ABDURRAHIM MATUKIN JIRGIN RUWA NE CHAPTER 3 BY FADDY BABY

ABDURRAHIM MATUKIN JIRGIN RUWA NE CHAPTER 3 BY FADDY BABY

 

 

Dabud’ar su, suka cigo gidan. Mama cikin fad’uwar gaba tafito daga d’aki.tom mariya yau dai Allah yayi Na’ima ta zama amaryar gali, afito mana da amarya sauri muke kin san hanyar tamu, ”

Mama kallan “yan d’aukar amaryar tayi, sannan ta kalli binta tace”binta d’an shigo daga ciki muyi magana.”

Bayan binta ta shiga d’akin mama ne, mama ta kalle tace” binta banfa san inda Na’ima take ba, wani uban ashar binta tayi, tace wallahi mariya tun daga ni sai ke ki fito da Na’ima kafin su yaya ya’u suji maganar nan, ”

Wani ban zan kallo, mariya tayi ma binta, tace kowa zaki fad’amawa kije
kifad’a mai binta. Tana kai wa nan tajuya tayi tafiyar ta. ”

Binta waya ta d’auka ta kira jimmai uwar ango ta gad’a mata abinda mariya tace, ”
Daya ke banisa tsaka nin dutun malam da sabon yalwa hakan yasa, cikin k’ank’anin lokaci, jimmai ta iso.”

Tun kafin takarasa shigowa gidan, take fad’in” ke mariya! duk inda kika kai Na’ima kiyi gaggawar d’akko ta, kafin in shigo, dan wallahi, in har na shigo ban ga Na’ima ba sai kin sani, dan yahaya ma bako mai bane bare ke! karan ka’da miya,”

Allah sarki mariya da yake bata saba rigima ba, jikin ta kota ina rawa yake, ”

Jimmai ko na zuwa ta shak’i wuyan mariya, tace”mariya wallahi ko zaki mutu ba zan sakeki ba , sai kin fad’a min ina kika kai Na’ima?

Wujijjiga mariya jimmai take da duk k’arfin ta, masu hankali ne daga cikin wa inda suka zo d’aukar amaryar, sukaga in sukabar jimmai zata yima mariya illa, in abun yazo da k’arar kwana ma ta kashe ta. ”

Dak’ar aka b’anb’are jimmai daga jikin mariya, dan bada wasa ta shake taba. ”
Dan Allah kubar ni da ita.”a’a yaya jimmai ki b’arta, mu bata nan da kwana biyu, cewar” Binta. ”

mariya kwana biyu na baki, wallahi duk inda kika kai Na’ima ki kawota kafin nan da kwana biyu, in kuma bahaka Hmmmm.”

“Yan d’akko amarya ko haka aka hak’ura aka koma ba amarya. ”

Mariya ranar kusan kwana tayi kuka yaran ta na taya ta,”

Aiko washe gari, dawuri ta shirya, ta nufi kaduna. bata tsaya ko ina ba , sai gi dan gwaggo, lokacin ita kuma gwaggo tayi shirin zuwa gidan da take aiki,”

Kai mariya kece da wuri haka? Cewar gwaggo, tom daga dai ga nin zuwan nan nasan banawa bane, dan haka zo muje in kaiki gidan da Na’imar ke aiki. ”

Aiki kuma gwaggo, nan dai kwaggo ta fahimtar da mahaifiyar Na’imar da lilin aikin nata dan ta tai makamasu ne,”

mahaifiyar Na’ima bata wani damuwa ba saboda tasan gwaggo bazata kai Na’ima inda zata cutu b.”

Koda suka isa gidan da Na’ima ke aiki, mai gadin gidan sukai ma magana yakakira masu Na’ima.”

Naima ko kullum da muwarta k’ara k’aruwa take, gafargabar auran ta, tana cikin wannan tunanin ne, mai gadin gidan yazo yace meta, tazo tayi bak’i”

Cikin fargabar kosu waye ke nai manta tafita. ”

Koda ta hangi mamar ta cikin fad’uwar gaba da wata jarimta da tazo mata ta idasa inda duke tsaye,”

Oyoyo mamana sannun ku da zuwa. ”
Nan dai suka gama gaggai sawa. ” mama ta kalki Na’ima tace”Na’ima sauri nake je ki d’auko kayan ki mutafi, mama lafiya ko cikin kwanciyar hankali Na’ima ke ma mamar tata magana dan bata so ta gane hakin da take ciki. ”

Yi abinda nace, sauri nake na baro k’annanki gida, tom mama amma hajiyar bata nan tafita sai dai in tadawo, kinga ni kadai ce a gidan.”

Na’ima bazan iya jiran kiba, amma daga hajiya tadawo ki dawo gida yau yau d’in nan, dan jiya Iyayanki suka d’aura maki aure. ”

Na’ima bak’aramin jarimta tayi ba dan tanuma mamar ta bata damuba, amma a ai nihin gaskiya ita kadai tasan halin da takeciki.”

Mama tom ya maganar da baba yayi, kajin yabar nun fashi? ”

Na’ima kiyi abunda nace kinji, iyayanki jiya bakalar abinda basuyi min ba, shike nan mama zan dawo yau din sai tadawo, amma mama kina son auran ne yanzu?”

Tom Na’ima ya zan yi amma maganar so ko ai banfa so,”

Shikenan mama sai nazo. ”

Na’ima koda tadawo gida , bak’in ciki yawa yayi mata, ga haushin abinda akai ma mamar ta, ga ta kai cin auran da aka ce an d’aura mata. Palon ta zau na tana ta kuka, har hajiya Rahina ta shi go amma bataji shigowar taba. ”

Kusa da ita hajiya taje ta zauna amma abin mamaki har yanzu Na’ima bata son da wata hajiya a polon ba, kukan ta kawai takeyi a bunta. ”

Ke! lafiyar ki? Cewar hajiya Rahina.”

Na lura da ke , tun da kika zo gidan nan, baki da wani aiki sai tunani, tom idan bazaki iya aikin ba zan samu wata, inda abun naki k’arak’aruwa yake, yanzu abun ya zama sai kizo ki zauna ki tamin kuka, ina Tambayar ki kuma kin min shiru kin zuba min ido, tom wallahi bazan d’auka ba. ”

Na’ima shiru tayi tana sauran hajiya, sannan tace”kiyi hak’uri. ”

Zama hajiya tayi tana fuskantar Na’ima , sannan tace”mai yasaki kuka yanzu nake son in sani? ”

Dama mama nace tazo yanzu tace wai duk abinda na keyi in dawo gida yau, tom ni kuma bana son komawa gidan, meyasa? Cewar hajiya, saboda “yan’uwan babana sun min aure ni kuma bana son auran da su kai min,”

Kallan ta hajiya Rahinata tayi sosai sannan tace”meyasa bakya so? ”

Saboda babana, yana gaf da mutuwa yace” ko bayan ran shi be yarda ba in auri yaya gali. Na’ima tashi tayi daga inda take ta muskan to hajiya Rahila tace”.

Hajiya dan girman soyayyar da kikema suga ban halita, dan Allah kitai makan, ki kaini, kasar nan, danji kina cewa za akawo miki kaya, kuma zasu dad’e basu dawo ba dan Allah, Hakane kawai zai sa in cikama maganar mahaifina. ”

Zan tai makeki amma sai naji cikakkyan tarihinki, naji dalilin dayasa mahaifin ki beso ki auri d’and’an uwan sa. ”

shiru Na’ima tayi kamar mai tunani, sannan tafara magana kamar haka. ”

Kakana Abdullahi yanada mata biyu, jamila da kuma Habi, Habi ita ce matar kakana ta fari dan haka ita ta haifama kakana manyam”yaya gwaggo jimmai itace babbar yarin yar kakana sai baba ya’u sai kabiru sai autar su binta. An haifi gwaggo binta bad’ewa kakana ya auro mahaifiyar babana wato kakata, kakata tun da ta haifi babana bata sake haihuwa ba, kuma ta haifi babana badadewa Allah yayi ma kakana Abdullahi rasuwa, babana yataso cikin maraicin uba dan duk wani abu da yayye sukema k’annan su tom su baba ya’u basama babana, amma fa in dai akazo maganar aiki tom akokacin zasu ce ai shine garami, da kakata ta lura wahala zata kassara d’anta d’aya tilo sai ta kai shi sabon yalwa almajiranci, bakalar fad’an da su baba rabi’u basu yiba amma kakata ta share, bayan tafiyar babana almajiranci badad’ewa kakata ta kwanta k’aramar jinya, wadda tazama sana diyar ajalin ta, babana yayi nisa da karatu alhamdulillah, saidai kash suna cikin karatu Allah yayi ma malamin nasu mutuwa sakamakon k’aramar jin yar dayayi, tom daga nan ne fa ya koma aikin gona ana biyan shi, ahaka ahaka Allah yabuda mai har ya tsaya da k’afarsa, cikin k’ank’anin lokaci yasai fili yafara gini, yana cikin gini Allah yahad’a shi da mama ta kasan cewar itama “yar uwar babana ce ma’, ana marainiya ce, babana bai wani sha wuya ba aka bashi auran ta. Tun da su baba ya’u sukazo bikin sukaga abinda babana yayi na kud’i tom daga nan fa duk wani Wanda da muwar kudi ta tashi mai sai ya d’aurata akan babana, in ta kai cemiki har sai dai sukaga sun karya shi sannan Suka b’arsh. ”

Masha Allah, Allah ya azurta mahaifina daa haihu dan mu biyar ya Haifa, ni sai k’anwata Aisha, sai Aiminu da umar sai auta auwal. ”

Tunda gali d’an gidan gwaggo jimmai ya fara nuna yana sona baba yahanani zuwa hidimar wajan su, dalili ko duk yarinyar da gali ya d’auka ido akanta sai ya lala tata. ”

Yaje gidan yari (prison) yafi ak’irga amma abin sai abinda yayi gaba, dan yanzu ma har sata yake. ”

Wannan shine dalilin da nida babana bama son aure na da yaya gali. ”

Nan Na’ima taitaba hajiya labarinta har izuwa auran ta da aka d’aura da gali kamar yadda mamar ta, ta shai da mata.”

Na’ima naji labarin ki kuma koni ban goyi bayan ki zaman aure da mutum kamar gali ba, dan haka zan kira gwaggon ki in shai da mata in har ta abinta tom, ba shakka dake za a, sai dai fa zaman jirgin ruwa akwai sanyi fa. ”

Waya hajiya Rahila ta d’auka ta kira k’awar ta hajiya suwaiba akan dan Allah ta turo mata da gwaggo mai ai kinta. ”

Driver hajiya suwaiba tasa ya kawo gwaggo har gidan hajiya Rahila. ”

Bayan sun gaisa ne. Hajiya Rahila tace” gwaggo nasan zakiyi mama kin kiran ki da nayi, tom Na’ima ce tarok’eni wata alfarma akan tana so….. ”

Hajiya fadama gwaggo tayi duk yadda su kai da Na’ima. Ta d’aura da cewa”

Gwaggo kin san HALIBIZ SHOPPING MELL tawace tom dama in dai shekara tazo tsakiya muna ai kawa akawomana kaya, kin san tafiyar ta jirgin ruwa ne, tom suna yin wata shida ahanya,. ”

Yanzu ya kika ce kin aminta atafi da ita koka, amma fa ni badani za ai tafiyar ba.

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE