gadon.
Da sauri ɗaya daga cikin ma’aikatan Hotel ɗin ya turo ƙofa rissuna wa yayi har ƙasa tare da cewa.
“Yallaɓai ba nan ne ɗakin dasuka kama maka ba room number 1 ne nan anyi amfani dashi bamu ma gyara ba no need ka zauna ciki”
Shafa saisayen sumar kanshi yayi.
“No problem kawai a gyaran bathroom nai wanka nan ɗin ma is ok”
Yafaɗa tare da kama yatsun shi yana matsawa suna bada sautin ƙas-ƙas.
Cikin mintuna goma wannan ma’aikacin ya kuma gyara ɗakin ya sauya bedshirt haɗi da gyara toilet wanda ba’ama ɓata shiba, Bayan ya kammala ya miƙa mai keyn ɗakin haɗi da amsar nashi wancan ɗin.
Sannan ya juya yana ƙoƙarin fita.
“Dan Allah ga keyn motana ka ɗauko min bags ɗina suna boot in ban takuraka ba”
Haɗaɗɗiyar muryarshi ta karade ɗakin cikin sauri ma’aikacin ya karɓa haɗi da fita mintuna kaɗan ya dawo mai da jakun kuna guda2 godiya yayi masa haɗi da ɗaukarsu ya fara firfito da kayan cikinta.
Sosai ya gyara kayanshi tsaf ya fito da system ɗinshi ya jona a caji sannan ya nufi Toilet sedai tsananin ƙyamƙyami irin nashi ya hanashi shiga sabida bai san adadin mutanan da sukai amfani dashi ba.
Dafe kanshi yayi yana ta jan tsaki akai akai ahaka ya faɗa bayin amman seda ya kuma wankewa tass sannan ya iya watsawa jikinsa ruwa……..

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE