KUNDIN KADDARATA CHAPTER 21 BY HUGUMA

Hannu ya sanya ya amsa,sai ya latse wayar ya kasheta baki daya ya ajjiyeta gefansa yaci gaba da aikinsa,wanda yana duba yanayin ginin gidansa wanda a yanzun ake daf da kammalashi
“Sai da na gaya miki kada ki daga” ya fadi idanunsa na kan computer din,cikin wata iriyar mutuwar jiki da kasala ta lallaba ta koma kan kujerar data tashi taci gaba da kallonta,saidai sam ta daina fuskantar komai,wani abu mai kama da zazzafan kishi ne ya shiga taso maga,ta dinga ambaton sunan Allah har zuwa sanda suka qare film din ta koma dakin gadonta.

           Sam bacci yaqi zuwa mata face nazari da take tayi ita kadai har mukhtar din ga gama abinda zaya yi ya cimmata akan gadon,jikinsa ya janyota sannan cikin taushin murya yace
“Meke faruwa ne sumy uhmmm?”
“Babu komai” ta furta can qasan maqoshinta
“Ban santa ba nina sumayya,abinda kawai na sani customer dina ce,tazo shago na siyayya ita da ‘yan uwanta,ta buqaci number dita saboda koda zasu tashi zuwa wani lokaci,tun daga ranar take matsanta min da kira ba yau ta fara ba,na gargadeta na kuma ja mata kunne amma bata ji ba,wannan shine abinda na sani” shiru sumayyan tayi taba nazarin maganar,sosai wani kishinsa ke taso mata
“Allah ya kyauta” ta iya cewa kawai,sai ya juyo da ita ta fuskanceshi
“Haka ma kadai zaki fada ko?,wato ma baki kishi na kenan sumayya” ya fada yana matse mata yatsu har sai da taji zafi ta saki ‘yar qaramar qaara,sai ya hade bakinsa da nata cikin wani irin salo da ya mantar da su komai

         ***     ***       ***

            Ta maida kiransa ya zame mata tamkar ibada,idan ma bai daga ba zata yita jelan tura masa saqonni iri iri wadanda dukkaninsu a akwatin share saqonni yake zuba su.

           Sau tari wani abun dariya yake bawa sumayya,tana mamakin yadda mata suka sauke farashinsu ya fadi qasa warwas,tana jin inda ita dince sam ba zata iya haka ba,ko babu komai akwai kunya irin ta diya mace,duk da ta sani cewa koda matar ma’aiki ta farko nana khadijatul kubra ta nemi ma’aiki da ya aureta,amma bata irin wannan sigar bace,ta siga ce mai tsafta,mai ban sha’awa mai cike da hankali nutsuwa da kuma KARAMCI,sa’an nan ta nemi a aureta a inda take da yaqinin samun qauna da kulawa,a ‘inda ko babu qauna akwai tausayi girmamawa da kuma MUTUNCI.

            Sau da dama idan saqonni da kiran ZAINAB ya ishi mukhtar yakan zauna yayita sababi,sai ta sa baki da haqurqurtar da shi,wani lokaci kuma ta zolayeshi shi kuma ya bita da harara,ko ya ranqwashi kanta,a haka lamarin yaci gaba da wanzuwa har tsawon watanni uku cur babu sassauci haka na babu sauyi.

Wace ce zainab?

       Zainab haifaffiyar garin kano wadda ke zaune cikin unguwar sheshe,suna da rufin asiri dai dai gwargwado,gida ne wanda ya kasance ya samu rarrabuwar kai da sabanin mabanbantan ra’ayi ga jama’ar gidan,maman zainab itace amarya a cikin gidan yayin da zainab ta kasance ‘yarta ta uku baya ga maza biyu da ta biyo,mama amarya mahaifiyar zainab ta zamewa mata biyu data tarar cikin gidan qarfen qafa,babu wanda ke da fada a ji cikin gidan sai ita,ita ke juya kowa ciki harda mai gidan,taci karenta babu babbaka har zuwa lokacin da Allah ya yiwa mai gidan rasuwa aka raba musu gado kowa ya kama gabanshi,koda zainab tayi auren fari mama amarya ba irin mijin da take so zainab din ta aura ba kenan,miji take so ta samu koda ba mai kudi ba amma yana da abun hannunsa,wanda zasu maqale suyita tatsarsa suna tara abun duniya,talaka ne bashir futuk,qarfin soyayyar da zainab din ke masa ya rufe mata idanu har ta aureshi,tayi aurenta ne bayan data kammala kataratun ta na NCE a federal college of education kano wato FCE,kusan zamu iya cewa bashir abokin karatunta ne tare suke daukan lactures course dinsu daya,bayan kammala karatu kuma aiki bai samu ba,sai shagon wani maqocinsu dake kasuwa yake zuwa yana masa jira ana biyansa.

         Duk iya yadda mama amaryan taso ta fahimtar da zainab din taqi fahimta,duk da kusan cewa babu abinda ta baro na daga halayen uwarta,bata cimma nasara ba sai bayan da akayi auren,sukaci soyayyarsu suka cinye,a lokacin da gishiri ya fara fita daga kan kaza ne zainab din ta fahimci bashir bai dace da ita ba,daya bayan daya ta dinga bin sawun duk wata dabi’a da huduba da uwar ke azata kai.

        Cikin watanni biyar kacal suka balle auren,a lokacin tana dauke da ciki na watanni uku,duk yadda suja zo zubar da cikin abin ya gagara,a cewar mama amaryan baya da wani amfani tunda ubansa bai mallaki komai ba bare su saka ran samun wani alfanu tattare da shi.

          Saidai kuma ina,maqaginsa ya riga ya QADDARA sai ya taka doron qasa,bayan wata bakwai ta haife yaronta namiji,ko yayeshi bata yi ba ta soma balle zawarci mai lasisi,a lokacin ta sake haduwa da qawaye kala kala idanunta suka bude,tasan duniya sosai har fiye da yadda uwarta ta sani ta koma dorata akai,hakan ya so tsorata maman har ta soma shirin hanata wasu abubuwan,amma ina…….maqeri ya riga mabada hali,tuni zainab din tasa aka rufe bakin maman da yayyenta maza biyu,duk wani abu da zata aiwatar bata laifi a idanunsu,musamman idan ta samo ta yaga musu.

           Tun randa taga mukhtar zuciyarta ta yaba da shi,bata bata lokaci ba wajen bada sunanshi aka mata bincike a kansa,yadda takeso haka sakamakon yazo mata,mukhtar din yayi dai dai da ra’ayinta,saidai bata qaunar kishiya ko misqala zarratin,amma da ta samu labarin wace sumayya sai hankalinta ya kwanta,ta tabbatar ba matsala bace a gunta,aiki guda daya tak zata mata rana guda ta koreta daga gidan,duk da tana diyar malamai ai bata da maganin kirsa ko?.

        ***       ***      ****

    Hankalinta bai kwanta ba sai data gana da yaya yahanasu,wadda bata tunkareta ba sai data yi shiri sosai akanta,qwarai yaya yahansun taji wata qauna da aminta wa zainab,musamman data ji cewa ta taba haihuwar d’a namiji ma,nan zainab din ta zube mata alkhairai masu tarin yawa tare da tsara yadda zasu cimma nukhtar din duk da taimakon yaua yahansu wadda ke kiran kanta YAAYA kuma UWA a gunsa.

        ***       ***    ***

          Suna shirin cin abincin dare kiran yaya yahanasun ya baqunci wayarsa,dama ya tsammaci hakan saboda tun yammacin jiya da ya ziyarci gidan yaga gilmawar wata cikin layin nasu tamkar zainab din,zuciyarsa bata gasgata masa hakan ba tunda ya riga da ya sani bata san muhallinsu ba,amma duk da haka zuciyarsa bata samu nutsuwa ba har zuwa wannan lokaci.

“Kiyi haquri yaya,amma yanzu bazan samu damar fitowa ba” ya sanar da ita kai tsaye.

“La’ilaha illallahu,mukhtar yaushe kayi wannan riqar,akwai ranar dama da zata zo zan buqaci ganinka kaqi mukhtar” sai ta sa kuka
“Lallai ba shakka sumayya ta gama da mu,taci galaba akanmu ta sake cutar min da d’an uwa” sam baya son yaji kukan nata kamar yadda zuciyarsa ke quna idan yaji tana zagi aibata ko zargin sunayyarsa,hakan ya sanya ya amsa mata kan cewa yaba zuwa.

          Wayar ya sauke yana duban sumayya
“Sumayya bana son fitar nan,ina zargin wani abu”ya fada idanunsa na sauya launi da alamun ransa ya fara motsuwa,kai ta kada
“Ka zargi alkhairi ya mukhtar,tunda kasan koma mene yaya jininka ba zata taba cutarka tana sane ba ko?” Shiru ya danyi sannan yace
“Na sani,amma matuqar abinda nake zaegi taje shirin aiwatarwa wannan karon wallahil azim sunayya ba zata kwashe mana da dadi ba,bazan yarda a ringa walagigi da rayuwarmu” duk da cewa a dunqule yayi maganar amma sai data haifar mata da matsanancin faduwar gaba wanda ta sanya har ta kasa tankawa, ya miqe ya shiga dakinsa ya dauki hularsa ya zura da muqullin babur dinsa don ya riga da ya ajjiye motarsa a inda take kwana ya fice daga gidan.

        Kan kujera ta koma ta kwanta rigingine gabanta na ci gaba da lugude,a hankali ta dinga ambaton
“Ya rabbi yassir wala ta’asir” sabida neman gudun mawa da daukin wajen ubangiji.

           Cikin falonta ya taddata wanda tun kafin ya kai ga shiga ya dinga jiyo dariya da hirarsu ita da yaran da alama cikin nishadi suke da walwala,sallamarsa ya katse hirar tasu,da daya da daya suka fice a dakin ya zama daga shi sai yaya yahanasun.

        Suna kan gaisawa jamila ta shigo da jug guda biyu ruwa da lemo da kofuna ta dire masa,ya dauke kai ya dubi yaya yahansun yace
“Gani” sai ta dan murmusa
“Haba muntari,sai kace wanda ake gutsura,ko ruwa ai ka sha ko?” Sai yaga rashin dacewar yadda yazo matan,ko babu komai tsakaninsu ta bashi shekaru,saboda haka ya rusuna ya tsiyayi ruwan yayi kurba daya ya ajjiye kofin.

          ***    ***    ***

         Tana jin qarar babur dinsa ta miqe da hanzarinta,har ya shigo da shi ya kulle gidan ya qaraso falon tana tsaye,sam hankalinta ya gaza kwanciya a haka ya sameta a tsayen.

         Saidai yanayin da taga fuskarsa ya zabge kaso mafi yawa na tashin hankalin da ta shiga,har ta saki bayyananniyar ajiyar zuciya ba tare da ta sani ba,’yar qaramar dariya ya saki yana fadin
“Me ya tsorataki haka?” Qwayar idanunta ta juya
“Kaine mana,hankalina ya qi kwanciya tunda ka fita”
“To ya kwanta,don babu komai sai alkhairi” duk da bata ji farinciki ko kadan ba yadda ta tsammata sai tace
“To Allah ya lamunce ya shige mana gaba” tayi maganar tana zama.

Ko kadan baiyi mata maganar komai ba,babu abinda yace mata kan hakan har bayan kwana biyu,a tsarinta mutum ce da bata shishshigi cikin lamuran da suka shafi rayuwar wani,hakanan ko da ga mukhtar din ne bata tambayarsa wasu lamura nashi na daban saidai idan shi yaga dama don rad’in kansa ya sanar mata,hakan ya sanya itama bata tambayeshi ba sai tayi zaton wani lamari ne da ya shafesu shi da ‘yar uwar tasa.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE