ABDURRAHIM MATUKIN JIRGIN RUWA NE CHAPTER 4 BY FADDY BABY
ABDURRAHIM MATUKIN JIRGIN RUWA NE CHAPTER 4 BY FADDY BABY
Hajiya Rahila kallan gwaggo tayi, tace” gwaggo baki ce komai ba, kin yarda in tura Na’ima, u, s, d’akko kayan sabuwar shekara da zamusa a plaza? ”
“Tom Hajiya ba wai nayi shiru bane, a’a wallahi, kin san Na’ima, ba yarinyata bace, shine nake gani kibani nan da zuwa gobe, inje in tambayi mahaifiyar ta in tabari tom.”
Kafin Hajiya Rahila tai wata magana, Na’ima tayi wuf tace.
“Ahalin yanzu mamana tana wani condition na rayuwa, yayyan babana sun tasata gaba, akan auran nan, tun da gwaggo kikaga mama tace sai dai in dawo gida akai ni d’akin yaya gali, tom wallahi bak’aramin furgita tayi ba, da lamarin su”.
“Hajiya kiwa girman Allah, ki amshi tayin tafiyar nan tawa ko dan in cika burin mahaifina, na rashin auran nan da har’ya komama ga Allah baya son shi. ”
“Tom gwaggo kinji abinda Na’ima tace?”,
“Nibawai nak’i tafiyar Na’ima bane, a’a wallahi kawai dai, kin san yanzu muna wata irin rayuwa ne, sai kayi Abu da niyar tai mako, nan gaba yazamarma matsala”,
“Gaskiya ni bazan d’auki Na’ima ba bada amincewar kowa ba, in kaita wannan kasa mai nisa, kuma tafiya ce bata yau ko gobaba”.
“Badamuwa Hajiya amanar Na’ima ahannu na take dama, dan haka na amince, Allah yasa haka yazamo mafita garemu baki d’aya”, cewar gwaggo.
“Ameen ya Allah”.
“Kije gida ki shirya dan goba ne tafiyar”, cewar hajiya Rahila.
Duk wani shiri da Na’ima za tayi, tayi shi, gobe kawai take fatar gani.
Na’ima zau ne a gaban Hajiya Rahila, tagama duk wani shiri da za tayi.
“Tom Na’ima Allah yakiyaye hanya, Allah ya sauke ku lafaya, yanzu ga driver nan zai kaiki airport , kaya ko mai da komai anriga angama saya, daga kun je sai tafowa, Amma fa zakisha sanyi yarinya, zakiyi kalar tafiyar da nake sha’awa Amma ni tsoro yahanani yi danni tsoran jirgin ruwa nake Allah”.
“shekara daya da wata hud’u zamuyi ko hajiya?”.
Dariya sosai hajiya Rahila tayi, sannan tace “yanzu ai a jirgin sama (airplane) zaku, wajan dawowa ne dai zaku dawo a jirgin ruwa saboda kaya”.
“Ikon Allah sai kallo wai yau nice a u, s. Inji Na’ima kenan”.
Kwance take akan tafkekean gadon hotel d’in da jamilu, abokin tafiyar ta ya kamamusu.
Juyi kawai take sanyin k’asar da tunanin halin da maman ta take, yahana ta bacci.
Washegari koda Na’ima ta tashi kasa wanka tayi tsabar sanyin da take ji, jamilu da kan shi ya kawo mata tea da wani farfesun nama.
“Tashi kik’arya (breakfast) dan yanzu zaku Kama hanya, Amma fa zakiyi doguwar tafiya”.
“Dan allah in tambaye ki mana?”.
Ya kuma fada yana dubanta
“Ina jinka”, cewar Na’ima.
“Dan Allah me yajawo miki wan nan wahalar haka?”.
Dubanshi tayi da mamaki akan fuskanta ta ce
“Wahala kuma tame fa?”.
“Ta tafiya a jirgin ruwa mana, waya fad’a maki su kaya dole sai an tsare su, ai daga anba direbobin shike nan, ba sai an had’a da mai tsaron kaya ba”, Jamilu ya fad’a.
“Tom nima sha’awar tafiyar ce kawai”, ta fad’a mai haka ne kawai dan ta wuce maganar.
Na’ima da jamilu tsaye suna sallama dan yanzu su Na’ima jirgin su zai kama hanya.
Hannu jamil ya mikama Na’ima.
Juya kai tayi kamar bada ita yake ba. Tace ‘kaji min mutum, ko yau she na san shi’, tayi maganar a zuciyarta.
“Tom shikenan Na’imatu Allah ya isomana dake lafiya, Allah ya karemin ke gaba da bayanki”.
Da Ameen ta amsa duk da addu’ar tasa ranada alamar tambaya injita.
Jamil bashi yabar gurin ba har sai da yaga jirgin su ya tashi sannan.
Can b’angaran mama kuwa bayan ta koma gida, tun tanasaran zuwan Na’ima har ta gaji, tace”wata k’ila sai gobe, tom Allah yasa dai goban ma tazo da wuri, kafin guyababbun iya yanta sudawo cewar mama”.
Washe garima haka ya faru, ba Na’ima badalilinta, mama ganin rana tayi Na’ima bata dawo ba, abin tsoro yaso bata, dan tasan tunda tacema Na’ima tadawo tom ba’abinda zai hanata da wowa, tom kodai an sace tane, haka mama taita tik’a da kwancewa, tana ahaka ne tajiyo sallamar su, ya’u cikin kid’ima mama ta fito data b’arma a hannunta, tana k’ok’arin shimfid’a masu, ya’u ne yad’aga mata hannu yace.
“Dakata mariya bazama ya kawo muba, munzo ne kibamu ‘yarmu kuma matar d’an mu, ko kuma wallahi mariya hukuma zata rabamu da ke”.
“Wallahi! wallhi! Wallhi! saunawa narantse ya’u?” Cewar jimmai.
“Sau uku, yaya jimmai”.
“Wannan shine gargad’i nak’arshe, mariya, ki fitomin da surukata, in kuma bahakaba tom zaki san ruwa ba sa’an kwando bane”.
Tana kai wa nan tai gaba.
Ya’u kusa da ita yadawo yace “mariya ni zan tai makeki amma sai da sharad’in in kin aminta zaki auran?”.
Wani mugun kallo mama tayi masa, tace “ba aure atsakanina da kai, amma ba abin mamaki bane dan ka fad’i haka, inda nasan akwai k’arancin rashin sani atare da kai”.
“Kamarya mariya banganeba? ”
“Nufina bakan haramun ba bakadan halaliiba”.
“Haba mariya mai Ya kawo maganar haramun kuma da halali ai…. “.
Maganar jimmai dayaji ce tasa ya canza abinda yayi niyar fad’a tahan yar cewa “kinji dai abinda nace maki kinada damar samun mafita, in kinyarda in kuma kink’i kik’are a wahala”.
Yana kaiwa nan yayi gaba abinsa.
washe gari da sassafe mama ta nufi kaduna, sakamakon wani munmunan mafarki da tayi akan Na’ima.
Gidan gwaggo mama ta sauka.
Cikin gwaggo sai da ya kad’a dan ganin mama da tayi, dan bata san abinda zata ce mata ba, game da tafiyar da Na’ima tayi bada izinin taba, haka ma fa nad’aukar mata yarinya na kai gidan aiki bada sanin taba, ai ko yanzu da kunya in ce mata bata k’asar, tom inama zance mata taje.
Muryar mama ce da gwaggo taji, tadawo da ita daga tunanin da ta Lula.
“Gwaggo kiyi hak’uri kin mun abun kirki amma nada meki da sin tiri, wallahi bubawa ne sun kacame min, gashi itama Na’imar da nace tayi hak’uri tazo a kaita d’akin mijin ta shine tak’i zuwa, ni hartasani ma afargaba, na fara tunanin ko lafiya?”.
“Lafiya”, cewar gwaggo dabatasan ma abinda ta fa’daba.
“Alhamdullh”, cewar mama.
“Dama wani mafarki ne nayi akan Na’imar mai ban tsoro, shine nazo ingani lafiya daga nan kuma k’afarta-k’afata”.
Wani irin kuka cikin gwaggo yayi, cikin rashin dabarar abinda zata ce mata, tace “tom tashi muje gidan da take aikin”.
B’angaran Na’ima kuwa, al ajabi ne ya inshe wai yau ita ce acikin jirgin ruwa.
Wani irin k’ara sukeji daga k’asan jirgin kamar ana balla Abu, cikin kid’ima suwagabannin jirgin suka fara sanarwa jirgi yasamu matsala, kafin kace wani abu, jirgi yafara mangar-mangar.
Na’ima kuka tafarayi ganin ruwa yafara tud’ad’owa acikin jirgin.
Ahankali ahankali jirgin yafara k’asa ruwa ko kamar ana k’ara antayo shi..