ALLURA CIKIN RUWA BOOK 1 CHAPTER 18 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA
ALLURA CIKIN RUWA BOOK 1 CHAPTER 18 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA
Da ya taka mota ba mu zame ko ina ba sai
Ieventis, a nan ya ce in zabi abin da raina ke so a sai mini a madadin kyautar da zai yi mini ta nasarar dana samu a wajen kwallon tebur.
Nayi shiru, na ce,Abinda duk ya ga ya
dace da ni”Shi kuma ya ce dani in zaba. Sai na dauki wani biro parker mai kyau. Ya yi dariya, sannan ya dauko wani biro mai kyau da aka rubuta wa One love a ciki da kwalbar turare mai suna Rememher me, sannan ya sayi cakulet da biskit da cingam masu dadi.
A wannan rana bamu isa gida ba sai gab da
magariba. A wurinmu Aliyu ya yi sallar magariba da isha’i ya ci abincin dare, sannan ya koma gida. Ana sauran kwana biyu in koma Malumfashi, muna zaune a falo dani da Mama Inki da Alhaji mijinta, da yaran gidan, duka, sai Alhaji ya bani kudi har dari biyar yace ko zan yi wa kannena tsaraba, ya kuma bani turmin atamfa yar kasar waje tare da
bandir din farar shadda ya ce in kai wa mahaifina. Na yi masa godiya mai tarin yawa, wanda har na ma rasa kalmar da zan yi amfani da ita saboda jin dadi. Shi kuwa ya ci gaba da yaba mini a kan irin tarbiyyar da nake da ita, da rashin hayaniya, da nuna
halin kamun kai da nake da shi.
Ya Karfafa mini ta inci gaba da mai da hankali a bisa karatuna ganin ina cikin Kankanin
lokaci da zan kammala shi. Ya kuma ba ni shawara cewa, yana son in cika form na shiga jami ‘a saboda dai ya san mahaifina ba zai hana ni wucewa gaba ba
Bugu da Kari na yi sa’a za ni shiga jami’a da
matsakaitan shekaru. Sai yake cewa,
“Da zarar an fara sai da form
ki saya ki cika ki aiko da shi, a fara nema miki
makaranta da ita” Ni kuwa sai na nuna masa daman wanna shine raayina. Ya
kara nuna mini in shaidawa mahaifina
kada ya sami damuwa na daukar
dawainiyar karatuna a jami’a, yayi
alkawarin taimakawa ta kowanne bangare.
Idan ma son samu ne zai yarda in na shiga
jami’a In koma hannunsa da zama saboda
Malumfashi karamin gari ne kada a damu mahaifina da surutu a kaina har ya yi fushin zuciya ya fidda ni. Na nuna masa wannan bahu komi mahaifina yana sha’awar karatu ba zai taba yarda ya dauki shawarar wani ba, idan dai ba daga wajena aka sami batanci ba, wanda kuma insha Allahu hakan ba zata
faru ba. A wannan dare bayan na kwanta barci na yi tunani irin wannan arziki nasu Mama Inki,
wanda kuma kowa yana karuwa dasu, ba wai
mu yan uwansu kawai ba, hatta ma’aikatansu
suna hutawa da su. Na dubi irin gadon da nake kwance na ga nan da kwana biyu zan koma bisa dan bonona a gida, nace.
“Uhangiji Allah ya bamu ilimi da zai amfani
rayuwarmu ta duniya da lahira
Na sha alwashin in dai har ilimi na sanyawa
kaji dad irin wannan, to insha Allahu sai nayi ilimin da zan ji wanna dadi ni da iyayena duk mu dandana irin wannan rayuwar a dalilin iliminmu Da irin wannan burin barci ya dauke ni
Ranar alhamis ana gobe Juma’a za ni gida, da
misalin karfe goma da rabi muka shirya zuwa
kasuwa da ni da Mama Inki. A kasuwar na sayawa Zainab bebin wasa guda biyu, da yan rigunan sawa guda biyu da takalmi. Shi kuma Yusuf na yi masa tasa tsarahar, Yaya Abubakar na saya masa agogo.Ita kuma mahaifyata na sai mata wasu takalma
masu igiya saboda na san ba za ta sanya takalmi irin na Mama Inki ba. Mahaifina na saya masa dara, ita ma hadiza nayi mata tsaraba kamar kayan faninmu na mata, wato pant, under wear da makamantansu.
Mama Inki a nata hangaren ta kara saya mini
sutura kala-kala abin ba a cewa komi, sai dai addu’ar Allah ya yi musu sakayya da alheri, amin. Ta kuma kara yi mana sayayyar kayan makaranta da ni da Yusuf wanda ban yi mamaki ba, saboda duk hutu Tana aika mana
Bayan mun koma gida, ina zaune a daki ina
duba irin kayan da na samu da tsarabar da na yi wa yan’uwana, dadì ya kama ni, na ji babu abin da nake so irin in ganni a gida gobe. Ina cikin wannan hali sai ga Mama Inki ta
shigo, ta dube ni ta yi murmushi tace
“Ga wannan akwatin na san jikar da kika zo da ita ta yi kadan”.Na dubi akwatin dankarere
mai taya mai ruwan bula, na yi ajiyar zuciya sannan na fara godiya.Ta ce,A,a, Asiya abin da duk muke yi miki muna yine a matsayin ke
‘yace a gare mu, kuma abin da ya cancanci in yi miki ne ke nan saboda bani da wadanda ya
fiku a duniyar nan, kin ga ya zama dole in yi miki kulawa ta sosai, saboda ranar
Kiyama ku zan gani, Yaya Aisha kuma taga su Abba. to kin ga babu bambanci ke nan.
Abin da nake so da ke ki saki jikinki, ya isa ki
daina dari-dari da ni, duk abin da kike so ki rika fada mini ni da Aisha duk daya ne a gare ki”Na ce,To Mama Inki’Can kuma tace mini,
“Ga wata talabijin nan a falo idan zan tafi gobe in wuce da ita, ta gaya mini
ne yanzu don karta manta Na yi tunani wai! Naso in ga Zainab da T.v)
a gidanmu, an huta da zuwa gidan Alhaji Talle kallo kenan. Na zauna na shirya kayana
cikin sabon akwatin da aka ba ni, na rufe shi da kayan sun cika shi.
Hmmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe