ALLURA CIKIN RUWA BOOK 1 CHAPTER 15 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA

ALLURA CIKIN RUWA BOOK 1 CHAPTER 15 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA

 

 

Da misalin karfe shida na safe, bayan na yi salah na koma gefe guda na zauna ina jan tasbaha, sai na ji ana kwankwasa mini kofa, na ce,Wanene”

Sai Anas ya ce,Ni ne, bude sako ne daga

Aliyu Gabana ya yanke ya fadi, na tashi da sauri har zanina na faduwa na bude.

Ya miko mini wata katuwar ambulan, sai na ga hohutansa guda biyu

manya, amma ba a cikin gilas ba, sai guda uku

Kanana, da alama ba a kasar nan ya dauke su ba. Daga nan sai katin gaisuwa masu kunshe da rubutun maganganun soyayya har guda uku, daga Kasa yana kara tuna mini sai yazo in anjima, Har wa yau, a cikin ambulan din ya hado mini da wata irin cakulet mai dadin gaske. Na ce a raina, lalle idan na biye wa Aliyu ina shan irin kayan zakin da yake dirka mini nan gaba ba zan ganu ba

saboda kiba. Sai na nufi gado na kwanta na Fara karanta abin da ke jikin katin da kuma maganganun da ya rubutu min, na yi ajiyar zuciya nace Ni da Aliyu ko wa ya fi son dayanmu?”Na tabbata Aliyu na so na, haka ni ma ina matukar sonsa, yanzu idan Aliyu ya rasa ni ko ya ya zai yi? Haka ni ma idan na rasa Aliyu anya zan iya kula wani da namij a nan duniyar kuwa? Da wuya dai, saboda na ga Kabir da ya fara yi mini maganar

so rannan sai na ji kamar ya yarfa mini wuta

Muna tafiya cikin motar Aliyu ni da shi a

gaba, Maryam na gidan baya, saboda hajaru zata  raka Mama inki unguwa, sai Aliyu ya ce,

Asiya wannan motar ta gabanmu ya sunanta?” Na harare shi na ce,Ka ga Aliyu bana so ka bari” Ya ce,nace ke yar kauye ce kin ce a a” Ya fara dariya.Sai na dube shi nace,Oho dai, kauyancin ai tare da kai muke yin sa”, Yace A’a, nikam ba ni ganin passat ince sunny ce

Na juyar da kaina wajen tagar motar ina

kallon tili. Ya ci gaba da yi mini-hegantaka har ya gaji ya Kyale ni. Mun kusa isa gidan da zamu sai ya ce Asiya gaskiya leshin nan ya yi miki kyau, ina ganin jar kala ta amshi jikinki da ruwan ganye, wato danyen kore, ni kuma wace kala ta dace dani Asiya?’ Na Ce,Yar Kauye ta san kyau ne?” Na fadi hakan ina mai langabe kai tare da kashe masa ido. Ya yi murmushi ya- ce,Ke dadina da ke komi cikin soyayya da nishadi kike yi, saboda haka nake Kara mutuwar sonki, ina ganin idan Allah ya sa

munyi aure, ina daya daga cikin maza masu sa’a a duniya, tunda na aje mai faranta mini rai a gida. Irinku ne Asiya mata masu son ko da yaushe su faranta wa mazajensu zuciya, ba tare da gajiyawa ba” Na yi murmushi na ce,

“Ni ina son ma inyi godiyar hotunan da ka aiko mini amma kaqi bari sai tsiya kake yi mini, bayan kuma godiya da nake yi, ina mai kara rokon arzikin abu guda da nake so a bani”

Ya ce,Fadi ko mene ne zan baki tun da na

san ba zai fi karlina ba”To bari sai mun fito tun da mun riga mun kawo gidan da za mu shiga

Abin da ya bani mamaki gidan da muka je

ashe ba gidan Hausawa ba ne, masu gidan mutanen Bendel ne, matar mai kyau haka mijin da yarsu daya mai shekara hudu. Suna da kirki kwarai ainun, mun sha hira dasu, balle da muka samu muka kebe dani da ita da Maryam a wani falo, ta bamu labarin jharsu sosai. Muka kuma shiga kicin muka girka abinci tare da ita, sannan maigidanta ya dauke mu

hotuna dani da ita da ‘yar ta da Maryam.

Aliyu ya lura ya san duk karshenta mai gidan

ya ce zai dauke mu dani da shi, sai ya yi sauri ya fita waje, gudun ya san ba zan so ba tun da mun yi wannan rigimar da, shi, da aka gama sannan ya shigo. Da misalin karfe biyu da rabi muka bar gidan, a inda ta bani kayan shafe-shafe, shi ko maigidan ya bani turare mai kamshi Da muka ja mota bamu tsaya ko ina ba sai gidan Aliyu, sai na ce,

“Haba Aliyu kada mu yi haka da kai mana, idan ka yi adalci sai ka mai damu gida

yanzu Sai ya ce,Wallahi Asia na dan gaji ki yi

haquri in huta sai na kai ku gida,. ki tuna fa yau sauran kwana uku ki tafi, Wannan yana

cikin bankwana da muke yi da ke”

Na bude baki zan yi magana sai ya yi farat ya

sanya dogon yatsansa bisa labbana, ya ce,

“Shiru!”Muka fita muka shiga cikin gida muka sami yaronsa ya shirya mana abinci kala-kala, na ce,Daman ashe da niyya ka kawo mu”

Ya ce,Ba haka bane, na yi zaton ba ra ki

saba da gidan da na kai ku ba, to sai kika bani

mamaki yadda kika saki jiki kuka yi ta hira. Amma gaskiya Asiya Turancinki na da dadin sauraro, ina zaton ke ce ke daukar na daya a fannin Turanci?”

Na yi shiru ina jin dadin sauraron maganarsa,

can na amsa masa na ce,A’a, ta biyu nake dauka, sai dai a lissafi nake daukar ta farko

Na hango Maryam ta gama alawala ta fara

sallah, na yi sauri na shiga kewaye na fara alwala, yayin da shi ma Aliyu ya shiga nasa kewayen don ya yi shirin sallah.

Na fito falo na sami Maryam har ta yi barci

bisa kafet, Aliyu ya ce,

“Yanzu ya ya za ayi kenan ko a kai ta bisa gado?”Na ce,A’a, rabu da ita a nan sai dai a kara sanya mata matashi

Shi ma Aliyu ya sanya kayan barci ya zo ya

kwanta bisa doguwar kujera, ya ce,

“Kai Asiya dama ace har mun yi aure babu inda za ki yanzu sai da izinina Na ce,

‘”Aliyu kana da dauki da yawa, idan

Allah ya nufe mu da aure, har sai nama gundure ka nan gaba” Ya ce,Kada Allah ya

nuna mini wannan ranar da zan ga kin gundure ni, ya ya maganar dazun da kike son wani abu a gare ni?”Na gyara zama na ce,

“Aliyu na ga wancan

hoton da yawa a gidan nan… (sai na nuna hoton

Hmmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE