BA SONTA NAKE BA TAUSAYI NE CHAPTER 3 BY AUTAR MANYA

Saukar tattausan hannu agadon bayanshi tare da wani irin ƙamshin shu’umin daddaɗan turare mai kashe jikin mutum.
Tsintar kanshi yayi da lumshe idanunshi nan da nan jikinshi yahau rawa bakinshi na fitar da wani irin zazzafan huci, kamo ƙasan laɓɓanshi yayi yana faman tsotsa yana fitar da hucin zazzafan feeling ɗin dake taso masa.
Kwanciya tayi lamo a faffaɗan gadon bayanshi idanunta lumshe tana jin tamkar ba’a duniya take ba sabida tsabar shauƙin soyayyarshi dake huɗa sassan jikinta tana jin daman su dauwa ma a haka.
Kanta ta ziro ta gefen wuyanshi hannunta takai dai dai saitin cream ɗinshi ta ɗauko da wani irin salo ta buɗe tare da lakatowa tana kokarin shafa masa agadon bayanshi ƙara manne masa tayi ajikinshi tana goga masa tudun cikakkun kirjinta masu firgita maza.
Cikin wani irin salo mai kama dana tafiyar tsutsa take shafo man a tsakiyar allon bayanshi tsintar hannunta tayi da cigaba da mirzawa aguri ɗaya haka nan kanta har yanzu na saƙale da gefen wuyanshi tana fesa mai sassanyan numfashinta mai cike da wani irin ƙamshi mai kashe jiki.
Hannun ta sauke daga tsakiyar gadon bayanshi ta ƙara mayarwa dai dai saitin ƙugunshi tana wani irin matsawa tamkar tana mai tausa.
“Ashhhhhhh”
Barrister ya faɗa tare da matse cinyoyinshi yana wani irin fesar da huci gaba ɗaya jikinshi rawa yake da wani irin zafin nama yake ƙoƙarin juyowa domin ganin wadda take ƙoƙarin jefa rayuwarshi a masifa sedai juyowar daze yaci karo da tattausan laɓɓan ummul data tura masa cikin bakinshi cikin hatsabi banci irin nata take sarrafa harshenta acikin bakinshi kuma har lokacin hannunta yana bisa saman ƙugunshi gaba ɗaya sun manne sun zama abu ɗaya tamkar zata shige cikin jikinshi haka take faman sarrafa shi.
Ƙarar wayar shi ita tai saurin dawo dashi daga duniyar daya faɗa jikinshi na rawa ya tunkuɗeta ya turata gefe.
Dafe jikin madubin yayi yana wani irin fitar da zazzafan huci bakinshi baya ambaton komai se kalmar.
“Ƙanu innalillahi wa’innah ilahirraju’un”!!!
Kalmar hakan kaɗai itake yawo a saman laɓɓanshi.
Wannan wace irin rayuwa ce mace da ƙoƙarin yima namiji fyaɗe mai ma ya kaishi biye mata? abin da bai taɓa aikatawa ba tsayin rayuwarshi bai taɓa haɗa jiki da mace ba se matarshi wannan wace irin shaiɗaniyyar yarinyace zata biyo shi har ɗaki ta nemi jefashi cikin halaka?
Da ƙyar ya gyara zaman tawul ɗin dake ɗaure a ƙugunshi tare da azamar yayimo jallabiya black colour ya sanya gudun kartaga al’aurarshi kafin ya dai dai ta nutsuwar shi.
Ya tunkaro ta fuskarshi da zallar rashin imani tamkar bai taɓa wata aba wai ita dariya ba.
Raɓe take a gefen gado sakamakon jefawar dayay mata ta haifar mata da buguwa a ƙugunta wanda bata jin ko yatsa zata iya ɗagawa a halin yanzu bare ta iya fita daga ɗakin duk da tsananin tsoron shi dake nausarta wanda tana jin tamkar ta arta aguje domin ceton lafiyar jikinta.
Duk takunshi ɗaya zuwa gabanta yana mai dai dai, da dokawar kirjinta mai ɗauke da tsananin tsoronshi gami da wata irin kwantacciyar soyayyarshi dake huda mata dukkan sassan jikinta.
Agabanta ya zube tare da dafe hannunshi a ƙasa yana mai ƙureta da kallonshi mai nakasa dukkan sassan jikin ma’abocin kallonshi.
Tura kanta tayi tsakanin cinyoyinta tama kasa jure kallonshi gareta.
“Mai ya kawo ki ɗakina?”
Saukar sassanyar muryarshi ma’abociyar nutsuwa kamala da haiba ta dirar mata cikin kunnenta.
Bai jira amsarta ba ya cigaba da cewa.
“Kamar yadda kike gurɓa tacciya shine nima kike son gurɓata mini rayuwa? kamar yadda kike najasa shine kike son nima na zama najasa zaki biyoni har ɗakina kinemi cillani a tarkon shaiɗan?”
A wannan karon muryarshi cike da tsantsar ɓacin rai yake faɗin maganar sedai tsabar nutsuwar shi yasa bai ɗaga murya ba, inma ka gansu bazaka ɗauka magana yake jefa mata ba seka rantse maganar arziki suke duba da yadda yake fitar da maganar a sautin hankali da nutsuwa tare dayin ƙasa da murya tamkar mai yin raɗa.
“To zan baki shawara in ma kina ganin hakan waye wa ne to sam ba waye wa bane sema naƙasu daze janyo miki tare da zubewar mutunci kamarki yarinya ƙarama wadda a tsarin ilimi ba lallai kin kammala karatun secondry ba amman ki zaɓi wannan harkar ta jagaliyanci wadda baxata fusheki komai ba se taɓewa da wahalar rayuwa, ban taɓa ganin shaiɗaniya irin kiba hakan yasa na baki muhalli na matsayin karuwa ƴar jagaliya maiwa maza fyaɗe marar kamun kai daƙiƙiya marar tunani naji ina tausaya miki da wannan makauniyar rayuwar da kika zaɓa ma kanki tabbas idan kika yarda na kuma saka idanuna akan fuskarki zan sauya maki halittar zubinta zan maki mugun tabon da ƴan gidanku bazasu ƙara shaidaki ba”
yafaɗa tare da saurin tashi ya wurga mata wayarta se yanzu ya tuna ashe ɗazu garin sauri bai saka ma ƙofarshi key ba wannan dalilin ya bata damar ratso mai ɗaki harta so jefa rayuwarshi cikin bala’i da dana sani wanda wayar da sukai da basmah ita ce ummul’aba isin na shigar shi cikin halin feeling wanda idan yana ciki yake jimawa bai dawo dai dai ba wanda shine har ita wannan shaiɗaniyar yarinyar ta sami damar raɓar jikinshi.
Daga zaunan datake ta yunƙura kaɗan tana matse fuska alamar har yanzu akwai zafin buguwa a tare da ita amman hakan bai sa ta zauna ba seda ta cigaba da tashi har Allah ya bata ikon miƙewa gaba ɗaya tare da taimakon dafe bangon datai ta kai duba gareshi ya bata baya tare da zira hannu cikin aljihun jallabiyar jikinshi.
Murya can ƙasa mai cike da kukan nadamar abin da tai take furta.
“Nima ba laifina bane laifin zuciya tace wadda batai min adalci ba don ta kaini inda bazata sami muhalli ba! nagode da dukkan furucinka gareni amman kasani atun haɗuwarmu dakai a ɗazu naji duk duniya bani da Aminin zuci idan ba kai ba Ina sonka! ina son ka!! ina Sonka!!! wanda soyayyar ka ce tajani na afka maka kuma ka riƙe a ranka har abada Ummul khairi mai son kace………
“Ƙarya kike munafuka ƴar iska ba sona kike ba sha’awa ta kike irin na matan bariki marasa aji irinki! to ki sani Ni ALIYU DIKKO nai miki nisan da har abada bazaki kamoni ba Domin wuta da ruwa basa haɗuwa kin taɓa ganin tsafta da najasa sun haɗu? to ni dake babu maganar soyayya domin bakya cikin types na matan dana ke burin mallaka a rayuwata”
Yafaɗa yana mai nufota kamar ze shaƙeta.
Da wani irin sauri ta juya har tana ƙara yarda wayarta a karo na biyu tai saurin nufar ƙofar fita muryarta a dakushe ta furta.
“I love you for ever Aliyu”
Tana faɗin hakan ta fice a ɗakin tare da datso ƙofar ta silale a wajan tare da sanya kuka! mai ƙarfi na jimamin Rashin Aliyu na har abada anya zata jure……..?

Girgiza kai ta shigayi tamkar wani naganinta.
“No! bazan iya ba soyayyar Dikko ajini na take bana jin koze cire dukkan naman jikina zan iya rabuwa dashi”
Tafaɗa tana mai cije jajayen laɓɓanta dasukai wata irin kumbura sakamakon tsotar dasuka sha a bakin barrister dikko.
Kafin ta miƙa hannunta a hankali tana ɗingishi take tafiya wadda da ƙyar take taka ƙafafunta.
Cikin mawuyacin hali takai gaban motar ameerah ta buɗe ta shiga taja aguje tabar harabar hotel ɗin wanda hakan yayi dai dai da sanda ake ta faman ƙwaɗa kiran sallar magariba.

Cikin rawar jiki ya faɗa saman faffaɗan lafiyayyan gadon dake ɗakin hannunshi duk suna zube a ƙasan mararshi yana shafa kwantaccen gashin dayay ma wajan ƙawanya idanunshi lumshe suke bakinshi na fitar da zazzafan huci wanda ya gauraye da zazzafan numfashin dayake ta faman fita da sauri da sauri duk irin uban kiran da Basmah ke mai acikin wayarshi bai sami zarafin ɗauka ba, Sabida yadda jikinshi yake a mace sakamakon waccan yarinyar data so kunno mai cajin batir ɗinshi.

Hancinshi har yanzu yana manne da wani irin sihirtaccen ƙamshin turarenta data bar mai wanda bai taɓa ji ko ganin turare mai kamshi kamar nata ba.
Wata irin lallausar fata gareta wadda take tamkar katifa dan tsabar laushi wanda laushin nata ba’a iya fatar jikinta ya tsaya ba har ma da kyawawan laɓɓanta datai nasarar jefasu cikin bakinshi.
Da wata irin kasala ya miƙe yana mai dafe sirrin girmansa data miƙe take neman agaji, A hankali yake taka ƙafafunshi har ya isa bathroom ruwa mai ɗumi ya haɗa A bathtube nan da nan ya shiga gasa jikinsa da ruwan sabida wani shegen zazzaɓi dake neman kawo mai bara, Kafin ya kammala ya ɗauro alwala ya fito agurguje ya sanya fara ƙal ɗin jallabiya yayi ma kanshi ɓarin haɗaɗɗan turarenshi kana ya shinfiɗa sallaya ya soma gabatar da sallar cike da nutsuwa har ya idar anan zaunan yayi azkar haɗi da karanta suratul baqrah wadda ya ɗauki tsayin lokaci yana karatun bayan ya kammala ya shafa kana ya miƙe domin gabatar da sallar isha’i wanda lokacin daya ɗauka yana karatu shine yakaishi har zuwa isha’i yana idar da sallar isha ya kuma bada nafila raka’a biyu ya jima yana addu’a cikin sujjadarshi ta ƙarshe kafin ya ɗago yayi sallama ya shafe jikinshi da addu’a tashi yayi tare da ninke sallayar gami da tube jallabiyar jikinshi waya ya kira da akawo masa Coffee.
Kana ya ƙarasa gaban gadon ya ciro laptop ɗinshi a chraging ya kunnata ya cigaba da aiki da ita har sanda akai mai knocking ya miƙe tare da raɓewa jikin kofar batare da mai miko mai coffeen ya ganshi ba ya zira hannu ya amsa ya mayar da ƙofar ya rufe.
Adai dai sanda ze koma wajan zamanshi yaga wayarta watse a wajan tsaki yaja tare da tsugunnawa ya ɗauka ya kunnata ya koma mazauninshi still aikin gabanshi ya cigaba dayi akan shari’ar daze gabatar a gobe, Gefe guda yana shan coffe wanda zafinshi ke saukar mai da kuzarin daya rasa a ɗazu

Bai kammala aikin ba se wajan taran dare sannan ya kashe laptop ɗin ya aje cup ɗin coffee ɗin a gefe ya mayar da kanshi saman pillow idanun shi na hasko mai kamannin yarinyar ɗazu………”Ina son ka! kalmar data ke mai yawo a kwanyar kanshi kenan wannan wace irin hatsabibiyar yarinya ce dazata iya furta kalmar so agareshi babu tsoro? watsar da shirmenta yayi tare da ɗaukar waya ya kamo numbern Amminshi duk da tarin kiran basmah daya gani amman seya share a wannan karon jin kewar ammi yake wadda ya jima bai jita ba, Jiki na rawa yake danna mata kira kuma a wannan karon yaci sa’a ta ɗauka cikin cool vioce yake gaisheta kafin tafara masa nasiha cikin tsanani da shauƙin soyayyah irin ta ɗa da mahaifi tsayin lokaci suna magana da ammi har sukai sallama zuciyarshi fes ya miƙe ya ɗauro alwala ya kashe ƙwan ɗakin bayan yayi addu’a ya kwanta ba jimawa bacci yayi gaba dashi sabida akwai tarin gajiya atare dashi.

Allah kaɗai yakai Ummul khairi Gidansu lafiya tana rangaji ta kashe motar tare da daddafawa da ƙyar ta ƙarasa cikin gidan nasu wanda ya koma kamar wata kasuwar mata banda kiɗa babu abin da yake tashi daga tsakar gidan mata ne birjik wasuma daga su se pant da bra suke faman tiƙar rawa cikin sautin wakar data cika gidan.
A hankali take dafa bango tana zubar da hawaye ta ƙarasa ɗakinsu wanda harta kai ga ɗakin babu wanda yasan data shigo ma bare a tanka mata.
BARIKI KENAN GIDAN KAZO NA ZO!
Duhu dumɗin ɗakin babu haske alamun ameerah bata ma ɗakin ahaka ta lallaɓa ta aje mata key ta kuma lallaɓawa ta ɗauki ruwa da dafe bango takai bayin tsakar gida ta kama ruwa haɗi da ɗauro alwala a zaune tayi sallah sabida yadda zazzaɓi da zafin jiki ke damunta ahaka ta zauna ta cusa kanta a tsakanin cinyoyinta tana kuka! idanunta jajir fuska jajir kamar mai afolo har lokacin isha’i yayi ta tayar anan saman dardumar bacci ya kwasheta wajan ƙarfe goman dare ameerah ta shigo ɗakin tana furta kalmar.
“washh yau fa kayana sunci ubansu! ke ummul yada bacci ga kaza na siyo mana”
Jin shuru yasa ta tsugunna ta tayar da ita wadda har lokacin zazzaɓin bai saketa ba da rarrabe tahau saman gado taja blanket jikinta nata karkarwa wahalallan baccine yayi gaba da ita.
Duk irin kiran da ameerah keyi mata bata iya farkawa ba haka tai ta baccinta wanda bata farka ba se asubahi.
Da ƙyar ta yunƙura tayi sallah wadda da ƙyar ta gabatar da ita haka ta takure a gefen gado tana rawar ɗari.
Ameerah bata farkaba se wajan goman safiya ganin ummul rakuɓe tana ta mayar da numfashi yasa taɗan tsorata tana furta.
“Ke ummul lafiyarki?”
Girgiza kai ta shigayi.
“Bani da lafiya amerah kaini gidan Hajjah seki je gidanmu ki gayama Bamu kice mata bani da lafiya jina ke kamar zan mutu”
Tafaɗa tana mayar da numfashi.
“a,a ummul bara na kaiki hospital”
Girgiza kai tayi wanda hakan yasa ameerah ta gane gida take so don haka da sauri tayo alwala rana gatsal tai sallar safe ta zira katon hijab bayan ta tarairayo ummul jikinta ta ɗauki keyn mota suka fita.
Motsi kaɗan ummul tace”washhh amerah kimin a hankali”
Wanda hakan ya tabba tar da tai muguwar buguwa a ƙugunta.
Da haka suka shiga mota domin nufar inda ta buƙata…………….

Barrister Aliyu Ali Dikko kuwa se………

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE