INA DA HUJJA CHAPTER 4 Ayshat Ɗansabo Lemu

*Koda Khairiyyah ta shanye kokon sai ta koma ta kwanta,tana sauraran yadda maran ta ke cigaba da murɗawa.Rintse idanunta tayi wasu hawaye na sauka mata,bakin ta kawai take iya motsawa tana addu’a cike da tsananin jin azaban da bata taɓa tunani ba.Don a iya wauta da tunanin ta ta ɗauka haka kawai ake ganin jinin yazo ba tare da wani ciwo me wahalarwa ba,ashe abin ya wuce duk yadda take hasashe.Wani amai ne da ya taso mata yasa ta saurin tashi tana kai hannu da dafe maran ta da yai azaban ɗaukan zafi.Sabida tsananin azaban da take sha,sosai take kwara aman duk kokon data sha gaba ɗaya sai da ta dawo da shi,ta koma tayi rub da ciki bisa katifan tana maida numfashin wahala.A haka Inna ta sake shigowa ta same ta ganin halin da Khairiyyan ke ciki ya sa ta ƙwalawa Ahmad kira.Ya shigo ɗakin yana faɗin “Gani Inna ya jikin Khairyn?”

“Da sauki kenan kaga wani aman ta sake da alamu har yanzu ciwan maran bai faɗa mata ba.Idan akwai kuɗi a jikin ka maza kaje chemist ɗin Ustaz ka samo mata magani,ko Allah xaisa idan ta sha na baturen ciwan yayi saurin faɗa mata.Idan baka da kuɗin ka amso maganin haka nan idan mun samu wankau na yi saina biya sa da kuɗin,kace masa maganin da me ciwan maran al’adah zata sha ta samu sauƙi.”

Inna ta ƙare maganan tana fita don ɗakko tsintsiya da fakan da zata kwashe aman.Ahmad ya fita don tafiya amso maganin bashi kaman yadda Innan tace,don kuwa bashi da ragowan kuɗi a jikinsa.Dama da ɗari biyu ya kwana shine kuma ya amso musu ƙosai da shi don su haɗa da kokon da Inna ta dama su karya dashi.

Lokacin daya dawo amso maganin ya tadda Khairyn taji dama-dama don har Inna ta taimaka mata tai wanka,da ruwa me zafi sosai ta gasa maran da take complain ya riƙe,kuma sosai taji daɗin hakan don maran ya ɗan saki sai kaɗan-kaɗan yake murɗa mata,kuma har lokacin jinin bai fara fita ba bare ta samu rangwami.Sannu yai mata yana nuna mata yadda zata sha Dose ɗin maganin,ya fice don zuwa yai wanka ya shirya tafiya gareji.Don goma har ta wuce shiyasa yake ta sauri-sauri,bayan fitansa Khairiyyah ta sha maganin ta koma ta kwanta,baccin wahala na yin awon gaba da ita.Koda Malam ya sake leƙowa don duba jikin nata sai ya tadda tayi bacci.

Hamdala yayi yana addu’an Allah ya bata lafiya,don sosai yake tausayin ta don shi zai ƙarar da irin wahalan da su ke sha lokacin Inna na ganiyan fama da ciwan maran,har fargaban zuwan watan ta yake sabida yadda take shan wahala.

Misalin ƙarfe ɗaya Khairiyyah ta farka daga baccin.Cikin ikon Allah ciwan ya faɗa mata don sam bata jin murɗawan maran,sai dai ya ɗaure kaɗan dai hakan yasa ta miƙewa ta fice don zuwa bayi.Bayan ta yi fitsarin da ta je yine tana shirin yin tsarki ta ga jinin ya fara ɗiga,hakan ya sa ta jin wani yamm! tsigan jikin ta na zuba,domin ita akwai ta da ƙyanƙyami,haka tai tsarkin tana faman yamutsa fuska da tunanin yadda zata maida pant ɗin jikin ta,kada jinin ya sake fitowa ya ɓata mata.Ta sha raka Ruky siyan pad a chemist idan tana jini,don ita takai 2yrs da farawa kuma bata taɓa ganin tana shan wahala irin yadda ita yau take sha ba,sai tunaninta ya tafi ga yadda za’ai ta kula da kanta ita gashi bata da abin tare jinin bata kuma da kuɗin siya daga ita har Innan nata,duk ɗan kitson da take yi da wankin da su ke yi ba kasafai kuɗin ke taruwa ba.Wannan tunanin yasata jin hawaye masu zafi suna zubowa daga idanunta,tana ayyana irin yadda ,ƙunci da raɗaɗin talauci yake da ciwo.

Jikin ta a matuƙar sanyaye ta fito daga bayin,ta nufi ɗakin ta don tasan dai ba batun yin sallah tunda jini yazo,har sai ta samu tsarki domin sun riga sun wuce babin jinin haila da hukunce-hukuncen sa.Hakan yasa ta san komi game da zuwan jinin har zuwa lokacin samun tsarki,zama tayi daga gefen katifan ta tana kai hannu ta rafka tagumi.A haka Inna ta shigo ta same ta cike da kulawa ta isa ta zauna kusa da ita.Tana kai hannu ta sauke tagumin da Khairiyyah ta yi tana faɗin “Ni kam bana son wannan ɗabi’a na tagumi Khairy sanar dani miye damuwan ki a yanzu ko jinin yazo ne?”

Khairy tayi saurin yin ƙasa da kanta tana jin wani kunyan Innan na kama ta.Ta gyaɗa kai a hankali hawayen da take riƙewa suka zubo,cikin murya can ƙasa take faɗin “Inna ban san da abinda zan tare jinin ba idan ya sake zubowa,na ga Ruƙayyah Always take siya idan tana yi,ni kuma bani da kuɗin siya.”

Ta ƙare maganan tana fashewa da kuka don ita bil haƙƙi tana ƙyaman yadda jinin zai ɓata jikin ta, ƙyanƙyamin sa ta ke ji sosai.Inna ce ta dafa kafaɗun ta tana faɗin “Khairy kiyi haƙuri ni kaina na so ace wannan abu yazo ina da ɗan kuɗin siya miki wannan abun kiyi anfani da shi,sai dai hakan bai samu ba.Bani da ko sisi kwana biyu ma wankin da muke samu shiru bai samu ba,tun da Maman Haneef ta yi tafiya dama ita ce me yawan kawo wankin.Amma kiyi haƙury yanzu bari in nemo miki ƙyalle in koya miki yadda zaki ƙunzugu da shi,kafin Allah ya kawo hanyan da zan siya miki audigan matan.”

Khairy ta gyaɗa kai kawai tana bin bayan Inna data fice da kallo,wani abu na sukan zuciyanta ta lumshe idanun ta ta buɗe tana ayyanawa a zuciyanta ko sai yaushe ne zasu fita daga wannan kuncin talaucin da suke ciki? ga tsadan rayuwa kullum rayuwan sake tsada yake,ga masu kuɗin kullum kaman ana ƙeƙashe zukatan su ne da rashin tausayin na ƙasa dasu,sai ƙalilan daga cikin su.

Har Inna ta dawo ɗauke da tsummokaran da zata ba Khairyn,Khairiyyah na duniyan tunani sai da Innan tai gyaran murya sannan tai firgigit tana sauke manyan idanun ta akan Innan,tare da bin tsummokaran da Innan ta aje da kallo.Sam Innan ta kasa duban cikin idanun Khairiyyan da ta ke hango tsantsan damuwa a cikin su,wasu hawaye masu ɗumi take ji na taruwa a idanunta tana yaƙi dasu,don ko kaɗan bata son sake karya zuciyan yarinyar na ta.Sai kawai ta fara gwadama Khairyn yadda zatai anfani da tsummokaran,idan sun ɓaci ta cire ta wanke ta sake yin wani kunzugun da wasu,ta ɗaura da sake mata bayanin yadda zata kula da kanta.Ta shiga mata nasiha da gargaɗi akan sake kama kanta,duk da ta san Khairiyyah tana da nutsuwa amma a shekarunta dole sai da tsoratarwa tare da ƙarin nasihohi a gare ta.Daga ƙarshe ta umurci Khairyn da ta tashi ta je ta kintsa kanta ta zo ta ci abincin rana gashi can an kammala.

Khairiyyah ta kammala cin abincin nata kenan,tana ƙoƙarin shan magani ta jiyo sallaman Ruky Sulaiman.Ta amsa sallaman tana faɗin “Ruky gani a ɗakin Inna shigo nan.”

Ruƙayyah tai sallama a ƙofar ɗakin Innan Khairiyyah ta amsa tana bata izinin shigowa,ta shiga ta zauna bisa kujera tana ƙarewa fuskan Khairy kallo,wanda kallo ɗaya zakai ma fuskan ka gane taci kuka don idanun ta har sun tasa sosai.Ruƙayyah ta cire Hijab ɗin jikinta tana faɗin “Lafiya beauty ɗin Inna na ga idanunki sun kumbura haka?”

Kafin Khairiyyah ta bata amsa Inna dake uwar ɗaki ta fito,hakan yasa Ruƴayyah zamewa ta gaida Innan,Inna ta amsa cike da sakin fuska tana tambayan ta mutan gidan ta bata amsa da kowa lafiya,daga haka Innan ta fice zuwa ɗakin Malam ta bar Ruƙayyah da Khairiyyah,Khairy ta taɓe baki tana faɗin “Ke dai bari kawai Ruky yau nasha mutuwa zanyi,dama haka ake uban ciwan mara idan za’ai wannan jarababban abun,shine baki taɓa gaya min ba.Kika ce babu wani wahala,to ni kam yau na gama gane shayi ruwa ne,sai fa yanzu na samu kaina in faɗa miki.”

Tuni Ruƙayyah ta gama gane inda maganan Khairy ya sanya gaba,hakan ya sa ta yin dariya ta na faɗin “Ayyah ƙawata kice yau kin zama babba,Allah sarki ki ce ke na ki da ciwan mara yazo,ni kam tsakani da Allah bani ciwan mara me ɗaga hankali sai dai kaɗan,barni dai da tashin zuciya sannan kuma kirjina kan cika sosai baya ga hakan bani wani shan wahala,ki ce yau kin sha kuka kin ɗagawa Inna hankali gaki da uban raki.”

Khairy ta zabga mata harara tana faɗin”Hmmm! ke baki ji irin azaban da nasha bane Ruky sai da nai amai har sau uku fa,amma cikin ikon Allah tun da na sha wannan maganin naji sauƙi don har jinin ya fara fita.”

Ta ƙare maganan da nuna wa Ruky kwalin maganin da ke gaban ta,Ruky ta kai hannu ta ɗauki maganin ta na dubawa.Kafin ta aje ta na duban Khairiyyah ta ke faɗin “To yanzu dai an mata kitson zai samu ko mu haƙura ba zaki iya ba?”

Khairy ta saki murmushi ta na faɗin “Haba dai bari mugani zan iya,yanxu dai bari in zubo miki abinci ki ci tukun.”

“No Khairy wallahi sai da na ci abinci na fito gida.”

Khairiyyah ta zabga mata harara tana faɗin”Ke dai wallahi kina da damuwa Ruky,ko yaushe ki ka shigo akai miki tayin abinci baki ci sai kace wata baƙuwa.”

“Kai Khairiyyah ban san sharri ke ma kin san indai ban ƙoshi ba ina ci,kawai dai yanzu ɗin na ƙoshi ne.”

Khairy ta ɗauki plate ɗin data gama cin abincin na ta,ta nufi hanyan fita ta na faɗin”To ai shikenan sai ki taso mu je ɗaki.”

Kitchen ta wuce ta kai plate ɗin ta aje ita kuma Ruky ta nufi ɗakin Khairy.Sun fara kitson suna hiran makarantan su Ruky,hakan ke sake kwaɗaitar da Khairiyyah son komawa bokon ita ma sai dai babu hali.Kitso sosai ta yarfa ma Ruƙayyan kaman yadda ta saba fito da ita,ganin sun gama da wuri har lokacin da sauran time a kira la’asar,sai Ruky tasa Khairy ta sake biya mata wani karatun Hadith da aka biya musu jiya bata iya fassaran sosai ba.Suka ɗakko littafin Rukyn na karantawa ita kuma Khairiyyah na fassara mata,har sai da ta tabbatar Ruky ta iya fassaran duka sannan su ka aje littafin,Ruƙayyah na tashi ta fice don ɗauro alwala.Ita kuma Khairiyyah sai ta miƙe don fara shiri tun da ita babu sallah akan ta har sai ta samu tsarki.Huɗu dot su kaima Inna da Malam sallama su ka fice don wuce wa Islamiyan,su na fita sun zo dai-dai masallacin layin na su wanda gida biyu ya raba tsakanin masallacin da gidan su Khairiyyah,Khairy ta ɗaga kai tana duban yadda aka yaye kwanon masallacin,ta mai da duban ta ga Ruƙayyah ta na faɗin”Ruky kin ga har an fara shirye-shiryen zuwan Ramadan,an fara gyaran masallaci har kwanon saman za’a sabunta da alama.”

Tayi maganan cike da farin ciki domin ita duk shekara idan za’ai gyaran masallacin abin na birge ta,tun ba tai girman haka ba musamman ta ga anyi fenti masallacin ya haska layin nasu,dama kuma shine kaɗai masallaci a layin nasu.Ruky ta ɗaga kai itama tana duban yadda ake cire rufin masallacin ta na furta.”Wallahi kuwa gyara za’ai sosai da alama,nima tun da zan fita skull na ga an fara aikin da na dawo gida ne na ji Sufyan ɗin gidan mu na faɗin wai me sabon gidan can ne ya bada kwangilan gyaran masallacin,har dasu AC duk za’a saka a masallacin,ba kiji yadda abin ya birgeni ba.”

Khairiyyah ta murmusa cike da farin ciki ta ke faɗin “Allah sarki aiko ya kyauta sosai,masallacin zai ƙara kyau kenan ya zama na ƴan gayu,har da su Ac.”

Su ka sanya dariya baki ɗaya su na cigaba da tafiyan su a nutse,yauma dai da su ka zo dai-dai sabon gidan da ba su san sunan me gidan ba,sai da su ka tsaya su ka ƙarewa gidan kallo kafin su wuce su na sake tattauna tsaruwan gidan,har Ruky na faɗin ita dai har addu’a ta ke idan masu gidan sun tare Allah kawo sanadin da zata shiga cikin sa ta ba idon ta abinci,don ta tabbatar tsaruwan gidan aciki yaci uban daga waje da su ke hange su na santi,ita dai dariya kawai tayi bata ce komi ba don bata da abin cewan,tun da tasan basu haɗa komi da masu gidan ba kuma bata ga ta yadda za’ai wani dalili ya sa ta iya shiga gidan ba musamman idan akai duba da yadda igiyan raƙumi yayi nesa da ƙasa,haka su ka isa Islamiyan su ka nemi kujeran zaman su su ka zauna bayan sun gaggaisa da ƴan ajin,kafin Malamin Qur’ani ya shigo Malam Kabeer ya fara rattafo musu kira’arsa me daɗin sauraro cikin suratul Rhum.

Da aka tashi Khairy ita kaɗai ta kamo hanya don Ruky ta sanar da ita zata biya ta amso saƙo a can ƙasan layi.Hakan yasa Khairiyyah ke takowa a hankali kanta a ƙasa cike da nutsuwa,har ta zo za ta wuce wannan sabon gidan kaman ance ta kalli gate ɗin gidan sai ta ganshi a buɗe,haka kawai ta samu kanta da tsayawa tana hango tsaruwan haraban gidan daga ciki,katuwar motace na wani company ta hango ana sauke wasu kaya,bata jima tana kallon cikin haraban ba ta ga an zuge gate ɗin hakan yasa ta cigaba da tafiya tana sake jinjina kyawun gidan,har ta isa gida.

Kwanakin da suka biyo baya haka Khairiyyah tayi su,cikin matsi da takuran ciwan mara wanda indai ba magani ta sha ba tofa bata da sauran sukuni,gefe guda ga ƙyanƙyamin wankin tsummokaran da ta ke tare jini da su,da ke addaban zuciyanta.Har lokacin Inna bata samu kuɗin siyan mata Pad ba,sunyi wankau har sau biyu amma kuɗin da suka samu duk wajen hidiman yin cefane yake ƙarewa waima don har lokacin kayan abincin da su ka siya bai ƙare bane,hakan ya sa ta gaza samun halin siyan Pad ɗin wanda Inna ta jinjina tsadan sa da ya kai har kusan 500,ina talaka ko ina iya siyansa ana fama da ta ciki,haka nan Khairiyyah tasa dangana tana anfani da tsummokaran badon ranta na so ba,gashi duk in za ta tafi islamiya a tsarge ta ke har ta je ta dawo tana alhinin kada jinin ya ɓata jikin ta har ya fito sarari a gani.

A haka dai tayi kwanaki biyar sannan jinin ya ɗauke ta samu tai wankan tsarki,ta cigaba da ibadan ta.Gashi kwana kin gabatowan azumi na ta ƙaratowa,yayin da ya kasance ba su da komi ɗan cefanan da su ka yi ya ƙare.Sun sake komawa ƴar gidan jiya sai Ahmad ya fita gareji ya dawo su ke samu suci abincin rana,shi ma idan ya dawo da kuɗin kirki kenan,idan bai dawo da kuɗi sosai ba sai dai ya tsaya a kasuwan tudun wada ya siyo musu garin rogo shi za su ci da rana da dare kuma ko oho.Idan sun sama wanki ne ko Khairiyyah ta samu ƴan kitso shine zasu samu su ci abinci sau biyu a rana.Haka rayuwan ke ta gara musu cikin kunci da rashin wadata don ma suna da tsananin tawakkali da juriyan danne raɗaɗin babun da suke ciki,ba don haka ba da tuni sun fara bara,shiyasa duk yadda Inna ta kirfa zuwa Katsina don yin ta’aziyan yaron Zainabu Fahad daya rasu abin ya garara,don ba ta ga ta yadda za’ai kuɗin motan zuwa Katsina ya haɗu musu ba a halin da suke ciki,hakan yasa ta haƙura da zuwa sai kiran wayan Yayah Kariman ta yi ta turo da number ɗin Zainabun ta sa Ahmad ya kira mata tai mata gaisuwa ta waya,yadda Zainab ɗin ta ke amsa gaisuwan na ta alalace ne ta wayan,ya sake ɗaga hankalin Inna da sake jefa zuciyan ta cikin ƙunci da zafin wannan lamari.Ta yadda qanwarta ciki ɗaya ke amsa gaisuwan ta a wulaƙance sabida ita ɗin ba wata bace,sai ta gode ma Allah da bai sa sun je gaisuwan bama da bata san irin wulaƙancin da zasu gano ba.Ranan sai da ta shiga ɗaki tai kuka sosai tana sake Allah wadai da lalacewan zumuncin wannan zamani.

A cikin irin wannan halin na matsi Azumin watan ramada ya riske su,ba tare da su na da ko ƙwayan marasa ko gero ba,sai yammacin da ake saka ran ganin watane,Guggon Ruƴayyah ta aiko musu da tiyan garin tuwo da na shinkafa ƴar hausa,ita ma cikin wanda ƴan uwanta su ka tara mata ne.Ta tuna da Inna da halin da su ke ciki ta ɗibar musu don tasan su na buƙatan taimako sosai.Aiko hakan ba ƙaramin farin ciki ya sanya zukatan su Mallam aciki ba.

Cikin rahaman ubangiji sai ga Ahmad shi ma ya dawo,ɗauke da leda daya samo sadakan gero da masara da wani me kuɗi ya kawo garejin su a raba.Kasancewan mutumin a garejin su ake masa gyaran motocin sa ko na iyalin sa idan sun sami matsala,ɗan kuɗin daya dawo dashi 500 naira shine ya bayar yace ayi cefane dashi su sami abinda zasu ci da dare da kuma lokacin sahur……..✍

Ina masu son a tallata hajar ku muna maraba da ku,sai ku tuntuɓe ni ta wannan line ɗin don neman ƙarin bayani 08167768704

Wanda za su yi payment tun yanzu za ku tura kuɗin ku ta wannan asusun 0504192664 aisha ibrahim ɗansabo GTbank.

Shaidan biyan ku ta nan 08167768704.

Kaman yadda kuka sani tsarin biyan kashi biyu ne,masu son samun updet sau biyu a rana zasu biya 500,sau ɗaya a rana kuma zasu biya 300 kaman yadda aka saba.

Masu turo katin waya zaku turo katin MTN ta wannan line ɗin 08167768704 shaidan biyan ku ma ta line ɗin zaku tura.

Shatu Ɗansabo ce 

DANNA DOMIN CI GABA

https://arewabooks.com/book?id=62b735ad7f7fce1c0ba4d533

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE