ALLURA CIKIN RUWA BOOK 1 CHAPTER 17 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA
ALLURA CIKIN RUWA BOOK 1 CHAPTER 17 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA
Ni Aliyu ni kadai ne a wurin mahaifiyata, amma mu goma sha daya ne a wurin mahaifina.
Lokacin da mahaifiyata ta haife ni ina da
shekara biyu suka rabu da mahaifina, a inda ta koma Kankiya da zama wajen Kanin tsohonta, saboda dama marainiya mahaifina ya aure ta. A nan ta dinga zama har sai da na sami shekaru bakwai, sannan mahaifina ya amshe ni. To wannan fa shi ya fi ta da mata hankali saboda a dalilina ta ki aure, sai fa cututtukan zamani suka sarke ta, kamar ciwon zuciya da hawan jini, har Allah ya ba ta wani miji ta aura. Idan ta sami sarari ta kan zo ta ganni, kuma Allah bai Kara ba ta wani rabon ba. Ina da shekara goma ciwonta ya tsananta a dalilin rashin ganina da
take yi, har ta baro dakin mijinta ta koma gidan kanin tsohonta. Kanin mahaifina ya nemi da ya rinka bari na ina zuwa hutu wajen ta, sai mahaifina yaqi, ya ce shiya”yansa ba su zuwa ko ina, idan dai ta so ganina ta zo inda nake bai hana ta ba. Ciwon zuciyarta ya Kara zafi na wani lokaci da ta sami sauki ta koma dakinta. Ina da shekara sha
biyar rannan sai Allah ya bata wani cikin, kwanci tashi. ta haihu. Allah ya ba ta tagwaye mace da namiji. Bayan kwana biyu da haihuwarta aka ce jini ya tsinke mata, a rana ta uku ta ce ga garinku nan. Su ma tagwayen a hankali da dai-dai da dai-dai suka
bita To kin ji dalilin da yasa nake ciwon son
mahaifiyata. Yanzu haka ko mai sunanta na ji, idan ina tafiya sai na tsaya na dube ta duba irin na da da mahaifi, idan naga tsohuwa ce, to har alheri sai na tsaya na yi mata. Idan har Allah ya bamu haihuwa ya ‘ya mata, to a gaskiya ko goma kika haifa mini duk sunansu zai kasance suna iri daya wato sunan
mahaifiyata Ni kuwa tunda ya fara bani labarin
mahaifiyarsa sai tausayin shi da ita ya kama ni, ban san lokacin da kwalla ya digo mini ba.
NaCe,Ni kuwa Aliyu na yi alkawarin duk
lokacin da nayi sallah sai na karanta mata
Kulhuwallahu kafa uku, in dai ina numfashi
a duniya Ya ce,
“Na ji dadin wannan alkawari da kika
dauka Asiya, kin ga na san za ta yi alfahari da samun suruka ta gari yanzu ta bar
“ya ya biyu ke nan a duniya masu yi mata addu’a a kullum Ya tashi yana fadin,
“Gara mu tashi mu yi sallar la’asar, ga masallaci can ana kira
Ya shirya ya tafi masallaci, na tashi Maryam
na shiga bandakin da ke cikin dakin Aliyu na sa makulli na kulle, na yi wanka cikin sauri na yi alwala na fito na zauna na yi kwalliyata, sannan na ta da kabbarar sallar la’asar.
Sai da na gama tsaf, Maryam ta ce,
” Anti Asiya ni ma shafa mini jan bakinki
. Na ce, To” Na bude jakata na dauko na shafa mata. A daidai wannan lokaci ne Aliyu ya shigo, ya tsaya ya dube ni ya yi murmushi ya ce Nima bari in yi wanka yadda kika yi kada ki fini kyau, saboda yanzu Kaduna Club zamu mu yi wasan kwallon tebur a ga ni da ke wa ya fi iyawa, tun da an ce ke gwana ce a makarantarku” Na yi dariya na ce,
“To shi kenan gama wankan mu tafi”
Muna zaune a falo muna kallo da ni da
Maryam, ban ji motsin shigowar Aliyu ba ya tsaya a bayana, sai na ji saukar ruwa da yake ta je gashinsa a bisa bayana. Na yi ajiyar zuciya na daga kaina sama muka
yi ido hudu da Aliyu, na ce,Kai Aliyu””. Muka yi
murmushi,Sannan yaCe haba Asiya”
Saiya Kyalkyale da dariya. Yace bismillah, gara, muyi harama ko?”
Aliyu ya saka “yar shet dinsa baka da bakin
wando, da muka shiga mota na bude jakata na fiddo bazuka cingam na bai wa Maryam guda daya, na bare guda na saka a bakina, sannan na fiddo daya naCe,
“Aliyu ga bazuka cingam Ya ce,
“‘Ai da na yi zaton kason ba dani ba”. Na ce,
“Wa ce ni? Yallabai har na isa”.To na gode, karasa ladanki ki bare mini”.
Na bare masa sai ya juyo ya dube ni ya bude
mini baki, na ce,Kai
Aliyu ga ciki ga goyo ga zanin daurawa’
Ya ce,Idan ba ki saka mini bai wa Maryam
“ta saka mini”Na ce,Maryam ga shi ki ba Aliyu cingam a baki? Sai na ji Maryam ta ce,
“Kai Anti Asiya ke yafi dacewa ki ba shi, amma idan ba ki iyawa bari in saka masa”.
Sai Aliyu ya fashe da dariya, ya ce,Da kyau
Maryam, kin ga yarinya karama ta fi ki wayo”
Sai na harare shi a lokacin da ya Kara bude
baki na yi saurin jefa masa, na yi sa’a ya shiga ba tare da hannuna ya taba labbansa ba,
Ya ce, Kai Asiya ina da aiki a gabana”.
Na ce,Wane irin aiki kuma?”
Ya dubeni yana mai lumshe ido ya ce,
“Ba komi manta kawai”. A haka muka isa Kaduna Club. Bayan ya gama abin da ya dace ya yi a wurin, sannan muka nufi inda tebur din wasan yake. A nan fa Maryam ta
zama yar kallo muka fara wasa, da farko abin
gwanin ban sha’awa, mun dauki tsawon minti goma sha biyar ba tare da an ci wani ba, sai zuwa can
Kwallo ya sulle wa Aliyu ya amince da wannan ci na farko. Na sake ba shi na biyun, nan ma ya amince da babu gardama. Amma a karo na uku sai ya ce,Ban yarda ba kina yi mini wasan Keta don ki dibga mini kwallo”
Na ce,Haba wane irin wasan Keta kuma?”
“To shi kenan mu zuba dani kike wasa”
Haka muka zuba dani da Aliyu, idan ya jefa
mini kwallo ta wani gefe in bi wannan gefen in
tallabo ta, da haka har muka gaji da wasa muka tashi. Ina da ci biyar shi kuma ya ba ni ci daya tak! Muka yi masa dariya ni da Maryam.
Yayi kwafa ya ce,Haba kyale ki dai kawai
na yi, amma zan rama wani lokaci?”
Na cé,San dai wani lokacin, amma wannan
karon an gama dai, ci dayan ma kyale ka na yi
saboda na tausaya maka, don na ga ka fara
galabaita”
HMmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe