ALLURA CIKIN RUWA BOOK 1 CHAPTER 23 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA

ALLURA CIKIN RUWA BOOK 1 CHAPTER 23 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA

 

 

so. Sai nake cewa,Ni wallahi Hadiza ban ki ba

amma sai mun yi aure da Aliyu kafin in ci gaba da makaranta zuwa jami’a, saboda idan so yayi yawa ba abin da ba ya sawa”

Ta ce,Kina da gaskiya Asiya, nima abin da

na fi so ke nan a ra’ayina, amma wancan satin da yazo ya fara yiwa Inna Hafsatu maganar kawo kayan zance sai tace a’a komi a hankali za ayi shi, saboda sai Yaya Aminu ya dawo za a yi maganar aure na Na tambayi Hadiza aikinsa da shekarunsa. TaCe,Asiya yanzu shekarunsa ashirin da bakwai, yana

aiki a babban kamfanin nan na karafa da ake kira Steel Roling Katsina Muna tsaye naji an

fara kiran sallar magariba, na ce,Bari in je gida anjima Aliyu zaiZo idan ya z0 zan aiko a kira ki”Muka yi sallama, muka nufi gida dani da

Zainab. Tun a gidan su Hadiza Zainab ke damuna da tambayar ko na sayo mata “yar bebi? Muna isowa gida ta fara fitina ta da in fiddo mata bebin. Na ce,Ke ni Zainab kada ki matsa mini sai na yi sallah zan ba ki

Ta bata fuska sannan ta takure a gefe tana fushi. Sai Inna tace Haba Zainabu ki yi

hakun mana a yi sallah, ba kya ganin ma an dauke wuta, ke ma ai gara ki tashi ki yi sallah” Na gama sallar isha ke nan aka maido wuta.

na yi sauri na debi ruwa na yi wanka na yi shafe-shafena na gama sarai. Kayan da na iso da su suna falo tattare wuri daya, lokacin nan kuma Inna na falon zaune tana shafa rob a kafafunta saboda suna mutsuka mata.

Na gangaro Katon akwatina zuwa kusa da ita,

“Inna gafa hidimar da Mama Inki ta yi naCe

Na bude akwatin yayin da Zainab ta fara tsalle-tsalle da irin Kara ta yara ta nuna ta kusa cimma burinta. Saboda haka Inna tace

“Don Allah Uwani sallami Zainab mu huta da wanna karar’Na bude akwati na fiddo mata da bebi guda biyu masu gashi babba da karama, nace Tsaya ki gani Zainab

Ta tsuguna a gabana hannayenta bisa

cinyata, yayin da na murza wani Karfe a jikin babbar bebin. saiyar behin ta fara kuka irin na jarirai inya!Inya!! Zainab ta kara rikicewa don dadin samun abin da bata taba gani ba, kuma an ce duk nata ne,Ta dinga yi mini godiya iri-iri, ta koma gefe guda da

“‘yar bebinta ta barmu muka sake na ji dadin nunawa Inna kayan da Mama Inki ta sai mini, Inna tace Uwani ai wannan suturar ba ta

kirguwa Sai na ce,Karamin aikin Mama Inki ke nan,ke ma ai bata barki hakà ba Na fiddo atamfa kala uku masu tsadar gaske, nace

“Wadannan cikin kayanta ta baki”Ta rike baki ta ce.Duk ni ke da wannan Uwani?” Na ce,eh

“Na ba ta tsarabar Yusuf da Baba

da Abubakar, sannan na ba Zainab kayan da na sayo mata. Nace

“‘Inna wannan sarkar da ‘yan kunnen na

wuyana cewa ta yi in rika sanyawa, idan ta je Umara ta sayo mini manya sannan in bai wa Zainab su”Na ci gaba da cewa,Zainab mene ne a wancan babban kwalin?”

Ta ce,Wallahi Yaya Asiya ban san ko mene

ne ba, gaya mini don AllahSai na yi murmushi nace,Talabijin Ce Mama Inki tace in kawo wa Baba mu dinga kallo Sai ta Kara rudewa da sabuwar murna, tace, Yaya Asiya kunna mana

Na ce,Ke ‘yar kauye sai Yaya Abubakar ya

dawo zai sawo Waya ya hada mana, sannan hoton zai fito sosai” Inna tace

“Ni abin ma wallahi duk ya daure

mini kai, wannan irin hidima, ba ita ba, ba Alhajin nata ba?” Nace Wallahi kuwa

Sa inna tace Wadancan dirka-dirkan kwalayen fa?”Sai na saki fuskata cikin nishadi na sunkuyar da kaina Kasa,

na Kara rage sautin muryata kasa- kasa nace

“Wannan Aliyun ne ya kawo muku,katon din omo ne da sikari da sabulai da madara, ni

kuma ya dinka mini wadannan kayan da wancan takalmin (na nuna da hannuna) da jakar da na ratayo dazu Ta yi shiru tana jinjina yawan kayan da Aliyu ya bamu, ta dauki lokaci mai tsawo tana kara kakabin abin a zuciyarta, yayin da na ci gaba da yi mata bayaninsa da iyayensa. Sai kuwa ta ce, Tana jin labarin mahaifinsa, amma bata san shi ba tun da komai sai ya yi dalili, kuma shiga gidan masu hali irin mahaifin Aliyu saida musabbabi.

Amma Uwani ina shakkar soyayyarku da irin

wadannan mutanen, ko da yake komi na Allah ne, kuma Allah ba ya halicci mai kudì don masu kudi kawai ba, haka dan talaka, sal

dai abinmu na mutane. Kuma tunda shi ya gani yace yana so ba talla aka yi masa ba ai shi kenan. Idan kin amince da shi sai ki tsai da shi ban da ruwan ido, ban da kuma

canje-caje”Da na ji tayi shiru na kuma tabbata Aliyu ya sami karbuwa a wajenta, sai na bata fuska na rika magana cikin rashin amincewa abin da ke fita bakina. Na zayyana mata maganar Kabir tun daga farko har karshe, na mika mata tulin kudin daya ba ni da yadda muka yi da Mama Inki, Ta yi shiru cikin damuwa irin ta manya,sannan ta nisa tace

“Hajiya Inki ta nuna halin Kuruciya a nan, ai da ba ta bari wadannan kudin sunZo wajenmu ba tunda ga yadda kika nuna masa.

Abin da ya dace ta yi ta aje kudin a hanunta,

sai ran da ta sami zuwa nan, mun san shawarar da zamu yanke”

Sai na yi sauri na ce,Abin da nace mata ke

nan, amma ta ce a’a, mahaifina ya kamata ya yanke wannan shawara Muna cikin tattaunawa na irin abubuwan dake gudana a game da zuwa na Kaduna, sai na fiddo

da wani dogon wando da rigarsa iya gwiwa masu ruwan hoda, Yadin mai sulfi ne yana walwali da rawa, ga dinkin an yi shi mai gajeran hannu, yayin da aka zizara leshi a hannu da kasan rigar, shi ma wandon

an zizara maya farin leshin a bakin

Hmmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE