ALLURA CIKIN RUWA BOOK 1 CHAPTER 29 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA
ALLURA CIKIN RUWA BOOK 1 CHAPTER 29 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA
Mu duka ‘yan zafi ne a wajen harkar karatu,
saboda haka sai mu kashe lokaci mai tsawo muna
yiwa juna matashiya. Misali a nan, a kowane darasi za a sanya daya daga cikinmu ta karanta, sannan tayi bayani a kan abin da ta karanta da yadda ta fahimci. abin. Bayan ta gama sai kowace daga cikinmu ta kara bayani ko ta tambayi abin da ba ta gane ba, sai mun tabbatar kowacce daga cikinmu ta gane sannan
mu wuce wannan darasi mu shiga wani sabo.
Ta,irin wannan: hanyar muka cimma burinmu,
ba‹mu taba yadda: mu zauna, muna, zurara karatu ba tareda Fahimtar komai a ciki ba
Acikin-wannan sito da muka mai da shi
dakin mabuyar-karatu, mun Kawala shi da abubuwan da sukan-taimakamana a ashen fannin karatunmu, Na aiki wata „mata mai daikin abincin makarahtarmu wadda ke zuwa daga cikin gari, kuma gidansu baya da nisanzuwa gidanmu, ta amso, mini sabon tulu muka ajeshi a wannan sito sbd mu dinga shan ruwa ba tare da saimun tashi munje nema a wani wuri ba haka ta amso amso mana tabarmi guda biyu, bayan
tebur da kujeru da mukasanya, idan mun gaji bisa
kujera mu kan kwanta bisa tabarma mu ci gaba da nazarin karatunmu, Sannan kuma mun yi amfani da loka din dake jikin teburanmu don aje abincimu.kamar su biskit da cakulet da konfeles da dai yan abubuwan Tsotse-tsotsen motsa baki.
A daidai bangon da kowace daga cikinmu ke
zaune bisa kujerar kavalunlu ta lika jadawali da ke
nuna lokutan jarrabawarta. Daga nan muke dage
dantse, muka ci gaba da karatu ba ji ba gani, muka yi shiri sosai don tarbar jarrabawar mock ta share fage ga babbar jarrabawar fita,
A wannan lokaci ba mu da komi daga karatu
sai nafiloli muna neman sa’a daga wajen
Ubangijinmu. Muna cikin haka time-table ya fito na jarrabawarmu ta mock, jarrabawar ta farko da za mu fara yi ita ce ta fannin Tarihi
Muka shiga aji muka zazzauna, bayan an bamu takardun tambayoyin kowace ta dukufa wajen
duba abin da aka tambaya. Da na gama karantawa sai na daga kai na dubi Rabi ‘yar mutan Karmiya nayi mata murmushi.
Abin da yasa na juya na dube ta shi ne, daga
tambaya ta daya har zuwa ta uku ita ce ta yi mana bayaninsu. Sannan nayi musu tambaya a kan bayanin da ta bayar, to cikin ikon Allah sai gasu su ne a farko, sauran kuma mun san su kamar yunwar cikinmu. Haka muka rinka samun kowace jarrabawa cikin sauki. Idan ka ji daliba tace, jarrabawa ba ta yi wuya ba, to ta san abin da ta taka. Ko da yake ba a cewa babu wuya, sai dai a ce an riga an sha wuya wajen yawaita bitar da muka yi, idan anzo wajen jarrabawa sai mutum ya sami komi kamar wasa
Bayan mun gama jarrabawa da kwana uku aka bamu hutu na sati biyu kacal, a inda muka isa gida da ramuwar barci a kanmu. Ranar da muka sami kwana hiyu da zuwa hutu
sai ga su hajaru da direban gidan su Mama Inki sun zo tafiya da ni Kaduna, a nan muka yi tayin ta dasu, a inda na nuna musu gaskiya su yi hakuri ba zan sami zuwa ba saboda akwai karatu
a tattare dani, musamman ga shi da mun koma makaranta da sati shida zamu fara jarrabawa ta fita.Suka matsa wa mahaifina ya tura ni in tafi, sai
yace Su yi hakuri ran da na gama jarrahawa insha
Allah suna gani na Da Kyar dai suka hakura dirceba ya mai da su Kaduna.
Lokacin da muka sami kwana hudu da samun
hutu sai muka fara zuwa aikin karatu na cikin gari.
Ba ni mantawa ranar wata Alhamis da la’asar
sakaliya zamu je Reading room karatu da ni da
Hadiza, mun kusa isa ke nan sai muka hadu da wani mutum a cikin mota Marsandi mai kirar kulba, kalar ta fara ce sol. Ya sha gabanmu amma muka Ki yarda mu tsaya har muka is dakin karatu muka shiga. Mun sauna ke nan sai ga shi ya shigo, yana sanye da riga yar shara da dogon wando na farar shadda. Mutumin dai dogo ne baki mai kyan Kira, yana da dogon hanci da idanuwa wadanda su ba kanana ba
kuma basu da girma ba, kadaran-kadahan.
A tsakanin hancinsa da labbansa na sama akwai gashi wanda ya yiwa hancin nasa tsari.
Ya sami kujera ya zauna kusa damu yace
“Haba yanmata ana yi muku magana amma kun ki ku tsya? Duk wanda ya ga shigar da kukayi yasan Yanmata ne ba matan aure ba, saboda haka ai ya yan manya ba a san su da raina mutane ba” Sai Hadiza tace Yanzu Alhaji wan irin raini muka yi maka? Mu tsaya muna magana da kai bisa titi, ina ganin ai ba mutuncinka ba ne, haka mu ma ba mutuncinmu ba ne
Ya yi ajiyar zuciya ya ce,Lalle yaran nan
kuna da kaifin hankali, kin san namiji idan ya ga mace yana, so bai damu da ya tsaya a gaban ko wane ne ya yi mata magana ba. A kan yi haka ne gudun kada ta bace masa, bai sani ba ko ya sake ganin ta ko ba zai sake saduwa da ita ba, inda kuka fi mu ke nan ku mata kun iya kannewa, ku jere ko mene ne a zuciyarku”Ya dube ni ya yi murmushi, cikin ikon Allah ban san yadda
Akai na maida masa Da martanin
murmushinsa. Ba Nan da nan sai ya ji dadì, ya gyara zama ya dubi Hadiza yace
‘Ina sunan malamar?
Hmmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe