NOOR ALBI CHAPTER 4 BY MAMUGEE

Washe gari tunda safe da hadari Mai qarfi aka tashi da iska
Da sauri ta fito palon ta nufa windunan dake palon guda biyu ta rufe ta nufi dakin momyn da sauri ta bude ahankali sbd karta dameta da motsinta
bakinta daukesa sallama ta shiga
Momyn na kwance kan gadon ta nufa windon dakin ta rufe ahankali ta fito ta nufa dakin anty Sa’adah itama ta rufe Mata nata windon kafin ta fito tsakar gidan lokacin iskan yaqara qarfi da gudu ta qarasa dakin abbanta ta rufe Masa koina duk da idonsa biyu bata tsayaba sbd aikin gabanta ta fito da hanzari tafara kwashe shanyar wankin momyn datai jiyan duk wasu har zun fado sunyi qura tahau kwashewa zuwa lokacin tuni ruwa masu qarfi suka sauko ta shiga ciki da sauri ta aje kayan palon Kan kujera duk da tasanma saita Kuma wanke wasu
Ta fito tsakar gidan ruwan na dukanta tahau tattara kayan dake tsakar gidan takai na kaiwa cikin takai na kaiwa Palo tasake fitowa ta taje ta bude gida sbd Kar suna ciki Abdullahi yazo basuji bugun gidansaba.

Kofar kicin ta tsaya ta kakkama gefen  kayan jikinta ta Dan matsesu tarage musu ruwan dake tsayaya ta zame Dan kwalin kanta shima ta matse daga waje ta shanyasa Kan kofar kicin din sbd Kan yasha iska Dan kuwa ta barsa da dankwalin sanyin Kan Dana dankwalin suka hadu sanyi zai shigeta ya kwantar da ita
Babu ciwon Dake tsananin azabtar da ita kamar sanyi idan yashigeta
Gashi kwantawarta ciwo ba kyau
Wuya takeci Mai tsanani Dan duk rintsi saitayi aikin dake kanta ga abbanta idan ta kwanta batada Mai kulawa dashi Dan hakan nema take dannewa duk girman ciwo sai idan yafi qarfinta Dan Haka takeda kiyayewa akan lafiyarta.

Risho ta kunna ta Dora ruwan zafi ta hada qullun kunun alkamar dazatawa Abban Takoma ta zauna Kan kujera tana jiran su tafada wani irin sanyin ruwan da ake Yana ratsata tanaji.

Ba jimawa ruwan suka tafasa ta hada kunun ta zuba Masa a flask dinsa ta rufe ta juyewa Anty Sa’adah sauran a flask itama sbd tanashan kunu sosai itama musamman nata dayake da Madara take shansa sbd lafiyar fata Inji momy.

Cikin ruwan takuma fitowa takaiwa bbanta ta basa Tasha tabasa magani ta goggoge Masa jiki ta fito Yana binta da kallo yanda take jiqe sharkaf sai Kama jiki take karta jiqa Masa daki Takoma kicin tahau aikin abincin karin kumallonsu momy.

Dakin Sa’adah taje cikin rashin son takurata daga baccin datake tace”

Anty Sa’adah me za’a dafa na Karin?

Cikin bacci Sa’adah ta juya tana sake shigewa Dan madaidaicin bargonta tace”

Laylah duk abinda kikai Amma dai karki manta da kunu na.

Anty Sa’adah jiya Momy bataci abincin dareba sosai Naga abincin yayi saura ko ulcer dinta ya tashine saina dafa Mata ruwan tea da faten dankali kawai.

Kimata duk yanda kikai kaina na ciwo bacci nakeji sosai.

Juyawa tayi Takoma kicin din tahau aiki.
Wani maganin ulcer din momyn tafara dafawa Mai wuyar dahuwa Haka taita jira har yayi kafin ta dafa taliya Mara yaji ko kadan sbd momyn ta juye a kula ta zuba Mata maganin a babban kofi ta saka Mata a fridge duk da Babu wuta zaiyi sanyi sbd ruwan sanyin Dake ciki.

Tana gamawa anan kicin din taci abincin sama sama tagama tai wanke wanke ta sharesa tsaf ta fito lokacin ruwan sun Dan rage sosai sai Dan yayyafi ta nufi dakinta tacire kayan jikinta ta watsa ruwa ta sauya zuwa wata atampar tafara gyara nata dakin fes ta fito tafara aikin gyaran palon tana gamawa tashiga na mum tayi Takoma na anty Sa’adah tayo tafito tsakar gidan shima Tai Masa tas kafin ta fita tasamo garwashi maqota tazo tayi turaren wutarda momyn qaidane sai anmata shi Dan tanason qamshi.

Gurin abbanta ta nufa ta gyare Masa koina taje ta dauko Dan sauran burbushin hayaqin turaren daga palon Momy takawo Nan dakinsa shima yasamu Dan qamshin ko yayane,
sai alokacin ta zauna gabansa bayan ta aje kaskon turaren cikin kulawa a natse Tai Masa Ina kwana tana kallon idanuwansa dasuka qanqance Suka sauya launi da alama Bai samu bacci ba ta dauko ruwa tasake bashi yasa cikin kulawa a natse tabude Baki tace”

Abba?
Akwai wani matsala da kakeji ne?

Saida ya Dan hadiye yawun dayake hadiyewa da dabara daqyar shiyasa shi nasa ciwon baya zubarda yawu ta gefen Baki Allah ya taimakesa saboda saukin dayake samun Yana iya hadiye yawu.

Dan rintse idanuwansa dasukai laushi yayi ahankali alamar yanada damuwa.

Faduwa gabanta yayi da qarfi saidai fuskar Bata nuna hakan
Ta zuba Masa fararen idanuwanta batareda ta iya cewa komaiba.

Hannunsa Dake rawa da gyangyadi yadan daga yayi Mana alamar karta damu bayajin ciwon komai.

Shiru kawai tayi Dan batasan Mai zataceba bayan jurewa ta boye damuwarta sbd ko nacewa tayi tasan abinda yake damun nasa Babu abinda zata iya Masa bayan tashiga qunci da damuwa sai addu’a da take Masa.

Shiru sukai daga ita harshi Dan ko Dan zancen datake Masa wasu lokutan takasa sbd mutuwa da jikinta yayi dakuma damuwar datashiga yanzu din akan yanayin nasa tasan Dole Kam akwai abinda yake damunsa tsakanin jiya zuwa yau din.

Ganin gwara ya kwanta kozai samu baccin yazo Masa yasa ta tashi ta tura kujerarsa har bakin gadonsa da kanta ta mirginasa zuwa Kan gadon ta gyara Masa kansa akan pillow ta rufe Masa Rabin jikinsa sbd akwai sauran sanyi sosai na ruwan saman da aka gama ta bude Masa windows Dan iska da Sanyi na shigo Masa ta fice Takoma dakinta itama ta zauna jigum sbd Haka tata rayuwar take.

Sai qarfe kusan goma Sha daya saura momy da anty Sa’adah suka fito dayake komai takawo musu palon na Kari suka zauna karyawa
Ita Momy tuni tayi wanka kafin ta fito.

Motsinsu yasata aje littafin datake karatu na koyan wasu abubuwan addini da anty Sa’adah tabata ta aje gefe tareda miqewa ta fito.

Bata tsaya ba kicin ta nufa ta dauko maganin data dafawa Momy Kai tsaye ta juyo tadawo palon cikin tsananin girmamawa ta qaraso gabansu ta aje kofin maganin gefen Momy anatse da biyayyarta tace”

Barka da fitowa Momy.
Ga magani andafa na ulcer dinki naga
Kamar zafin jiya ya tada Miki ita.

Batareda ta kalli gefenba ta dago ta kalli Sa’adah dake kallon Laylan cikin tsananin qaunarta kafin ta kalli Momy tasaki murmushi tana sake maida kallonta ga Laylah cikin sakewarta tace”

Laylah kinfi kowa sanin Momy da iya kulawa da ita.

Miqewa laylan tayi tabar gurin ta nufi kofa ta fice tsakar gida tana Kama hanyar kicin Dan Dora abincin Rana Dan kuwa tasani ko shekarun duniya zatai agurin ba tankawa Momy zataiba hakama ire iren wannan son cusata agurin momyn da anty Sa’adah keyi tana iya gani akan fuskar momyn tado Mata da tsananin dacin Dake zuciyarta na shekarune kawai takeyi shiyasa anty Sa’adah na farawa take ficewa Dan dama idan ba aikin doleba Bata tsayuwar data wuce minti biyu agurinda momyn take tunda momyn ta bayyanarda rashin son hakan qarara tuntuni.

Sbd ulcern momyn yau tuwan shinkafa tayi da miyar zogala da Babu Mai sosai,
Da kanta take zuwa bakin titin anguwar karbo kayan cefane gurin malam rabiu Wanda sai anhada kudi Kamar 4 zuwa biyar sai momyn tabiyasa sbd ita kanta duk qarfin haline,
Iyayenta da Yan uwanta nada arziki Mai yawa sbd kusan gidansu duk manyan Yan shiyasa ne,
Hakama yannanta da qannenta Mata duk masu hannu da shuni suke aure saidai kaf kusan danginta Babu Mai iya Taimaka Mata sbd aurenta da Abban da Babu Wanda yaso Dan Yana talaka Mara qarfi,
Ta tsaya tsayin daka ta auresa sbd tana sonsa,
Yanada iliminsa da hankalinsa Dan Haka bataga illar aurensaba Dan bayada kudi,
Mahaifinsu baya Raye sai mahaifiyarsu wadda Sam batawa momyn auren Wanda baida aikin Yi sai takardun karatu,
Yayyunta sunso inganta rayuwarta ta hanyar Bata karatu Mai zurfi tareda auren Hadi na tsakanin masu kudi Amma ta ture komai tace bataso sai Abba Wanda hakan yakawo rarrabewar Kai aka samu hargitsinda kowa yabarta ta aura Wanda takeso Wanda ba jimawa da auren yasamu aiki yafara ta samu kwanciyar hankali da nutsuwarda take tunanin tabbatuwarta har abada,

Mahaifiyarsu ta rasu alokacinda Abba baya gari ga laulayin ciki Haka tashiga damuwa da gagari Mai tsanani Dan kuwa acikin Yan uwanta kasa sakewa tayi ga ciwo,
Qarshe dasuka Bai dawoba Haka Kuma tana buqatar taimako suka kaita asibit saidata share sati uku a kwance kafin aka sallameta ahakan Takoma gidanta taci gaba da rayuwar kadaici da tawakkali sbd zuciyarta idan tanason Abu tana Masa sone mai tsananin gaske.

Saida cikinta ya Isa haihuwa Allah yabawa Abba ikon dawowa daga doguwar tafiyar da yayi ta haifi Sa’adah wadda taci sunan mahaifiyarsu,

Darajar sunan yasa Yan uwanta ke qaunar Sa’adah har suke iya Mata komai Ahankali ahankali harta shirya da Yan uwanta suka ringa Bata kulawa da gata kamar yanda mahaifiyarsu tabar musu wasiyyar kulawa da momyn kamar tasan wani abun zai faru,

Bayan haihuwar Sa’adah Abban tafiye tafiyensa suka tsananta ahaka Sa’adah ta taso ba shaquwa sosai da mahaifinta sbd baya zama,
Duk wani dawainiyar gidan momynce keyi sbd Abban kullum ciki yawon kamfani yake Wanda yake aiki sbd aikin gwamnatin Bai samuba har lokacin.

Momy nasonsa Bata taba Jin damuwa takaici ko gazawa da zamanta ahakan ba saima tausayi da qaunarsa datake qarawa ahakan.

Babban budin daya fara shigowa rayuwarsu shine dawowar babban Amininsa MUHAMMAD ABU TURAB TURAKI Wanda duniya tafi sani da AB TURAKI
Turaki shine ya bawa abba manyan kudin daya bude kamfanin kansa da kansa bayan ya siya Masa babban gida da babbar mota,

Da farko rayuwarsu Momy da yarta da abban Takoma ta kwanciyar hankali da Jin Dadi saigashi kwatsam Abban yaga ZAINAB yaji Yana qaunarta,qauna Mai tsanani batareda jawakai lokaciba ya aureta ya ajeta anata gidan daban tsawon shekara da shekaru har Allah yabata ciki momyn Bata saniba saidai yanada niyar bayan haihuwar ZAINAB din zai hadesu yafadawa momyn gaskia wadda halaccinta da kunyartane tun farko yasakashi boye Mata
Ashe qaddara bazata bar hakan ba Dan kuwa mummunan hadarin motar yafarune ranar da Turaki ya sauka Nigeria akan wata babbar nasarar rayuwa daya qara samu a qasar US
abban ya dauki zainab suka Isa gidan Dan tayasa murna da yiwa hajiyarsa wato Anne Allah ya Sanya alkhairi saigashi suna shiga gidan tsautsayi ya Tarawa zainab din ta zame tayi mummanar faduwa nakudar Dole ta taso mata,
Hankali tashe suka juya zuwa asibiti ganin halinda Abban yake ciki na rudu da rashin hankali yasa Turaki bin bayansu da mota wadda shine da kansa yake tuqawa gashi dare ne Dan Saida sukai ishai sukazo gidan.

Motar abbance tafara shigewa qarqashin babbar motar data Rasa burki tayo cikinsu kafin motar Turaki wanda Bai ankareba Saida yakawo gaf dasu shima tasa motar tayi cikinsu anan wannan mummunan hadarin ya afku Wanda yayi sanadiyar rayuwar zainab duk da ansamu ta haife cikin,
Shikuma Abban ya Rasa nasa qafafun da wasu raunika
Turaki kuwa Babu wani babban raunika ajikinsa saidai buguwa da yayi sosai wadda tayi sanadin tasa qaddarar ta rashin haihuwa da ake fada duk da Babu tabbacin rashin haihuwarne kokuma asalin inda ake samun haihuwarne yasamu matsala Dan kuwa tunda yabar qasar baikuma dawowa ba Saida lokaci Mai tsayi yaja
Zuwansa Nigeria saiya koma sai dace ne kawai duk da Suna da tarin dukiya da matsayinsa Babu inda Bai zagaba a jaridu da gidajen talabijin da media Amma Kam ganinsa sai dace Dan kuwa babban mutum ne da ko acikin masu kudin ba kowa ke samun damar ganinsa ko ganawa dashiba,saidai Amininsa Abba da koyaushe yakan ziyarcesa ya duba lafiyarsa duk yazo Nigeria saidai wannan karon ya Debi shekaru masu Dan dama Bai dawoba.

Bayan abunda ya faru dukkanin arzikin Abba Saida yashige gurin neman lafiyarsa Wanda daga qarshe wannan gidan dasuke ciki shine kawai ya rage musu Wanda aka siya da sauran kudaden kamfaninsa da kadarorinsa da aka siyar,

Dangin momy sunyi fushi da Allah wadai da ita akan zaman datakeyi da Abban har bayan irin abinda yamata gashi yanzu Takoma jinya da dawainiya dashi,
Ta ciyar da kanta,ta ciyar da yarta,ta ciyar dashi da tasa ‘yar hakama itace dawainiyar komai da sutura duk da dai Bata yiwa yarsa sai abinda Sa’adah ta kashe ta bata Haka shima kayansa duk rufin asiri ne Dan Haka kowa danginta ya saka Mata ido suna muamala da ita Amma basa iya taimaka Mata,itama dama ayanda cin amanarsa ta kangarar Mata da zuciya sai Bata buqatar taimako ko tausayi daga kowa,
Zata Gina rayuwar yarta suyi rayuwa Mai kyau da Jin Dadi wannan shine babban burinta sbd a duniya tariga tasan bayan ‘yarta data Haifa da cikinta babu wata qauna ta gaskia da Amana.

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE