ALLURA CIKIN RUWA BOOK 1 CHAPTER 19 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA

ALLURA CIKIN RUWA BOOK 1 CHAPTER 19 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA

 

 

Muka zauna muna hirar hankwana da yaran.

gidan duka, sun dame ni don Allah idan anyi mana wani hutu in Kara zuwa nan Kaduna.

Nace To, idan babana ya amince zaku

ganni” Sai Hajaru ta ce,Idan an yi hutu za a kawo mu, mu roki haban da kanmu

Na ce, “To sai na ganku Maryam ta ce,

“Anti Asiya yau za ki yi mana

tatsuniyar bankwana ko?” Na ce,Eh”Sai Hajaru ta ce,To mu tashi mu je dakin

Anti Asiya a fara yau da wuri Muka dunguma zuwa dakina, na fara yi musu tatsuniya kala-kala, amma ni hankalina na wajen Aliyu ina sauraren zuwan sa, domin na san tabbas

zai zo sallama. A lokacin da na shiga cikin tatsuniya kashi na biyar sai kuma na ji an turo mana kofar daki, wanda har ya sa muka ji toro, ashe Baba Suraj ne tare da Aliyu. Suka ce,

“Ku baku ji ana sallama bane?” Muka nuna sam ba mu ji ba. Bayan mun gaida su, sai su hajaru suka tashi suka fita gaba daya

tare da Suraj aka barni da Aliyu. Aliyu ya zauna bisa kafet ya nemi ni da in bashi filo ya dan kishingida, sannan ya bani wata leda

yace Ga kaya nan in bude in gani Na bude sai na ga wata jaka ta yanmata da

takalmi rufaffo farare sol masu tsini, da kuma dinkin yadin kafì shadda riga da zani

da dankwali masu ruwan kwai, dinkin rigar kuwa an yi doguwa har gwiwa, a inda aka yi mata kwalliya da wani zare mai

walkiya. Na daga kai a hankali na dube shi, duba irin na magana da ido. Ya kara kishingidewa kamar wanda ya yi aikin gona ya gaji, ya lumshe ido ya ce,Wannan dinkin anko na yi mana, saboda haka gobe za ki sanya idan za mu tafi Malmufashi Nace Yanzu Aliyu wata hidima ka sanya kanka haka bayan irin dawainiyar da kake mini?’Ya yi murmushi yace,

“Asiya da sauran ki,idan baki sani ba yanzu bani da wata hidima wadda ta fi taki tsarabar su Inna kuma tana gida, sai gobe zan sanya a mota idan zamu tafi, saboda naga wahala ne sai na kawo na kuma Kara mai dawa a mota

A nan na yi masa godiya mai tarin yawa,

sannan Yace mini, “ga hotuna can da kika lika ba ki cire ba kada ki manta da su gobe Na yi saurin na rufe do don kunyar abin da ya fada.

Ya yi murmushi yannan ya ce,

“Ko in dauko miki?” Na ce,A’a, ka bari

insha. Allahu bazan manta ba idan na idar da sallar asuba gobe zan dauka Muka dubi juna

muka yi murmushi. na sunkuyar da kaina kasa a yayin da ya ci gaba da kallona zuwa wani dan lokaci Na ji an kwankwasa kofa, na ce,

“Shigo” Ashe Anas ne, ya dube ni sannan ya dubi Aliyu, ya yiyar Karamar dariya yace “Kabir ne yaZo yana can cikin motarsa a bakin get, daman dazun da kuna kasuwa ya yi miki waya na manta in gaya miki, amma ya tambaye ni na shaida masa gobo zaki koma Malumfshi”

Na yi ajiyar zuciya tare da tagumi, na rasa

amsar da zan ba Anas. Sannan Aliyu yace

“To kiji da Anas mana kin barshi a tsaye

Na nuna neman shawara a fuskata a gare shi,  nan ya gane abin da fuskata ta kunsa.

Sai ya tashi zaune tsam ya cewa Anas,

“Ka shaida wa Kabir tana tare da mijinta

Daga nan Anas ya ce,TO”. Ya fita. Shi kuma Aliyu ya tsare ni da idonsa yana son ya ga abin da fuskata zata bayyana masa, ko jin

dadin abin da ya fada ko rashin jin adadin hakan. Na yi masa kallo mai sanyaya rai da nuna jin dadin ya warware mini wannan matsalar, sannan na neme” shi da zance don in Kara tabbatar masa da amincewa har cikin zuciyata. Na Ce,Aliyu”Yace na,am Asiya, mene ne”?”Na ci gaba da cewa,Yanzu idan kun mai dani Malumfashi kun koma yaushe zaka Kara zuwa wajena?”Ya yi murmushi ya ce, “Sai Juma’a ta sama wadda zanzo muyi sallama, saboda a wannan satin zaki koma makaranta ko?” Nace eh Sannan ya ci gaba da cewa,

“Daga nan kuma sai ranar ziyara zanzo ziyararki ko na yi daidai”Na daga gira na ce, “Eh, ka yi daidai”A daidai wannan lokacin ne Anas ya kara sallama ya shigo, ya miko mini wata doguwar ambulan yana murmushi, a  fuska na ce,Anas ba ka gaya masa abin da aka ce maka ba ne?” Yace

“Wallah na sanar da shi, amma sai ya

yi mini dariya ya bude aljihun motarsa ya fidda takarda da biro ya rubuta miki ya ce in kawo miki shi ya ta fi, sai kin gan shi a Malumfashi”

Na yi shiru. Bayan Anas ya tafi na rike

ambulan ina juyata a hannu na rasa abin da ke mini dadi, na kuma lura da Aliyu ya kura mini idanuwa da nuna alamar bai ji dadin wannan aike ba. Ga alama dai wannan ambulan tana kulle da makudan kudi ne, musamman ma idan an lura da yadda take nauyaya hannu.

Zuwa can Aliyu ya ce,Ki bude mana ki

karanta, barin kashi a ciki ai baya maganin yunwa Na Kara daure

fuskata sannan na. bare ambulan, na ga daurin kudi dauri biyu, wanda ko

wane dauri yana kunshe da kudi naira dubu daya sababbi fil ko lankwasa babu. Na bude “yar karamar wasika mai dauke da gajeran sako kamar haka.

Barka da yammaci, ya mutan gida?

NaSo ganinki  Kafin ki koma

Malumfashi, amma hakan bai yiwu ba, na ji sakon da wani ya ari bakinki ya ci miki albasa wanda bai dame niba, saboda haka na yi imani da cewa, karya yake yi ba mijinki ba ne dan nema ne kamar ni, ina

ba shi tabhacin cewa mu zuba dani da shi shege ka fasa, dan halas sai ya yi.

Hmmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE