ALLURA CIKIN RUWA BOOK 1 CHAPTER 25 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA

ALLURA CIKIN RUWA BOOK 1 CHAPTER 25 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA

 

 

Na ce.”Ke dai kina daurewa Aliyu gindi da

yawa Hadiza”A tsakar gida Inna ta ce,

“Ga fura Can an dama ko za ki kai musu?”

Muka ce,To Inna”Na ci gaba da cewa,

“Inna ko za ki sanya a yiwa Aliyu fura ya tafi da ita Kaduna, na ga kullum sai ya sha fura”

Ta ce,To bari in ba Zainabu geron ta kai wa

Tambaya mai fura tun yanzu, kin ga gobe sai ta hada masa Nace,

“Eh, lalle kam dakan fura sai ta

Tambaya Muka yi sallama muka shigar da wani abincin da fura, suka yi dariya suka ce,

“Gaskiya cikinsu a cike yake tun da basu dade da cin abinci ba”.Da na ga ba za su kara cin abincin ba, sai na ba da shawara da muje cikin makarantarmu mu buga Kwallon tebur, tunda tebur din yana karkashin wata makekiyar cediya ne, kuma maigadi ba zai hana mu

shiga ba, musamman ganin babu dalibai.

Kowanne daga cikinmu ya yi na,am da

wannan shawarar tawa. Muka sami maigadi muka gai da shi, sannan muka wuce. Haka muka dinga wasan Kwallon tebur, nan take na gane Aliyu har yafi Yayana iyawa kadan. Bayan mun gaji da wasa sai a ga Mukhtar ya

kamo hannun Hadiza sun nufi gindin wata darbejiya zasu zauna, sai Aliyu yà langabar da kansa ya dubeni ya ce,Kin gani ko? Na yi murmushi na juya na fara tafiya zuwa gindin wata bishiya, na zauna Aliyu ya biyo ni a

baya a hankali yazo ya zauna daf da inda nake zaune, ya dube ni ya ce,

“Asiya ko in tashi?” Na ce,A’a A. haka dai muna ta hira ban san lokacin da

Aliyu ya dora kansa bisa cinyata ba, na rika shafa masa sumarsa har na kai ga kitsawa a hankali, sai barci ya dauke shi Na yi tagumi ina kallon sa ba tare da ina motsawa ba gudun kada in takura masa jin dadin barcinsa, haka ya sami barci tsawon minti ashirin da

bakwai, da ya farka na warware masa kitso, na rika shafa masa sumarsa ya zuwa baya.

Sannan su Hadiza suka zo, ya yi sauri ya tashi

ba tare da sun gane irin zaman da muka yi ba.

Mukhtar ya ce,Surukina ai gara mu tafi

saboda karfe biyar zan bar ga rin nan

Muka tashi muka nufi mota, a nan Mukhtar

ya bude aljihun motarsa ya fiddo kum ya miko wa Aliyu, ya ce,Gara ka taje sumarka kada irin su Hadiza su yi maka dariya Sai na yi sauri na rufe fuskata, ita kuma tace,

“Asiya yar duniya, wa za ki rufewa fuska, yayan naki ai ga shi ya fara dago ki ya kuma fara tona ki”Mukhtar ya ce,Wallahi ki yi shiru ko in tona nakii asirin Hadiza Ta yi sauri ta sunkuyar da kai kasa ba ta kara

cewa uffan ba.Bayan sun yi sallar la asar, da karfe biyar saura kwata muka shiga falon Inna hafsatu suka gaisa da Aliyu da Mukhtar, biyar da rabi suka raka Mukhtar gindin motarsa ya nufi Katsina, shi kuma Aliyu shida daidai Baba Suraj yaz0 suka shiga gari.Da safiyar Lahadi mahaifina ya sayo kaji guda ashirin, inda Yusuf da abokansa suka zauna suka fige su tsab, sannan aka sayi manshanu mai yawa. Inna ta zauna ta toye shi da kyau, ga kindirmo

an saya jarka biyu. Da misalin sha biyu da rabi na rana su Aliyu da Baba Suraj

suka ZO sallama zasu wuce, mahaifina ya ba su kaji ya ce, su dauki biyar-biyar

su kai wa su Mama Inki goma tare da manshanu da nono jarka guda, fura kuma da jarkar nono guda na Aliyu da Suraj’ne.

Inna ta dake kuka da kubewa ta zuba a cikin

gwangwani, ta ce na Mama Inki ne. haka dai aka hada musu tsarabar kauye rankatakam

muka yi sallama da Aliyu, inda ya ce sai ya dawo sati mai zuwa sallama tunda wannan satin muke komawa makaranta. Ya kawo naira dari biyu ya bani na amsa da kyar, Baba Suraj ya ba ni naira dari.Ranar Litinin mahaifiyata ta dibar wa su Inna Tafsatu kayan da Aliyu ya kawo, ni kuma na hada musu da irin tsarabar dana yiwa Hadiza. A daren wannan rana ne Inna hafsatu taZO godiya, har na shiga daki na barsu suna hira ita da mahaifiyata.

Bayan na yi zurfi cikin tunanin Aliyu, sai

karaf cikin kunnena, na ji Inna Hafsatu na cewa,Ai dazun na ga Aliyun sun shiga sun gai dani, yaro mai kunya, daman ya fita daban cikin ya’ yan gidansu”Na yi tunani na ce,

“Lalle su Inna ba su san Aliyu ba, a gabansu yake nuna kunya, amma da zasu ga yadda nake fama da shi da sun tausaya mini”

Na yi murmushi na sake juyawa gefe guda.

Sai na ji can cikin barci yana nema ya kwashe ni, Inna Hafsatu tana cewa,Wallahi Aisha kullum in na yi sallah sai na roki Ubangiji Allah yasa Asiya ta zama rabon Bature, to sai yau na ga gashi har Asiya ta sami mai so wanda a bisa dukkan alamu ita ma tana son sa Kwarai ainun Mahaifiyata tace,Ban da abinki Hafsatu, aida wuya Aminu yace yana son Uwani saboda ya dauke ta tamkar Hadiza ne Taci gaba da cewa,Lalle kam Uwani na son

wannan yaro, ni abin har mamaki ya rika bani, idan an ce ga shi yazo babu ko irin dan kawaicin nan,yanzu kin ga ta yi zumbur ta fita babu kuma ko irin jan ajin nan na mata”

Inna Hafsatu ta ce,Wallahi duk haka suke,

rannan sai da na zazzagi Hadiza, na ce shashashar banza ya mai da ke sakarya, in ya gane kin mutu kansa cikin ruwan sanyi zai dinga juyaki , sannan ta rika dan ragewa. Ni wallahi Aisha lamarin Bature na ba ni toro, tsorona Allah tsorona kada dan nan yazo mana da mata jar fata” Sai na ji Inna ta yi

*yar dariya, ta ce,Haba Hafsatu ki daina kawo irin wannan tunanin, ki dai ci gaba da yi masa addu’a Allah ya dawo da shi lafiya.Amma Aminu au yana da kaifin hankali mawuyaci

ne yayi wannan sakarcin Ai ma duk takardun da yake rubutowa babu inda yake maganar aure,sai dai ya ce a yi masa addu’a Allah ya sa a dace da abin da aka je nema. Ki daina damun kanki in Allah ya yarda a nan zai yi

aure kuma ‘yar mutunci Sai kuma

Inna Hafsatu ta koma maganar

Mukhtar, ta ce,Ya matsa zai kawo kaya amma na

Hmmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE