BA SONTA NAKE BA TAUSAYI NE CHAPTER 4 BY AUTAR MANYA

Tuƙi yake cike da wata irin nutsuwa wadda a zahiri haka halittarshi take gaba ɗaya soya ke ya ƙarasa gidan hajja don ba ƙaramar wahala ya kwaso ba,da ƙyar yake tuƙin ga unguwar da hajja take mai azabar nisa daga inda ya fito.
Yana tafe yana duba tsarin sauye-sauyen da aka samu a garin sabida yaɗan jima bai shigo ba ahaka ya shiga cikin unguwar su hajja yana tuƙi yana jan tsaki akai akai sabida yadda wajan duk ya cika da tudu da kwari na ruwan sama da akai duk ya sanya hanyar tayi babu kyan gani.

A hankali ya ƙarasar da motar shi cikin layin sosai ya ware ido yana kallon yadda yara ke faman wasannin su rabon shi da gidan hajja tun kafin yayi aure shekaru biyar kenan se yau da Allah ya kawoshi yasan ba ƙaramar mita hajja zata yi mai ba tsintar kanshi yayi da ɗan sakin ƙaramin murmushi kafin ya kashe motar ya fito waje hannun shi riƙe da key tare da wayar shi wadda take faman zuba ringing na kiran da basmah take mai tun jiya wanda bai sami damar ɗagawa ba.

Cikin ɗan zafin nama kaɗan ya ƙarasa bakin gate ɗin lokaci wajan 12:30pm rana taɗan soma fitowa wannan yasa yake ta yamutsa fuskarshi kasance warshi mutum marar son zafin rana da zafi ko kaɗan, Azurfar dake yatsunshi yasa yake ɗan duka gate ɗin cikin ɗaga murya hajja dake ƙoƙarin fitowa take furta.
“Wani marar haƙurin ne ze karyan ƙofar?”
Dariya yaɗan ƙunshe yasan za’a rina hajja da mugun son abin duniya ita komai nata kif kif ne bata son wasa da abin duniya, Harta karaso ta buɗe mai gate ɗin tana faman mita shikuma bai yi magana ba.
tana buɗewa yayi wani irin sauri ya ɗaneta yana cusa kansa a saman wuyanta yana furta.
“I miss you hajjata”
Ture shi tai tare da cewa.
“Da Allah sakar ni gososo dakai zaka ɓallan ƙashi damma ƙashin bana rainon madara bane yasha jar dawar da ya horu”
Taɓe baki yayi tare da langwaɓar da kanshi gefe yayi kalar abin tausayi tare da ce mata.
“Haba hajjata duk duniya in kika cire su ammi wa nake dashi idan bake ba wa ze rungume ni yashafa kaina naji dadi idan bake ba amman shine zaki min haka”
Yafaɗa tamkar ba Aliyu miskilin da magana ma ke masa wuya ba.
“Dallah gafaracan ada dai kake min wannan soyayyar amman ban da yanzu da mace ta fi maka kowa ai yanzu tunda kana da Batsama ai kana da kowa”
Tafaɗa tare da wucewa cikin falonta tana jan mita.
“Wai batsama! ya mai maita sunan Basma da hajja ta lauya ya koma wani daban ya kuwa kwashe da dariyar da bai son ta fito ba wai mai yasa familyn shi suke ɗora laifin su ga Basmah wadda kullum ita burinta taga ta kyautata musu amman sukam kowa ita kowa ita basa duba busy da aikin shi keda sedai suce ta hanashi ziyara kota hanashi yi musu abu.
Shafa saisa yayyar sumar dake kanshi yayi tare da bin hajiya cikin falon haɗaɗɗan ƙamshin turaren wuta ya shaƙa wanda salame tai aikin gyara falon dashi zama yayi a saman three seater yana faman lumshe idanunshi.
“Washh hajja aka womin ruwa ko break fast ban yi ba”
Yafaɗa yana mai ɗora dogayen ƙafafun shi saman kujerar ya riƙe wayar shi yana mai duba tarin kiran da basmah ta bar masa daga jiya zuwa yau ban da messages rututu wanda duk ana lafiya bai ɗauki kiranta ba.
Layin ta ya shiga kira yana mai kwantar da kanshi saman seater ɗin dayake kai.
Ringing! ɗaya ta ɗauka tana mai sauke ajiyar zuciya mai mugun ƙarfi.
“Assalamu alaikum barka da rana”
Tafaɗa sanin bai son ka fara masa magana da hellow! yafi son sallama a tsarin shi.
“Lafiya lau baby ya gida?”
Murya can ƙasa tace.
“Cweet man lafiya tun jiya ina kira user busy amman kuma baka kirani ba?”
Kamar baze magana ba can kuma yace mata.
“Munyi waya da Amminah! shine kuma bacci ya ɗauke ni ɗazu kuma ina court bayan na fito na taho gidan Hajja”
Ya ƙarasa maganar murya cikin sanyi.
“Banji ba gidan hajja? ke nan ba zaka shigo yau ba?”
Tafaɗa muryarta a rarrabe da alamun maganar taɗan soke ta.
“Ban gane baki jiba ina da hausa nayi maki maganar?”.
Ya jefa mata tambayar.
Da sauri ta waske sanin da wa take waya tare da cewa.
“Ce wa nai ka gaida hajja yau zaka shigo nai maka girki?”
Aranshi ya furta kamar ta iya amman a fili se cewa yayi.
“Nima ina son haka sedai na gaya maki naje wajan hajja kinga rabona da ita tun kafin muyi aure idan har na gama da wuri zan iya shigowa idan ban gama da gidan ta da wuri ba sedai gobe sabida tafiyar mota nayo kin sani”
Shuru tayi amman a ranta tana tsinewa Ammi don ita ce zata sanya yaje gidan magananniyar kakar shi wadda sam bata kaunar ya raɓi kowa amman a fili se cewa tayi.
“Allah sarki hajiya hajja tsohuwa mai ran ƙarfe inda ka gaya min zaka je dana bada saƙo an kai mata amman pls ka gaishe min da ita da kyau”
Murmushi yayi yana mai kallon saitin hajja data kawo mai ruwa ta dire mai agabanshi tana zaune ta zuba mai ido kamar ma harararshi take.
“Kona bata ku gaisa gata ma can a zaune”
Ya faɗa tare da miƙawa hajja wayar yana cewa.
“Amsa ga kishiyar ki”
Kamar Basmah zatayi kuka ta fara aro yadda zatai ta gaisar da hajja ɗin tun ma kafin tayi magana hajja ta soma cewa.
“A,a giwar mata bakya bora barka da rana Aci ai kashi ba jini bare cibi”
Dumm basmah tayi batare data ce komai ba shiko murmushi yake don bai kawo magana hajja take gayawa basma ba.
A daddafe suka gaisa basmah tayi saurin katse wayar tana auna maganganun hajja masu cike da harshan damo.
Shiko watsar da wayar yayi gefe tare da sauka ƙasa ya miƙe ƙafafu yana mai ɓalle murfin gorar ruwan data aje mai yay bisimillah ya kafa baki ya shanye.
Seda ya shanye tas sannan ya ajeta gefe yana hamdala.
Haɗaɗɗan tuwan shinkafa miyar shuwaka wadda taji tantaƙwashi se kunun aya dayaji kayan kamshi hajja ta tura mai gabanshi da kanshi ya buɗe flaks ɗin yana zuzzuba wa amman fa duk hankalin shi yana kan abincin wanda yayi missing girki mai daɗi don basmah bata iya wani abinci ba ada wajan ammi yake zuwa yaci daga baya ta hanashi dole suka koma siya a wajan saida abinci idan ko ita tayi baya ciyuwa yace taje ta koyi girki tayi biris.
Tanƙwashe ƙafafu yayi bayan ya wanke hannunshi a tasar wanke hannu yayi bisimillah ya soma kai lomar tuwan bakinshi.
Bai sami zarafin bawa hajja amsar tambayoyin data ke mai akan su ammi da ƴan uwanshi ba seda ya cinye malmala guda sabida bai da cin abinci sosai ko wannan ma dan yana jin yunwa ne.
Sannan ya wanke hannu ya tashi da kanshi ya kai kayan kicin ya kuma tattare wajan bai tsaya ba tsakar gida ya fita ya ɗaura alwala ya fice masallaci.
Wanda itama hajjan lokacin ne ta mike ta shiga ɗaki don gabatar da tata sallar.
Har ta idar ta fito falo ta zauna bai dawo ba wajan awa biyu da fitar shi sannan ya shigo gidan lokacin ya cire ƴar saman suite ɗin dake jikinshi yabar white shirt ya cillata mota hannu riƙe da key ya shigo gidan.
Sallama yayi hajja ta amsa.
“Kaiko Baffa a ina ka zauna har na kammala idar da sallah ta baka shigo ba?”
Shafa kanshi yayi tare da komawa ya zauna.
“Na ɗan zaga gari ne kawai kin san ban son zaman kaɗai ci”
Harara ta ɓalla mai tare da cewa.
“Ai ni ba mutum bace ko?”
murmushi ya sanya yana mai danna cikin wayarshi batare daya tanka mata ba.

Juyi ummul tayi wadda bata ma san duk wainar da su hajja ke toya wa ba sabida baccin data farka daga shi yanzu
“Washh bayana hajja ze karye”
Da wani irin sauri Aliyu ya dubi saitin daya ji maganar macen wadda bai san ko wacece ba sabida bayan data bashi kuma sam shi bai ma san da mutum a falon ba sabida rashin lura da hakan.
Cikin kiɗima hajja tai wajan ummul tare da zama a gefen ta.
“Ta shi ummi naga wajan tun ɗazu kike furta ƙugunki bayan ki in babu dama se Baffa ya kaiki wajan masu gyara a duba maki”
Ta faɗawa ummul wadda take ƙoƙarin yunƙura wa ta tashi daga kwanciyar data yi.
Sedai me? juyowar da zatai don ta dafa hajja ta miƙe idanunta ya shiga cikin nasa……….

Lumshe kyawawan idanunta tayi tare da dafe saman kirjinta wanda ya tsananta bugawa tamkar zuciyarta zata faɗo Ƙasa.
Sake wara idanun nata tayi akanshi wanda ya wani kauda kai tamkar Bai taɓa ganinta acikin duniyarshi ba.
Kafe shi tayi da lumsassun idanunta tana cigaba da kallon shi tamkar zata lashe shi duk da ɗaure fuskar dayayi tare da cin magani kamar bai taɓa dariya ba, Ita hakan ma dayayi ba ƙaramin ƙara dilmiya zuciyarta cikin tafkin kogon son shi yayi ba.
“Hajja ina kika san shi?”
Fitar amon! sautin muryarta ya bayyana cikin tambayar data ke ma hajja.
“Ke ni bani son kankanba da shegiyar tambayarki kamar ta ƴan jarida tashi tsaye naga ina ke miki ciwo”
Cewar hajja dake ɓallo goron data kunce a gefen haɓar zaninta tana faman garza.
Tura baki tayi gaba cikin shagwabar data kema hajja idan suna tare gami da cewa.
“Nifa hajja bayana da gefen ƙuguna ke faman ciwo amman ina sanya ruwan zafi zanji daɗi”
Tafaɗa still idanunta kafe akan Aliyu wanda yayi kamar bai san da halittar ta a cikin falon ba.
Haushin yadda yayi banza da ita bai nuna yasan da ita wajan ba yasa ta miƙe da ƙarfin dayayi saura agareta tayi hanyar ɗakin hajja.
Sedai ko taku biyu bata kai ba ƙugunta ya riƙe gam da wani irin sauri take ƙoƙarin juyowa sedai yadda Bayanta yay mugun kawo damƙa yasa tai wani irin juyi ta zube bisa jikin Aliyu wanda yayi suman zaune.
Gaba ɗaya baƙon yanayi ya saukar mata ajikinta da sauri take kokarin tashi ya sanya hannu ya matse ƙugun nata yadda babu wanda ze lura da hakan wata irin ƙara ta sanya wadda hajja tai saurin tasowa zuwa gareta.
“Haba Aliko kaiko kamar mai zuciyar mutanan farko zuciya a dake kamar ta rodi kaga yarinya tana ƙarar azaba amman ka saketa ai ka tausaya mata”
Hajja ta sanya hannu ta janyo ummul jikinta da sauri ummul ta mike tana ɗingisawa ta wuce ɗakin hajja hancinta shaƙe da ƙamshin mayen turaren shi.
Tsaki hajja taja mai sauti tare da kokarin bin bayanta.
Shiko ya sanya hannu ya kamo hajja ya zaunar ta gefenshi cikin tattausar murya mai ɗauke da rashin Amo! ya fara magana.
“Haba hajja miye na ɗaukar zafin dan Allah karmuyi rabuwar haka dake please matar, Ita ɗin wacece har zata shiga tsakanin soyayyata dake?”
Ya faɗa yana wani janyo numfashin sa da ƙyar.
Goge ƙwallar dake saukar mata tayi da haɓar zaninta.
“Dole naji babu daɗi idan naga ana nunawa ummi ƙyama na fuskanci tunda ka haɗa idanu da ita kake jefa mata kallon ƙyamata to bari kaji ummi baiwar Allah ce wallahi kaji labarinta sekai kuka fatana dan Allah ku rabu lafiya bana son daga jinina inga wani na nuna mata ƙyamata a sanadin halin data tsinci kanta”
Hajja tai maganar tana mai tashi ta nufi cikin ɗakinta inda ummul ta shiga.
Da kallo Aliyu yabi bayan hajja yana mamakin wannan cakuɗaɗɗiyar magana da hajja tai masa wadda ko fahimtar mai take nufi bai yi ba.

Zaune ta tarar da ummul ta cusa kanta a tsakanin cinyoyinta tana riskar kuka!
Salati hajja taja tare da zama gefenta.
“Bari salame tazo ta siyo aboniki a shafa maki wancan miskilin baze je ya siyo miki ba sannu ummi ta yaya kika buge?”
Zumɓura baki tayi gaba.
“Nifa hajja ba ciwon bane nagaya miki a ina kika san shi kika hau yimin faɗa bari nayi tafiyata tunda kema ɗin dana kejin sanyi a wajan ki zaki fara hantarata”
Tafaɗa tana kokarin tashi.
Da sauri hajja ta kamota ta zaunar a gefenta.
Tahau share hawayen daya ke fitowa ta cikin idanunta.
“Bana Son inji kina ƙara faɗin zaki tafi ki barni ina fatan wannan zuwan da kikai ya zama shine zaman ki na din din din a wajena dama kinga ni ɗaya ce semu sha zamanmu na tabbata babu wanda zesan kina gidana”
“Shikuma wancan manta shi kikai Aliko ne fa ɗan wajan Ɗiyata Hafsatu dake aure a abuja wanda yake baki alewa idan kina kuka kin tuna shi lokacin dayazo wani ƙarashen karatu nan garin a jami’ar bayero har ya zauna a nan gidan”
Hajja ta faɗa mata cikin sigar murmushi.
Ɗan jimm tayi sannan ta ware idanu kamar yadda hakan ya zama al’ada cikin rayuwarta.
“Lahhhh hajja yaya Baffa daman shine amman ya nuna kamar be sanni ba?”
Tafaɗa tana zubo da wani hawayen.
“Ai baze nuna ba kinsan har yau halin shi na nan na miskilancin koda ma can da yake baki alewar ai wai kukan kine bai so”
Hajja ta faɗi hakan tana dariya.
“Amman ya jima da barin nan tunfa ina yawo ba riga”
Tafaɗa tana kunshe dariya tuno da datai lokacin kuruciya.
“A,a yazo gaf da bikinshi shekara biyar lokacin bakya gida shiyasa baki sani ba,Mace ce ya haɗu da ita shu’uma marar kirki ta karfin tsiya ta rabashi da kowa hatta uwarsa seya jima bai leƙata ba”
Hajja ta faɗa cike da tarin damuwa acikin ranta.
Dum!dum!!dum!!! gaban ummul ya bada sautin hakan cikin rawar murya ta furta.
“Hajja yana da mata kuma harta ma haihu kilan?”
Tafaɗa tana mai kokarin danne tsinin mashin kishin daya taso mata.
“Yana da mata amman bata haihu ba se faman zaga ƙasashe suke mukuma muna nan muna fatan karma ta haihun don irin su matarshi ba’a fatan haɗa zuri’a dasu domin irine na rashin imani! duk wanda ze raba soyayyar ɗa da mahaifi ka duba tsabar rashin imaninshi”
Fakar idanun hajja tai ta goge hawayenta da sauri kuma ta mike tayi cikin bayin dake dakin danne kukan dake neman tona mata asiri tayi tare da wanko fuskarta aranta tana ayyana shikenan yayi mata nisa don ita a duniya tana tsoron kishiya musamman irin matar shi da hajja ta gama faɗin halinta.
A daddafe ta dafo bango ta fito da kallo hajja ta bita kafin ta tashi ta fita minti ɗaya ta kuma dawowa.
“Ummi zo Aliko ya kaiki wajan masu gyara a duba ki dare ake ji”
Tana gama gaya mata hakan ta koma falo wajanshi wanda yaji wannan haɗasun da hajja tai tamkar ta ɗaura mai dala da gwauron dutse ne akan sa dan dai kawai baya son tayi ɓacin rai ne dan haka seya mike tare da daukar keyn mota ya fice.
Ummul kamar wadda aka shuka haka ta tsaya tana auna maganganun hajja kafin ta gyara hijabinta ta bi bayan hajja zuwa falon.
“Ki bishi baya son jira yana waje”
Babu yadda zatai haka tabi umarnin hajja tabi bayanshi seda ta kare fuskarta da hijabi gudun kar wani a yaran gidansu yaganta yaje yakai ma babansu rahoto sannan ta nufi motar gaban motar ta bude ta shiga kusa da shi ta zauna.
Bai ko bari ta karasa rufe kofar ba yaja motar aguje yabar layin a hankali ta dai dai ta zamanta tana mai tsirama hanya idanu………..

Tafiya suke kamar ta kurame domin kaf cikinsu babu wanda yayi magana sedai kowanne acikin zuciyarsa akwai wani abun da yake saƙawa

Ajiyar zuciya Barrister Aliyu Dikko ya sauke wadda sautin fitar ta, Har cikin kunnen Ummul-khairi data sunkuyar da kanta ƙasa tana wasa da dogayen yatsun hannunta.

Kafin ya ƙara gyara dai daiton fuskarshi wadda take tamke kamar koda yaushe ba kasafai yake far’a ba.

Cikin cool voice ya furta.
“Kin matsa se lallai mun keɓe shine zakima kanki sharrin ƙugunki na ciwo tou ba ruwana asibiti zan kaiki idan yaso su fama inda bai taɓu bama sakarar banza”
Yayi maganar tamkar bashi ba gaba ɗaya hankalin shi da idanun shi suna kan kwalta ya mayar dasu akan tuƙin daya keyi.

Ɗan tura baki tayi cike da salon shagwaɓa mai jan hankali, Tare da bin Hannunshi dake riƙe da sitiyarin motar da kallo wanda ya cika da wata irin gargasa baƙa sidiƙ ga wata irin jijiya data miƙe daga saman damtsen shi ya murɗe irin na ƙarfafan maza masu jida lafiya tare da yawaita training don inganta lafiyarsu.

Murya can ƙasa kamar wadda aka ma dole ta furta.
“Nikam ba ƙarya nike ba, Allah ma ya sani ba kaine kaji min ciwo ba”
Tafaɗa tana wani tura bakinta gaba tare da juya mai ƙeya.

Wani irin fiddo idanu yayi waje kamar yaga abu na ban mamaki wanda hakan ya ƙarawa fuskarsa wani irin sahihin kyau mai tafiya da ruhin mutum.

Tsintar kanshi yayi da cewa.
“Lalala bani son sharri yaushe naji maki ciwo jimin yarinya”
Yafaɗa yana wani ɗage girar shi guda wanda hakan tun usuli al’adar rayuwarshi ce.

Hannu ta sanya tana murza idanunta kamar irin na ƙananun yara idan zasuyi rigima.
Ƙwaɓe fuska tayi tare da zuba mai dukkan idanunta tana kallonshi bako ƙiftawa cike da wata irin sahihiyar ƙaunarshi wadda Allah ya ɗauka ya dasa mata.
“Jiya fa a ɗakin ka na hotel”
Yaji saukar siririyar muryarta cikin kunnen shi.
Ɗan rintse idanunshi yayi cike daɗan zafin rai kaɗan ya juyo gareta.

“Dallah rufe min wawan bakin ki anan ke bakiji kunyar abin da kika faɗi ba yarinyar arziƙi ita zata je hotel mai kikaje yi ma acan ɗin tukunna don ba wannan ne kaɗai ganina dake ba?”
Yafaɗa batare daya kalleta ba.
“Karuwan ci mana kamar yadda ka faɗamin shine ya kaini can”
Ta basa amsa ranta na mata suyar tunowa da zafafan kalamin daya gaya mata masu kama da saukar dalma acikin ƙahon zuciyarta

Shuru yayi mata tamkar bada mutum take magana ba kuma tun daga nan bai ƙara cewa komai ba sedai yana da tarin tambayoyi akan ta wajan Hajja.

Huci mai zafi ya fesar tare da karya kwana ya ɗauki hanyar rijiyar zaki lokacin daya zo kano yayi wani course a B.u.k yasan garin sosai dan haka bai sha wahalar ƙarasawa bakin wani clinic ba wanda yake anan rijiyar zakin mai suna Norr clinic, Parking ya dai daita tare da kashe motar ya buɗe murfin motar ya fita batare daya mata magana ba.
Ganin haka yasanya ta miƙa hannu ta buɗe side ɗinta itama ta fito tana ɗan yamutsa fuskarta kaɗan.
Hannunta ɗaya yana dai dai inda ke mata zafin ta riƙe wajan tana ɗan dannawa kaɗan.
Ganin yana tafiya ciki ya sanya tabisa da sauri ta cimmasa wanda suka jera tare seka rantse Ango ne da amarya sukazo ganin likita ahaka suka ƙarasa cikin reciption ɗin saman kujera ta zauna shikuma ya ƙarasa wajan masu bada kati.
Maganganu sukai kaɗan ya kuma dawowa wajanta hannu zube cikin aljihu murya a daƙile yace.
“Muje”
Da ƙyar taji abin da yace sabida yadda yayi amfani da ƙaramin sauti wajan fitar da maganar.
Miƙewa tayi tabishi zuwa wajan masu bada kati matar ce ta dube ta tare da cewa.
“Ƙanwata yaya sunanki dana mahaifin ki”
Tana wasa da hannunta kanta a sunkuye tace.
“Ummul khairi Abubakar”
Rubutu matar tayi akan farar takadda sannan ta miƙowa Aliyu.
“Zakaje can ka biya kuɗin ganin likita sannan ka kawo mana shaidar biyan kuɗin”
Shafa kansa yayi tare da jan tsaki marar sauti cike da takaicinta yabar wajan rai ɓace ya biya kuɗin wanda shiba biyan kuɗinne ya ɓata mai rai ba wannan zaryar data sanya shi ta ɓata lokaci ita ta sanya yaji ranshi ya ɓaci.
Haka ya dawo har lokacin tana tsaye tana kuma lura da yadda yake faman cin magani.
Takardar shedar biyan kuɗin ya bawa matar ta shigar cikin system sannan ta sanya hannu kana ta miƙo masa tare da nuna mai step ɗin bene ta bashi kwatancen office ɗin likitan.

A hankali ummul taɗan matso shi hannu na ɗan karkarwa take ƙoƙarin amsar takardar hannun nashi.
“Kaje ka zauna bara naje wajan likitan naga kamar ranka a ɓace yake”
Tafaɗa cikin kalar tausayi.

Wani kallo ya watsa mata haɗi da raɓeta ya wuce abinshi.
Tabi bayanshi da kallo yadda yake tafiya cike da kuzarin shi.
Bin bayanshi tayi sannu a hankali har zuwa saman benen daya ke komai akwai a rubuce yasan ya bai wani sha wahalar gane office ɗin ba.

Jan handle ɗin ƙofar office ɗin yayi tare da turawa ya shiga sallama a ƙasan laɓɓanshi.
Matashiyar likita ce fara mai ƙaramin jiki zaune akan kujera tana rubuce-rubuce idanunta manne da farin glass ta ɗago tare da zare glass ɗin idanunta fuska cike da murmushi ta amsa mai sallamar tashi tare da nuna mai kujerar dake kallonta.
“Bisimillah zauna”!
Ba musu ya zauna yana mai aje takardar dake hannun shi.
“Sunana Dr Fauziyya yaya akai yallaɓai?”
Tafaɗi hakan wanda yayi dai dai da sanda ummul ta turo ƙofar ta shigo bakinta ɗauke da sallama wanda dr fauza ita ta amsa mata sallamar tata.
Bai amsawa dr fauziyya abin da ta tambayeshi ba sema wayar shi daya fiddo yana dannawa cike da nutsuwa.
“Tare kuke mijin kine?”
Dr take tambayar ummul data tsaya adai dai kan Aliyu tana mai sunkuyar da kanta a ƙasa.
“Eh likita mijina ne”
Ta tsinci bakinta da faɗin hakan.
Murmushi mai sauti Aliyu ya sauke haɗi da taune ƙasan lips ɗinshi aranshi yana mamakin naci da cusa kai irin na yarinyar.
“naga matsalar ki a takardar daya bani in bazaki damu ba zan ɗan maki wasu ƴan tambayoyi?”
Dr ta faɗa tare da kallon ummul ɗin.
“Ina jin ki”
Tafaɗa murya na rawa.
“Yana yawan kusantarki da ƙarfi ne lokacin mu’amalar aure hakan ma yana janyo matsalar taɓuwar ƙugu”
Da sauri ummul tai wani irin farrrr da idanunta shiko tsitt yayi yana son yaji tata kalar rashin kunyar.
“Da katakon gado na samu raunin shi lokacin ma bai gida”
Tafaɗa cikin kunya.
Murmushi Dr tayi tare da cewa matso muga wajan.
Da ɗan sanyin jiki take jan ƙafafunta idanunta a kanshi tana son taji yaɗan fita ya basu wuri amman yayi funfurus.
Ita kuma likita sanin tace mata mijinta ne yasa bata ce ya basu wuri ba

Ita ko ummul dana sanin wannan furucin tayishi yafi sau a ƙirga.
“Ɗan kunce zanin jikinki sena duba wurin”
Murya can ƙasa tace

“Ba zani bane doguwar riga ce”
“To ɗagata sama ai mijin kine ba wani abu”
Da tsananin jin kunya ummul ta ɗage rigar santala santalan dogayen fararen cinyoyinta jawur suka bayyana safar hannu dr ta sanya tare da cafkar wajan da ummul ta nuna mata da sauri ummul ta ƙwalla wata ƙara wadda tai dai dai da sanda Aliyu yayi saurin kai duban shi gareta……

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE