ALLURA CIKIN RUWA BOOK 1 CHAPTER 31 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA
ALLURA CIKIN RUWA BOOK 1 CHAPTER 31 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA
Sai nayi sama da idona sama ina kallon farin
Wata wanda ya haske mu, ya rinka sanya tufafin da Ibrahim ya sanya suna daukar ido, yayin da atamfar da ke jikina ta rinka sheki. Yace
“Kin ga farin wata ya Kara sanya idanuwanki suna walkiya kamar an zuba musu ruwan zamzam, sai walainiya suke yi Na yi sauri na kau da kaina. Can Sai ya ce,Asiya ki daure mana ki yi azumin nan ko guda uku”Na ce,To, insha Allah gobe zan tashi da shi,abin da ya sa ma ban mai da hankali ba shine, yau kwanan mu shida da zuwa hutu, muna makaranta kuma karatu ya yi yawa’saboda muna cikin masu fita bana” Ya ce,Wallahi Asiya na dauka aji, uku kike ban san kin yi nisa haka ba, kin ga da kin gama sai a daura mana aure, mu je Umara cikin watan azumi, bayan sallah kuma mu je aikin Hajji Na yi sauri na bude ido na ce,
“Aure! Gaskiya ka daina yi mini irin wadannan maganganu, saboda ni yanzu na fara karatu, insha Allah nan da wata hudu ina
jami’ar Usman Dan Fodiyi Sokoto, ko ta Ahmadu
Bello Zariya”Ya yi murmushi ya ce,Asiya aure ai ba zai hana zuwa makaranta ba, idan dai don maganar makaranta wallah ina taya ki murna kuma zan taimaka daidai gwargwado. Yanzu wa ke son ya danne wa matansa yanci? Saidai idan matar ba ta da sha awar karatu ne; zanyi zaaman jiran ki. har ki gama jami;a idan dai har zanzo inda kike kuma ki fito bahu damuwa Na yi shiru,. Sai can ya ce,Asiya zan ba ki dan takaitaccen tarihina, Sai can ya ce Asiya Ni Ibrahim Tsiga mutumin Tsiga ne, an haife ni a cikin wannan kauye, na, tashi ba uba, yanzu haka yan uwana suna kira. na, ne da audi Saboda, ina ciki ubana
ya. rasu, an yaye ni na yi wayo da lokacin shiga
makaranta ya yi sai kanin tsohona Malam hamza ya amshe-ni, a hannunsa nayi wayo harna gama
sakandire, Bayan na, nemi aiki sai rannan kwatsam aka fara neman dalibai a jami,ar London,nan da nan na cika fom, nayi sa’a sunana na cikin wadanda aka dauka, muka yi shiri muka tafi. Cikin shekara biyar na kammala na dawo gida Najeriya, daman na karanto-fannin akanta ne. An fara aje ni aiki a Funtuwa a Area council a matsayin mataimakin Jami ‘in Kudi. Na fara aiki da shekara guda sai Kanin tsohona yace mini amininsa Malam Isa ya bani yarsa mai suna Habiha.Kaina ya daure sahoda a lokacin ban yi niyyar aure ba, kuma yadda nake girmama Kanin mahaifina sai na ga ba zan iya musa masa ba. Na shirya na je gidan su habiha aka kira mini ita. Na ga dai ga yarinya har yarinya, sai dai ba irin
macen da nake tunanin aure ba, amma ga shi kuma na yaba da hankalinta, ga kuma karamcin da ubanta ya yi mini. Domin wanda ya dubi nutsuwarka da hankalinka har ya ce ya baka “yarsa kin ga ba ka da kamar sa, sai na nuna musu na amince.Bayan an yi biki na sami Malam Hamza na shaida masa na yi godiya da wannan kyauta da suka yi mini. Na nuna musu ra’ayin bani da sha’awar auren mata biyu, sai dai
duk da haka saboda cudanyar rayuwa, nan gaba idan na sami wadda nake so zan aura
in hadasu su biyu. Ya ce,Wannan ai babu komi idan dai ba ka ci amanar ta ba, ai namiji mijin mace hudu ne” Haka na dukufa koya mata karatu da rubutu, yanzu haka duk da ba ta yi makaranta ba ko Baturen England za ta yi Turanci da shi.
“Ya yanmu uku da ita, da Zainab wato sunan
mahaifiyata wadda ta rasu ina London, sai Zulaihatu, sannan karamarsu Zubaida. Tunda na auri Habiba babu soyayya, amma kaifin hankalinta da son ta gyara mini rai a koda yaushe, yanzu ta nema wa kanta son a zuciyata.
Daga Funtuwa aka mai da ni Katsina, daga nan
sai nan Malumfashi. Yanzu shekara ta talatin da biyar,Habiba kuma ashirin da daya” Bayan ya gama bani labarinsa, sai na nisa na
daga kai muka yi ido hudu da shi, sai muka yiwa juna dariya. Sannan na ce,Kai kuwa don Allah yadda kuke da Habiba me zai sanya ka yi mata kishiya? Kuna zaman ku na fahimtar juna haka kawai ka yamutsa wa kanka gida” Yace,
“Asiya an sha ba ni yanmata haka kuma
‘yanmata sun sha aiko mini suna sona, amma ban taba kulawa ba, abin da yasa nake son auren ki saboda mashin sonki ya gifta mini cikin zuciyata, tun da na ganku dazu sai kawai na ji wani abu ya ratsa mini cikin jikina. Saboda haka ki yardan so da kauna ya sanya ni neman auren ki”
Muna cikin magana sai na hango mahaifina ya
shiga gida, na dubi Ibrahim sai ya yi dariya, ya ce,
“Dalilin ke nan na ki tsayawa kofar gidan ku, daman muna yar kunya da shi a Ofis ashe kila daman Allah ya yi nufin zai zama surukina ne”.
Na yi murmushi na ce,Ibrahim ka cika saurin
kaso da gamewa” Sai ya yi mini wani irin kallo mai tsananin saukar da sako cikin jiki, ya ce, “Asiya kin fi kowa iya kiran sunana”Na ce,
“Har Habiba taka?”Sai ya yi murmushi ya ce,
“Kema ai ta wace Asiya”Sai na yi sauri na duba agogon hannuna da yake akwai hasken farin wata, na ce,Wai! Wai! Dare ya yi
har goma da kwata, gara ka je gida kada Habiba ta kasa barci” Sai ya Kyalkyale da wata irin dariya ya ce,Saidai in ke ce za ki kasa barci randa na aure ki kika ga na dade ban dawo ba, amma Habiba hakuri ne da ita ba dan kadan ba”
Ya ci gaba da cewa,Kada ki manta da azumin
da za ki dauka Na ce,A’a, ba zan manta ba da yardar Allah”Ya fiddo dan karamin katinsa ya miko mini wanda ke kunshe da adireshinsa na ofis da na gidansa, muka yi sallama ya tafi na koma gda. Na sami mahaifina da shi da Inna zaune, Baba ya ce,Ina na fito?” Na shaida masa, na kuma mika masa wannan kati na shiga dakina.
Na dade da shiga daki har na kwanta da misalin
sha biyu lokacin gidan talabijin suke rufewa, sai na ji mahaifina na cewa Sha’anin “ya mace yana da ban tsoro, yanzu kin ga ta fidda wanda take so, shi kuma wannan yaron Alhaji Ibrahim da ya zo wajenta,ma’aikaci ne a ma’aikatarmu, yana daya daga cikin yaran da ke ba ni girma a ofis.
Ke in gaya miki gaskiya kamar ubansa ya daukeni
Yaro ne mai muhimmanci to yanzu yaya zanyi
Hmmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe