ALLURA CIKIN RUWA BOOK 1 CHAPTER 24 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA

ALLURA CIKIN RUWA BOOK 1 CHAPTER 24 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA

 

 

kafafunsa tare da roba ta matse bakin, sannan ga gyale da ya dace da kalarsà.

Na tashi na zuba su, na sami Yar siririyar

sarka wadda ta dace da kayan na Sanya.na

daura agogo mai yar Karamar leda, amma ban daura dankwali ba, Na sanya wannan gyalen na rufe kaina. Zainab ta zuba mini ido kai kace bata taba ganina ba wai wannan dare, ita kam mahaifiyata tayi sha,awata a wannan lokaci. Zuwa can ta tambayeni. Wadannan kayan a kasar Makka aka sayoSu ko?”Na yi dariya nace,A’a, wani abokin Alhaji ne ya kawo mana yadin daga Indiya shine yace a dinka mini dasu hajaru”Ta ce,Lalle wadannan mutane sun iya dinki,babu yadda za a ce ba ‘yan kanti bane A daidia wannan lokaci muka ji gyaran

muryar mahaifina, muka yi sauri ni da Zainab muka tarbo shi, muna sannu da zuwa Baba.

Yace Uwani saukar yaushe?” Na ce, Da la’asar muka iso Yaya su hajiya Inki da Alhaji?”Nace, “Baba suna laliya, sun ce a gaishe ku,ya ya Malam Abba da jikin Baba?”A’a, ai ya sami sauki” Daga nan suka fara gaisawa da Inna tana tambayarsa mai jiki, sannan ya umarceta data kai masa ruwan wanka. Bayan ya shiga wanka ne sai ga Yusuf, ya ce,

“‘Aliyu yace ga shi yazo Na ce, “Zainab zo muje Yaya Asiya da wanka zan yiwa

bebina”Na ce,Kin ga Zainab idan bata *yar bebin nan za ki yi zan Kwace?

Ta Ce,To na fasa mu je in raka ki”.Na same shi a kofar gida yana zaune a bisa

kan motarsa, na yi masa sannu da zuwa, sannan na neme shi da mu karasa dakin Abubakar. Muna tafe

muna hira da irin kallon da yake yi mini na sha’ awa da yaba kwalliyata tayi masa tsari.

›- Muna zaune a dakin Abubakar ya ce mini.

na “Asiya bana son rabuwa da ke har na lokaci mai tsawo, saboda haka na matsu kwarai da in bayyanawa iyayena game da ke, yadda su kuma zasu zo don su bayyana bukatata ga mahaifinki. Yanzuma zan koma gida da wuri don in sami ganin mahaifina a kan maganar Na yi ajiyar zuciya sannan na daga kaina na

dube shi na yi masa murmushi na kara sunkuyar da kaina. Ya cE

“Baki ce komi ba Asiya” Na ce,

“Aliyu me kuma kake so ince yanzu

ni,ai magana na gare ka Sai na dubi Zainab nace,

‘”Zainah amza kije gidan su hadiza ki ce tazo ga Aliyu yazo Ta yi sauri ta tafi, daman tana neman hanyar da zata  gudu ta koma wajen bebinta. Muka hada ido,da Aliyu ya daga mini gira, sai nan da nan muka yiwa juna murmushi.

Ya ce Asiya da ina da iko a wannan dare,

babu abin da zai hanani daukar ki in saba ki a bisa wuyana in dinga bin titi ina nuna wa jama’a irin son da nake yi miki, sannan in dire ki gaban dakina. Kila shi zan iya nuna wa mutanen Malumfashi da iyayena dan kadan daga cikin irin son da nake yi miki Na ce,

“Aliyu ko baka yi haka ba za a san kana sona, saboda yanmata nawa ka wuce sannan

ka zabe ni? Ka wuto wadanda suka dama ni suka shanye don kyau, balle kuma wajen maganar arziki ka baro dukkan ya yan masu arziki kazo gare ni yar talakawa likis. To wannan ya isa ka baiwa

jama’a tabbacin tsagwaron kauna da son da kake nuna mini daidai wannan. lokaci

sai hadiza ta yi sallama ta shigo, suka gaisa da Aliyu. Sai kuma yace Asia dawo bisa wannan kujerar kusa da ni ki zauna ki ba Hadiza wannan Na harare shi na ce,

“Kai Aliyu ai ba ta zama bakin gado”

Sai Hadiza ta ce,Idan dai kina so mu yi

hirar, to ki matsa bisa doguwar kujerar da yace, inko ba haka ba kin ga tafiya ta”

Aliyu ya ce,Yauwa Hadiza, lalle za mu

shirya da ke”Na je na zauna haka nan, daman kujeru biyu ce, da doguwa daya da karama daya. Sai Hadiza taCe,

“Asiya mene ne na hada kai da gwiwa? Ko

saboda na zo na takura muku ne? Ni yadda kika bani labarin Aliyu ai na yi zaton kin fara sakin jiki dashi, babu sauran jin kunya”

Aliyu ya gyara zama ya Kara matsawa daf da

inda nake zaune, ya ce, “Ai ni Hadiza abin tausayi ne in kinga yadda Asiya ke yi da ni, idan kin ga yadda take guduna ke kin dauka ina da cutar kuturta ne Ni dai ban daga kai na dube su ba, ban kuma ce uffan ba. Da na ji sun matsa mini sai na ce,

“Ke Hadiza yanzu haka kike wa Mukhtar kina zama kusa da shine?” Sai kuwa ta ce,

“Ai kuwa zaki yi mamaki idan Allah ya kai mu gobe, hatta abinci Mukhtar idan muna tare dole ne in ba shi a baki Karewar zama kujera daya kenan

Aliyu yace “Hadiza ya kamata ki rika wayar

mata da kai, irin wannan kunyar ai ina kwaruwa, ace mutum ba zai saki jiki da masoyinsa na hakika ba, a yi kwalliya amma ba za a bar mutum ya kalla ba

Sai ya ci gaba da matsawa kusa dani yana

kokarin janye hannayena, yayin nanne naji

numfashinsa na sauka cikin kunnena, sai kawai ya sanya hannayensa

ya dago ni gaba daya yana

kokarin dora ni bisa cinyarsa, na samu na zulle da Kyar, inda na lura da tsigar jikinsa duk ta tashi, ya koma ya zauna yana mai da numfashi da sauri.Na zauna bisa gado na yi tagumi har na zuwa wani lokaci, sannan na dan dago kaina kadan na ce,

“‘Aliyu ka manta ka ce yau da wuri za ka tafi saboda kana da uzuri?”Ya ce;Kin ji ko Hadiza har ta fara kora ta Hadiza ta ce,

“Ke dai Asiya kin bani tunda abin naki haka ne, idan Aliyu ya zo ko kin aika inzo

ba zanzoba, sai dai idan zai tafi ya leko mu gaisa”Sai na ce,Haba Hadiza Allah ba wani abu yasa na ce haka ba, akwai dalilin da yasa na tuna masa, shi ai ya san maganar

Aliyu ya yi dariya ya rika tambayar hadiza

labarin Mukhtar, har muka sami lokaci mai tsawo muna hira.

Da misalin goma da rabi muka raka shi har

Jikin mota, na bude masa motar ya shiga, sai ya ce,Ko tare za mu tafi ne Asiya?”

Na ce, “Aliyu idan har ka ga ya dace, to sai

mu tafi” Ya ce,”A’a, bai dace ba, amma in Allah ya yarda an kusan dacewar, kin ga Asiya kin tsare ni da hira yau ba zan sami ganin Baba ba Na ce,

“Kin ji irin ta ko Hadiza, sai da na tuna

masa amma ya ce ina korar sa ke kuma kika daure masa gindi, to kin ji kuma me za ki ce a nan Hadiza tace “Abin da ya faru Asiya har ya

zama lai finki shine da farko ba ki ba da hadin kai ba aka yi hira kamar yadda Aliyu ke so, sai daga karshe sannan muka sami hadin kanki”

Na ce,Ai Hadiza na dai lura Aliyu ba ya

laifi wurinki Aliyu ya kyalkyale da dariya ya ce,

“Sal Allah ya kai mu gobe kin ji ko, kun ga tafiya ta Muka yi sallama,hadiza ta shiga gida, nima na shiga namu gidan.

Washe gari daga ni har Hadiza bamu huta ba,

muna shirye-shiryen ahincin manyan bakinmu. Mun sami zabinmu lafiyayyu, muka yi miya muka kuma soya wasu, sannan muka dafa musu sufagetti da kuma alale mai hade da hanta da Kwai a ciki, sai fura da nono dame da kindirmo. A cikin dan lokaci kankani muka kammala muka shirya abinci nau’i-nau’i. Da misalin sha biyu muka fesa wanka,

inda na aiki Zainab da wata atamfa

yar England ta kai wa Hadiza ta yiwa

Mukhtar kwalliya. Ta rubuto mini “yar wasika ta nuna mini jin dadinta a kan wannan taimako da na yi. Sha biyu da rabi Aliyu ya iso, a inda Suraj ya kawo shi, yayin da shi kuma ya wuce Funtuwa wajen tasa sahibar.

Bayan mun gaisa da Aliyu sai na Kara shiga

gidan na fito masa da alala da soyayyun zabbi da yankakken lemo da ruwan sha.

Ya dube ni ya yi murmushi ya ce,

“Asiya kamar kin san ban yi kalaci ba”.

Ina jan sa da labari har ya ci alalan nan da

dama, sannan na rika mika masa naman yana ci, yace,Asiya yanzu ke kika girka mini abincin nan da kanki?? Na ce,

“Yallabai daga ni sai Hadiza muka yi

girkin nan Sannan ya matse lemo cikin kofi ya sha, ya kuma sha ruwan sanyi. Duk abincin nan da ya ci ya kwantar masa da hankali, na lura lallai akwai yar damuwa da take tare da shi da yake kokarin boye mini

Maimakon in dame shi da tambayar abin da

ya dame shi, sai na rika kawo labaran ban dariya ina ba shi; da kuma nuna masa ba ni da wani wanda yafi shi.

Sai kuwa Allah ya taimakan har ya ware

amma idan abin da ya dame shi din ya fado masa à rai ya kan dan yi zugum. Muna cikin hira sai muka ji dawowar Baba. Aliyu ya dube ni ya ce,Baba ne?”

Na ce masa,Eh”Sai ya yi sauri ya dauki babbar rigarsa ta shadda ya mai da, ya tarbi Baba a zaure ya durkusa

har kasa ya gai da shi. Ya ce,Ai jiya mun zo bamu same ka ba an ce kun je dubiyar mara lafiya, ya ya jikin nasa?

Baba ya ce,A’a, jiki ya yi kyau, kai kuma

haka ake yi daga fara neman aure sai ka fara wahalar da kanka? Abin da nake so ka nemi so wajen yariya, amma kada ka dauka wa kanka wahala, mu dai fatanmu Allah ya tabbatar da abin da ya fi zama alheri”

Sai Aliyu yace, “A’a, Baba ba komi wallahi babu maganar wahalarwa”

Baba ya ce, “An ce tare kuke da Suraj?” Ya Ce,

“Eh, amma ya je Funtuwa sai anjima

zai dawo” Baba ya ce,To don Allah kafin ku tafi gobe zan baka sako wajen Alhaji

Sai ya ci gaba da tambayar Aliyu ya ya Alhajin na wajen naku, ka same shi lafiya ko?”

Aliyu ya amsa da murya mai nuna jin dadi da

karamci a kan wanda ake magana da shi.

Baba ya shiga cikin gida, shi kuma Aliyu ya

shigo inda na yi kasake ina sauraron su. Aliyu ya nuna mini murnarsa ta samun suruki mai fara’a da sakin jiki irin na Baba.

Na ce masa,Idan dai don ta Baba ne nan

gaba kai ne abokin shawararsa”

A yayin nan ne muka ji sallamar su Madiza da

Mukhtar, muka amsa masu gaba daya. Bayan mun gaisa na ce,

«Mukhtar mutanen Katsina, ya ya mutan

gida? Ya ce,Asiya mutuniyar Kaduna, ya ya su

Aliyu?”Na yi murmushi na ce,Ga shi nan zaune na da abina”.Mukhtar da Aliyu suka kyalkyale da dariya. Aliyu ya ce,Kamar da gaske, yanzun nan idan na matsa mata da kallo sai ta rufe fuska” Mukhtar ya ce,

“Kai kuwa Aliyu ai ba ta da laifi tun da har tana fadin kai nata ne a gabanka, ni da ka san magana ta da take yi wajen Hadiza, sai da

nayi mata yayin kanta, sannan na samu muna

yar hira’ Na yi sauri na ce,Ni ladiza yau an tona ki, shine kuka tasa ni a gaba kuna yi mini tsiya, yau Allah ya kawo mai rama mini, ni daga yau ka zama yayana Mukhtar”

Ya ce,Kanwata, daga yau idan ina wajen

babu mai kara yankarki. Kai kuma Aliyu na zama surukinka ke nan

Da irin wannan barkwancin muka ci gaba da

hira har aka kira sallar azuhur suka nufi masallacin unguwarmu, ni da Hadiza muka shiga dakina muma muka yi tamu sallar.

Muna gyara kwalliyarmu ne na cewa Hadiza,

«Gaskiya Mukhtar ya amsa sunansa, yana da kyau Hadiza. Sai na ga yana da yanayin Yaya Aminu, amma Yaya Aminu zai fi shi fari, shi kuma Mukhtar ya fi Aminu manyan ido

Ta ce,Ai na gaya miki Mukhtar babu dama

fagen kyau, ke ma Aliyu ba daga baya ba”

Na ce,Ai na fi Aliyu kyau”.Hadiza ta ce,

“Sai ki gayawa wanda bai sanki ba

Hmmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE