AL,ADUN WASU CHAPTER 1

AL,ADUN WASU CHAPTER 1

Mal Bashir dattijo mai kimamin shekaru hamsin da takwas na shigowa cikin layinsu yara suka fara binsa suna oyoyo Baban yara. Da yake kullum haka suke masa shiyasa baya rabo da yar tsarabar da zai kawo musu. Hannunsa daya yasa a aljihu wanda daga tsintsiyar hannun a yanke yake ba yatsu sakamakon zarton da ya fada kai har ya tsinka masa jijiyoyin hannu. ya sha wahala sosai likitoci suka ce hannun ya mutu dole a yanke shi. Duk da haka bai dena zuwa wurin sanaarsa ba ta kafinta. Da dungulmin hannun ya bude aljihunsa ya saka mai lafiyan ya zaro carbin malam ya mikawa yaran. Suna ta murna suka tafi su raba. Yayi gaba yana dan murmushin suka hada ido da wani matashi a layin. Da sauri ya taba na kusa dashi kai don ubanka kashe ga Baban yara nan. Tare suka tashi suna karkade jikinsu. Baban yara barka da yamma suka fada da ya karaso kusa dasu. Ya dan bata rai bazan amsa ba Sani. Yanzu don Allah baza kuyiwa kanku fada ba da shaye shayen nan? Ya kalli katon ciki Anas so kake ciwon babanka ya sake tashi saboda kai ko? Wanda aka kira Anas ya girgiza kai. Kayi hakuri in Allah Ya yarda bazamu sake ba. Yayi murmushin takaici Allah Ya bada ikon denawa. Kuna ta batawa kanku rayuwa a banza. Idan baku sani ba abinda mutum yayi da kuruciya yakan bishi har girma. Na tabbatar babu wanda zai so nan gaba a bawa dansa labarin ya taba busa wiwi a tarihin rayuwarsa. Sani ya dan yi murmushin jin abinda ya fada. Baban Yara ya ce au dariya na baka ko? Ya kama bakin ya murde. Muna nan da ku idan baku dena ba wata rana kwata zaku shiga ku kwanta kuce gado ne. Yayi gaba abinsa yana ta mitar halin da yara ke saka kansu a yanzu.+ A kantin kofar gidansa ya tsaya suka gaisa Munkaila mai shago. Mal Bashir ya dauko naira dari ya mika masa. Gashi nagode sosai. Munkaila ya karba na meye kuma wannan Baban Yara? Darin da ka bawa Zuhra mana da safe. Ina shirin fita ta tambayeni kudi zata je karbo sakamakon jarabawarta. Lokacin bani da chanji shiyasa nace ta karba a wurinka. Munkaila ya mika masa kudin, ai yau ko sau daya banga fitowarta ba. Mal Bashir ya karba ya shiga gidansa da sallama. Zuhra na yanka yakuwa taji muryar Babanta a soro. Hantar cikinta ce ta kada sosai ta tashi da gudu ta shiga bandaki. Garin sauri ta zubar da yakuwar da take yankawa. Ummanta ta soma fada ke lafiyarki kuwa. Mal Bashir ya karasa shigowa tsakar gidan. Ina ta sallama babu mai amsawa kamar babu kowa a gidan. Atine Umman Zuhra ta ce yi hakuri Baban Zuhra. Wallahi bari tayi min nake fada banji sallamar ba. Takalmansa ya cire ya zauna kan tabarmar dake shimfide a tsakar gidan. Fitsari ta bari ya matseta shine take wannan gudun ko. Umma tace anya kuwa? Hira mukeyi fa kana yin sallama ta tashi kamar wadda ta ga abin tsoro. Baban yara na jin haka yasha jinin jikinsa. Yace da Umma ta karbo sakamakon jarabawarta kuwa?Umma tana kwashe yakuwarta ta ce bana jin amma ga wasu takardu can akan taga wanda Hajara ta kawo mata dazu. Mal Bashir ya tashi ya dauko a sanyaye…ai tunda ta gudu yasan bana ma bata kitsa abin arziki a makaranta ba. Ai kuwa yana budewa yaga abin haushin da yasa rai da gani. Ta 48 tayi cikin su 52. Ransa ne ya sosu. Ya rasa yadda zaiyi da yarinyar nan. A fusace ya tashi ya tafi kofar bandakin. Zuhra me kike yi ne ya tambaya da daga murya. Daga ciki ta ce ehem ehem! Ya sake bugawa idan ba so kike na bude ki ba gara ki fito tun wuri. Zuhra ta gwammace ta yini a bandaki da ta fito ta sha fadan Baba. Ta sake cewa ehem….. ya ce bari na fita tunda mun koma wasan buya da ke. Sai da ta kara kusan minti biyar sannan ta fito duk ta hada gumi. Ta dubi Ummanta, wai yau da Baba ya kamani bansan….saukar rankwashi taji a tsakar kanta ta durkushe a kasa tare da rike kan ta soma kuka. Baban Yara yace idan baki rufe min baki ba sai na kara miki. Da kuka Zuhra ta mike tsaye tana turo baki ko saboda rankwashin nan ba dole na kasa kokari ba. Idan kana taba min mandula oblongata dina haukacewa zanyi nan gaba kadan. Baban Yara yace kece mandular ai. Nan kika fi kauri dama. Kin iya haddace ‘yan kalmonin turanci kizo kina barazana dasu kamar wata wadda tasan abinda take yi. Zuhra dai kuka ta cigaba da yi har sai da Umma tayi mata tsawa. Wallahi idan kika tara min makota yau jikinki sai yayi tsami. Jin haka ta soma tsalle tana kara kukan. Baban Yara yace bari na dauko wayar chaja na yi miki mai dalili. Ai kamar anyi ruwa an dauke haka ta hadiye kukan.+ Takardun jarabawarta da aka hada da report card din ya soma dubawa. Wasu har zero ta ci. Maths(lissafi) tace arbain da takwas, Arabic tace casa’in da hudu sai Hausa ta taci sabain da daya. Dama sune darrusan da suke dan taimakawa bata daukar ta karshe gaba daya. Sai ko rubutu da ta iya mai kyau idan ka gani zaka dauka na wata mai kokarin ne. Yana dubawa yana tsaki sai daga baya ya kula da yadda take rubuta suna. Kansa ya rinka girgizawa kawai don takaici. Ko shi da iyakarsa aji hudu a secondary ga shekaru sun mika amma yasan idan suka shiga aji shi da yar tasa sai yafi ta kokari. Zo nan ya yi mata tsawa. A hankali ta ja kafa ta je ta tsugunna a can gefe. Yanzu kin tabbatar duka takardun nan naki ne? Nawa ne Baba duba sunan da rubutun mana. Yace ai na duba. Wasu ki rubuta Zuhra Bashir wasu kuma Fatima Bashir don tsabar rainawa malamai hankali. Yana cigaba da dubawa yayi karo da wata. Takalminsa ya raruma ya kwada mata. Ya daga takardar yana nunawa Umma. Kinga wulakancin yar nan wai Fatima Basiru. Ya nuna kansa nine BASIRUN??? yadda yayi yasa ta soma dariya Umma tace Allah Zuhra zanci mutumcinki. Ana miki fada kina wa mutane dariya don shakiyanci. Zuhra ta kara matsawa gefe tana sharar hawaye to ba haka naji su Kawu Sabiu da Innar Ajingi suna kiranka ba. Baba ya cije lebe saboda takaici. Da kika ji sun fada ba sunan gida bane?. A nan wa kika taba ji ya kirani Basiru? Tace to yi hakuri wallahi daga yau na dena. Ki ma kara ya fada yana tattare takardun. Yana yi yana mita. Yarinya sau nawa ana miki repeating gashi kin kusa shekara ashirin. Amma kanki kamar kifi, nasan duk ajin kece mamansu ko. A’a Baba ga Hajara, ka manta ajinmu daya. Yace ina fa zan manta…an tara dakikai biyu a aji daya. Baku da aiki sai cin awara da wainar flawa. Zuhra da baki baya shiru tace to ba kai kake bani kudin ba. Umma tace kaga ka dena kula yarinyar nan sai jininka ya hau.3 Takardun ya miko mata jeki ki ajiye min a dakina. Ni ina ta kokarin hada kudi na biya miki kudin WAEC saboda kada a rufe amma naga kamar asara zanyi. Sau biyu kina qualifying din nan amma kin kasa hada credit uku. Zuhra tasan yadda babanta ya damu tayi karatu amma duk yadda ta dage a cewarta ko kadan bata ganewa. Zama tayi kusa dashi kaga Baba kawai ka kaini makarantar koyon sakar nan. Har na tambayo matar tace a wata biyu zata koya min sau uku a sati zani. Kuma a dubu shida. Ai kaga yafi sauki akan WAEC din. Ta nuna kanta ni da ka ganni bani da abinci a boko. Kan baya dauka yadda kasan an zuba dusa a kwakwalwar haka nake. Shi din ma ya kusa dariya sai ya dan dake. Tashi ki bani wuri ni. Ko damuwa ba kya yi yan ajinku zasu tafi makarantun gaba ke kina son koyon saka. Ta dan tura baki to ya zanyi Baba. Suma fa duk harkar ta koma satar amsa. Idan sakar ma bazata yiwu ba kawai kayi min aure ka huta. Shi da Umma a tare suka yo kanta suna mata fada. Da gudu ta tashi tayi hanyar waje tana dariya tare da jan mayafin Umma a igiya. Mal Bashir Ibrahim mutumin Ajingi ne ta jihar Kano. Su biyar ne maza a gidansu shine na biyu. Mahaifinsu manomi ne kuma yana kiwon shanu da tumaki. Da farko sun fara karatu har ya kai aji hudu a makarantar gaba da firamare sai babansu ya matsa akan basa samun lokacin taimaka masa a gona. Shi a son ransa duk su hakura da karatun. Ko kadan Bashir baiji dadin hakan ba, sai da ya hakura shi da wansa da mai bi masa suka koma gona. Sauran biyun suka cigaba. Akayi rashin saa autanma ya dena zuwa don shi yafi son kiwo. Wanda ya karasa kuma kan nasa kamar na Zuhra. Ba wani sakamakon kirki ya samu ba. A halin yanzu ma masinja ne a wani company. Mal Bashir ya dawo birni shima aikin kafinta a nan ya hadu da Atine yar kwanar Diso ya aura.sun jima basu sami haihuwa ba gashi yana da son ‘ya’ya ,sai daga baya aka haifi Fatima wadda taci sunan mahaifiyar Mal Bashir kuma sunan Atine shiyasa suke kiranta Zuhra.+ Zuhra na fita gidansu Hajara ta nufa tana ta mita ta jawo mata fada a gida. Da sallama ta shiga sai dai babu kowa a tsakar gidan. Daga dakinsu Hajara ta ji an amsa ta shiga. Kwalliya Hajara take yi anyi wankan yamma tana shirin fita unguwa, mudubi ne a hannunta tana zana gira. Zuhra ta sakar mata dundu a baya…shegiya kin hada min zafi a gida kin zauna kwalliya. Hajara na sosa bayanta suka ji muryar mamanta. Ta shigo dakin haba Zuhra sau nawa za’a hanaki zagi ne? Zuhra ta sunkuyar da kai tana hararar Hajara. Mama tace idan na sake ji Allah da yayanku Lawal zan hadaki. An kwana biyu ba kiji bulala ba shiyasa kika dawo da yi mana zagi. Zuhra tace don Allah kiyi hakuri na dena daga yau In sha Allah. Mama tace da kin kyautawa kanki sannan ta fita. Hajara ta cigaba da kwalliya suna hira tace ke ni fa Sahabi ya dage sai nayi karatu. Yace zai rinka yi min lesson kafin a fara WAEC don har ya biya min kudin a wata makarantar. Zuhra tayi dariya zaiyi asarar kudi da lokaci kenan. Baki fada masa kina sahunmu bane? Bana son wulakanci wallahi tunda na fahimci yana son nayi karatu na soma dagewa. Wannan karon mutum shida na doke harda ke. Zuhra ta daga hannu alamar jinjina kaga su Fropesa Hajara kenan. Hala irin su Ligan dinnan zai nema miki. Kanwar Hajara da ke tsakar gida sai dariya ta leko ta taga…Yaya Zuhra kin fiye abin dariya. Wai Ligan…Legal ake cewa. Zuhra ta hade fuska tace in ba tsoro ba ki shigo dakin nan ki fada mana kiga yadda zanyi dake. Marar kunya kawai. Hajara ma dai dariyar take ta dauko dankwali zata daura. Sai da ta daura wani dakal dakal din mayafi karami. Ta daure shi da ribbons har biyu manya sannan tayi dauri. Daga karshen daurin ta zaro wani ribbon din mai gashi dogo daga jikinsa ta makala taga ya zauna sosai sannan ta tura shi a jaka. Duk abinda take idanun Zuhra kyam a kanta. Tace Hajara gashin doki kika koyi sawa? Da sauri Hajara ta toshe mata baki. To sarkin karadi kada ki fada da karfi sai na fita zan saka. Zuhra tace wallahi babu kyau kuma kema kin sani. Ga acuci kin dora wannan wari ma ya isheki. Hajara tace ke ba yau zan saka ba fa. Yanzu ma gidan Anti Faiza zani tayata aikin abincin da zasuyi a makotansu. za’ayi party ne a gidan. To gobe zansa idan zaa wurin party din. Zuhra tace happy bazday tuyu zasu yi? Oho nima ban sani ba. Tace dai yan gayu ne a gidan. Zuhra tace duk da haka bani gashin na kona ko na fadawa Mama. Da kyar Hajara ta bata ribbon din. Za ta fita Zuhra tace ke kamar kwailin kike ko, kinga fuskarki kuwa? Sai yanzu na lura. Hajara ta dora hannu a ka. So kike dai Mama taji tayi fada kike wani daga murya. Kuma bleaching ake cewa ba kwailing ba kalmar ko dadin ji babu. Tana murmuahi tace wani mai na samu mai dan kyau na gyaran fata. Kinsan tunda biki ya matso gara na shafa na dan washe. Zuhra dai tabe baki tayi…wallahi Hajara ki kiyaye sabon Allah. Ga acuci, ga bleaching ga karin gashi. Shi Sahabin zaki ha’inta da farin karya ko danginsa. Naga dai duk a unguwar nan kuka tashi to meye basu sani ba. Karasa hada jakar tafiyarta tayi tace to malama zuhra idan kin gama waazin ki zo ki rakani bakin titi. Kuma wallahi kika fadawa su Mama sai munyi fada. Zuhra tace mun dade bamuyi ba…ni akan irin wannan ba sai dai aji kanmu ba. Lokaci guda kika tsiri irin wadannan abubuwan kawai don zakiyi aure. Hajara tace to in kinji haushi kema ki fitar da miji mana. Ran Zuhra ya soso ta dan yi murmushi miji dai Allah ke bayarwa. Kuma da yardarSa idan na tashi aure sai na sami miji na gani na fada. Daga nan tayi tsaki ta fita Hajara na kiranta tana bata hakuri. A tsakar gida suka tarar da Mama tace har anyi fadan ne kajin Mama? Ku zo nan…suna harare hararen juna suka durkusa gaban Mama. Tace duk naji abinda kuke fada. Ke Hajara akan an fada miki gaskiya kike gayawa yar uwarki magana ko? Duk canjin halin da kika koya yan kwanakin nan ina lura dake. Shiru nayi so nake farin naki yafi haka yawa sannan nasa yayyanki maza suci ubanki a gidan nan. Zuhra ta kwalo ido….lah Mama kema zagin kike yi. Mama tace ban kuma ce kiyi ba, nima kuskure ne. Ta cigaba da yiwa Hajara fada kije gidan Yayar taku ki dawo zanyi maganin rawar kan nan naki. Ita ma ba kyaleki zata yi ba kin sani sarai. Idan na sake jin kuna fada kuma ni daku ne. Ki wuce ki rakata ta hau adaidaita tace da Zuhra. Sum sum suka tashi suka fita. Zuhra ke rike da jakar kayan amma har suka je titi ko tari basuyi wa juna ba. Sai da adaidaita sahun ya fara tafiya Hajara ta leko tana dagawa Zuhra hannu. Itama dagawa take tana tambayarta yaushe zaki dawo. Hajara tace sai yanzu zaki tambaya? Kwana goma zanyi…..Zuhra harda dan hawaye ta koma gida. Irin wannan fadan sun saba yin shi da Hajara. Sai dai suna sake haduwa zancen ya wuce kenan. Hajara na sallama gidan yayarta ta hadu da babban dan Anti Faiza Abba zaune a bakin kofar gida. Hannunsa ta gani a nade alamun gyaran karaya ko gocewar kashi. Yana ganinta ya rungumeta A dan tsorace tace Babana me ya sami hannunka? Yace fadowa nayi daga kan babur din Baba. Ba dai hatsari kukayi ba ko ta tambayeshi suna shiga cikin gidan. Yace a’a jiya ne da daddare na hau sai na fado. Anti Faiza na jin muryarsu ta fito tana mata sannu da zuwa. Tace kafin ki fara korafi jiya abin ya faru ni kuma bana son tadawa Mama hankali sai ya dan ji sauki. Hajara tace ba komai Allah Ya sauwake. Sauran yaran uku suka zo suna mata sannu da zuwa. Mai bin Abba ce ta kalli Hajara da kyau sai tace Anti Hajara kinga fuskarki tayi fari, kafarki kuma baka. Ko kema mai bleaching ce irin ta fim dinnan….+ Gaban Hajara ya fadi, Anti Faiza ta bar raba kayan wanki da take yi tace bazaki make mata baki ba kina jin abinda take fada. Nabila ta ce Allah ki kalli kafarta da fuskarta ki gani. Anti Faiza ta taso zata kaiwa Nabila duka sai taga Hajara na jan siket dinta tana kara rufe kafa. Anti Faiza tace su fita tana mata wani kallo. Gaba daya cikin Hajara ya duri ruwa. Tun kafin ta tambayeta tace wallahi Mama tayi min fada dazu kuma bazan kara yi ba. Anti Faiza tace da kina hauka ne kika fara shafe shafe. Ta fizge jakar kayan Hajara ta zazzageta a wurin tana duba kayan tana fada. Hajara a hankali ta gode Allah da Zuhra ta karbi ribbon din mai gashi a jiki. Anti Faiza kuwa ta kare mata tas sannan tace ke da Zuhra kuke yi ko? Hajara tana matsar kwalla tace a’a ni kadai ce. Ba wani nan, abokin barawo ai barawo ne kuna tare wata rana zata koya ne. Ta fara laluben wayarta. Zan kira Umma ince a turo min ita ko zuwa asabar ne in ja muku kunne da babban baki. Ba don hannun Abba ba ai gidan zani na hada ku. Wato kun girma zaku nunawa duniya baku da mafadi. Ita dai Hajara sai bada hakuri take. Bayan kwana biyu Zuhra na zaune kan karamar kujera a kofar kitchen Umma na ciki tana duba miya da yar karamar fitilarta gwamnati ta gaza. Zuhra ta rike ciki ta fara waka. Dan kanzo Iya ko dan dago dago Iya yunwa bata da hankali Iya yunwa taci mutum tara Iya….. Umma tace Zuhra ko in miko miki kwano ne? Ta washe baki Umma kin gama girkin. Umma tace a’a wai da ki tafi makota bara. Baki Zuhra ta turo tana rike ciki ni shiyasa bana so kice zakiyi girki Umma musamman tuwo sai ki dade. Miyar nan tun kafin magariba kika dora gashi har an idar da isha. Umma tace ni kuma kinga bana son danyen girkin nan naku. Sai ayi tuwo da miya cikin rabin awa. Suna magana Baban Yara ya shigo. Zuhra tana matse ciki tana masa sannu da zuwa. So take yasa Umma ta kada miyar haka. Dariya yayi musu ya shige ciki. Ga mara juriyar yunwa , ga mai dadewa a girki. A falo suka zauna suna ci. Da yake ba wuta Zuhra kasa jira tayi nata tuwon ya huce tasa mafici tana fifitawa tana ci. Ta cika baki da tuwo tace Ummana kin iya girki sosai sai dadewa. Umma tace bazaki yaba min ba sai kin hada da mita. Wannan mijinki sai yayi da gaske wurin noma. Baba yace to dai kada ki takurawa babata. Ya fito da wata leda daga aljihunsa. Ya danne ta da dungulmin hannunsa sannan ya bude da dayan ya dauko gasashshiyar kaza. Umma tace yau dadi zamu ci BabanZuhra. Yace Ya’u ne ya siya shine ya debar min yace na kawowa Zuhra. Dadi ya kamata taje ta durkusa a gabansa. Cinya ya dauko mata da fikafiki biyu. Ta karba da murna ta koma wurin zamanta. Kamar ance ta daga kai ta hango hannuwan iyayenta a gefen kwano suna kokarin raba wuya su ci. Duk zumudin da take a lokacin wani daci taji a wuyanta. Hawaye ya sauko mata tayi saurin gogewa. Ta dan gutsiri naman kadan tace washhhh. Umma tace kin kone ko? Dama cin abinci kin kasa jira ya huce. Zuhra tace hakori na ne yake min ciwo daga nasa naman a baki. Baba yayi mata sannu. Ta tashi ta mayar da duka naman gashi ku cinye bakina zafi. Baba yace ki ajiye zuwa gobe mana. Idan ya lalace ai sai nayi kuka Baba. Ta dauki tuwon bari na kai kitchen bazan iya ci ba. Ta fice tana fifita baki. A bakin rariya ta tsuguna ta cinye tuwonta ta wanke baki. Umma tace ya naji shiru ko bakin ne. Tace a’a almajiri na nema a waje. Wuraren shadayan dare su Umma sun kwanta Zuhra ta lallabo ta fito falo. Tayi sa’a kuwa ledar naman tana nan kan dan tebur din da suka ajiye tare da jug din ruwa. Zuhra ta bude ledar a hankali ta sami yan kasusuwan da basu cinye ba duk ta tsotse don naman yayi mata dadi. Baba ya taso Umma suka tsaya ta yar kofar jikin tagar dakinsu suna kallonta. Hawaye Umma take sosai a hankali tace bar mana tayi muci. Baba yace muna tausayinta tana tausayinmu. Allah Ya albarkaci rayuwarki Fatima. Suka koma suka kwanta.3 Da safe Umma ta riga ta tashi. Ta fito suka gaisa ta dauko tsintsiya zata fara shara. Umma tace kamar na bar ledar naman nan a falo. Zuhra ta dan tsorata sai tace ai da asuba na dauke saboda beraye. Umma tayi murmushi kawai ta fita tsakar gida.

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE