KUNDIN KADDARATA CHAPTER 21 BY HUGUMA

Bayan kwanaki biyu*

*** *** *** ***

             a hankali ta shigo dakin ganin tunda ya kammala wanka ya shiga bai fito ba bayan ta kammala shirya abincin dare sa zasu ci,turus ta tsaya tana dubansa.

            Tsaye yake gaban mudubi sanye da sabuwar shaddarsa ruwan qwaiduwar qwai dinkin boda,taje sumar kansa yake,sosai kayan suka masa kyau,sai ta jingina da bango ta harde hannayenta tana dubansa,da alama ma baisan ta shigo ba.

        “Da kyau,irin wannan kwalliya haka da akemin?” Juyowa yayi ya dubeta yana murmushi
“Girmanki ne ai,amma zan danje unguwa tukunna” sai ta danyi jim gabanta na faduwa,take ranta ya darsa mata wani abu,batasan sanda bakinta ya subuce ba
“Zance zaka kenan” juyowa ya sakeyi yana ajjuye cumb din tare da takowa gabanta
“Ya akayi kika canka?,naso ace da kaina na gaya miki my sumy” wani irin abu taji yana ratsata tun daga kanta har qafafunta,yanayin fuskarta ya sauya
“Wai don Allah da gaske kake ko wasa?”
“Da gaske nake mana sumayya,na taba miki irin wannan wasan” ya fada yana qoqarin janyota jikinsa,sai ta zame jikin ta kana ta ja da baya,jikinta ya soma rawa hawaye na shirin zubo mata,hakan ya sanya ta tallafi kanta ta hanyar zama gefan gado,baiyi qasa a gwiwa ba ya bita ya zauna gefanta
“Yi a hankali mana sumayya,me na daga hankali kuma,koma wace zata zo ai kema kinsan a bayanki take ko?” Idanunta ta dago wadanda suka cika da qwalla har sun fara gangarowa ta dubeshi
“Meye na tada hankali kuma,shin ban cancanci nayi kishinka bane ya mukhtar?”
“Kin cancanci fiye da haka ma sumayya,amma kiyi haquri,in sha Allahu ina saka ran wannan karon alkhairi ne auren da zanyi”.

         Cike da mamaki ta watsa masa wani kallon
” wanne alkhairi ya mukhtar?,har ka manta wuyar da mukaci cikin shekara guda kacal?…..”
“No….ki kyautata zato sumayya ba haka na sanki ba….”, qarar wayar sa ce ta katse abinda yake shirin gaya mata,ya sanya hannu ya daga wayar bayan ya hade fuska kamar yana gaban mai kiran
” nace miki gani nan ko?”daga haka ya datse kiran ya maida hankalinsa kanta.

          Hannu ya sanya ya share mata hawayen sannan ya miqe
“Ki bari na dawo zamuyi magana,ki kwantar da hankalinki sumayya kinji” bata iya amsa masa ba har ya sanya hularsa ya fice.

          Wani kuka ta saki bayan da taji tashin motarsa,meke shirin faruwa?,mukhtar ne yau ya tafi zance gun wata a gaban idonta bayan ya ganta tana kuka,mukhtar din da baison bacin ranta balle har yaga hawayenta?
“Ya rabbi yassir amrih” ta dinga fada bayan ta zame ta kwanta saman gadon tana digar hawaye.

          Kimanin awa biyu sai gashi ya dawo,lokacin qarfe goma har ta dan gota ma,a dakin nasa ya sake taddata kwance,da sauri ya isa gareta ya dagata ya zaunar yana duban idanunta da suka kumbura
“Subhanallahi…..sumayya meye haka?” Kamar jira take ta kuma fashewa da kuka,tsawon mintina talatin ya ciyo kanta bayan ya tursasa mata sunci abinci,sai da suka kammala sannan ya nemi magana da ita.

           “Ta hanyar yaya yahanasu zainab ta biyo sumayya,babu yadda za’ayi na iya bijirewa maganar,ni kaina ina jin yadda da auren cikin zuciyata bansan dalili ba,ba kamar auren fa’iza ba hakan ya sanya nake zaton QADDARATA ce zainab” yayi shiru yana jin quna can qasan zuciyarsa da wata iriyar takura,saidai daga sama yana jin kamar dole ake masa ya auri zainab.

         Jin shiru bata ce komai ba ya sanya shi cewa
“Yanzu haka cikin satin nan suke da buqatar na kai kudi a kuma saka rana baki daya,idan da alkhairi sai kiga ta haifa mana yaro ta sanadin haka kema ki samu naki” maganar sai tayi mata duka biyu,batasan sanda ta fashe da kuka ba
“Ta haifa maka dai yaya mukhtar,ni sumayya kam banda cikin haihuwa ai” tayi maganar tana mai niyyar miqewa ta bar masa gun,yunqurin riqota yayi ta kauce tana fadin
“Ka qyaleni kawai ya mukhtar,ka qyaleni kaje kayi aurenka,ka auri wadda zata haifa maka yara,na yarda nikam juya ce” ta qarashe maganar cikin gunjin kuka kamar zata shide,da azama ya riqotan ya rungumeta yana lallashi,sam sai kalmominsa suka gaza yin tasiri cikin zuciyarta,ta kasa bashi hadin kai wajen yin shiru da haquri
“Nace ma ka sakeni kaji ko?!” Ta fada cikin gunjin kuka.

         “Naqi na sakekin!” Ya fada a tsawace
“Yaushe kika koma haka sumayya?,yaushe kika koyi shegen kishi haka?” Ya fada yana kwantar da murya,a hankali ta daga kai tana dubansa,ta karaya sosai wannan karon,banbanci take hangowa qarara cikin idanun mukhtar din,sai ya janye idonsa daga kanta yana tuhumar kansa akan tsawar da ya mata,a tausashe ya janyeta gefan gado ya zaunar da ita sannan ya zauna daura da ita,cikin sanyin murya yace
“Kiyi haquri sumayya,baki na bazai gaji da baki haquri ba yau da gobe da kullum har ABADAN ma sumayya,abu daya zan iya gaya miki shine inaji a jikina dole ne nayi auren nan,bazan iya haqura da shi ba,ki yafemin sumayya,ki yafewa mukhtar dinki mai qaunarki kinji sumayyata” ya fada cikin raunin murya tamkaf mai shirin yin kuka,abinda bata taba ji daga gareshi ba kenan,idanunsa kadai zaka kalla ya tabbatar maka da gaskiyarsa,take tausayi so da qauna sukayi tasiri a kanta,ta rungumeshi tana fadin
“Babu komai ya mukhtar,Allah ne ya halatta maka,kaji tsoron Allah kawai ka kuma yi adalci”
“In sha Allahu sumayyata,ki tayi ni da addu’a” ya fada yana kuma qanqameta.

        ***       ***     ***

       Cikin abinda bai wuce sati uku ba aka kai kudi bayan sati daya mukhtar din ya hada kayan sa rana akwati biyu,bai shawarceta ba hakanan batasan zaya yi ba sai ganinsa tayi da kayansa,yace ta duba tace basai ta duba ba Allah ya sanya alkhairi,haka ya janyesu ya miqawa yaya yahansu,suna guda suna gwalli suka je suka kai kafin lefe ya qaraso,fadi suke Allah ne ya karya alqadarinta,wannan karo kam ta gamu da mai qarfin kurwa,kuma in sha Allahu zama daram tazo.

         Daga can bangaren zainab din ma haka suka gaya mata,sumayya bata barin mace ta zauna da mukhtar ko anyi auren saita tarwatsa abun,dariya zainab din tayi,don tasan komai game da sumayyan,tasan sarai akwai qarin gishiri cikin maganarsu,ta lura mutane ne masu jarabar son kansu da nasu,tilas tayi maganinsu tun da wjri,din ba zata lamunci abinda sumayyan ta lamunta ba,duk da hakan ba zama zatayi ta zubawa sumayyan idanu ba,koba komai diyar malamai ce bata san nasu shirin ba.

          Sosai sumayya ke ganin banbanci wannan karon,ashe da sam ba aure mukhtar din yayi ba,wani rawar kai sosai take gani dangane da shi,sabbin dinkuna yake da lissafe lissafe,tuni ya maida kai wajen ganin an kammala abinda bai kammalu ba na ginin sabon gidansa,ita kanta yace ta kwashe duka kayan dakinta ta siyar ko ta bayar zai sauya mata komai da sabo itama zata tare,saidai abinda ke daure mata kai wani lokaci sai ya hau qunci shi kadai yana fadin baison auren nan,sgifa yana jin tamkar ya fasa,bata san meye matsalar ba,data gaza gano haka sai taci gaba da addu’a kan Allah ya sassauta lamarin ya kawoshi da sauqi,don zuwa yanzu ta tsinke da lamarin kishiya,ashe a da tabbas quruciya ke cinta,batasan dadin mijinta ba sai yanzu,bata san meye kishi ba sai yanzu.

          Kayan lefe ya mata itama yadda ya yiwa zainab kowa akwati hurhudu,bata yi mamaki ba saboda budin da mukhtar din keta samu dai dai gwargwado.

Biki ya rage saura sati biyu abdur rahman ya kawo mata ziyara,ta tarbeshi yadda ta saba,suka gaisa cikin mutunci,saidai wannan karo babu walwala da zolayar da suka saba,da ya tambayeta batayi qasa a gwiwa ba ta sanar masa,sosai ya mata nasihar da ta sake kwantar mata da hankali,ya jaddada mata ta riqi addu’o’inta,sosai taji dadi ta kuma gode masa,bai jima ba sukayi sallama ya tafi dama mukhtar din yazo nema kuma bai taddashi ba ya tafi zance gun amarya zainab. Saura sati daya bikin ta shirya ta je gidan anty dije,da biyu taje don ta samu mai bata shawara,don sosai taji dadin shawarwarin da ta bata wancan karon,wuni tayi mata sur ta kuma qaru matuqa da gaske,taji dadin maganganunta wadanda suka sake kwantar mata da hankali. Ranar da akema amarya jere ranar itama aka yi mata nata jeran cikin sabom gidansu,sai ya zama na tamkar amare biyu ne zasu tare,sosai zainab tayi rawar ganin hadawa kanta kayan daki,duk da haka babu abinda zata gayawa sumayyan,don itama wannan karon dai komai sabo ne,babu abinda ta shiga da shi tsoho banda sutura su dinma kusan rabinsu sababbi ne. Ana ya gobe za'a kawo amarya ta tare,tare da 'yan rakiyarta suka je,sosai gidan ya burge kowa,duk da ba wani kantameme bane amma da girmansa dai dai gwargwado,da fari compound ne wanda ya dauke motar mukhtar din da wani space din daban,sai qofar da zaka bude wadda me dauke da babban falo guda d'aya,daga hagu da dama corridor ne guda biyu,daya na sumayyan daya na amarya,kowanne cirridor akwai daki falle biyu da toilet,daga falon akwai qofa biyu,daya ta kitchen dinsu ne mai yalwa wanda ka masa tsarin tsohon kitchen dinsu kowa da kantarsa,daya qofar kuma idan ka bude baya ne inda aka yiwa 'yan shuke shuke,anan falon mukhtar yake da bedroom dinsa shima,gida yayi dai dai gwargwado sai son barka.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE