ALLURA CIKIN RUWA BOOK 1 CHAPTER 33 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA

ALLURA CIKIN RUWA BOOK 1 CHAPTER 33 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA

 

 

Ta ce, “Ni dai Uwani akwai ni da gudun rigima,

har yaushe za mu zauna muna amsar dukiyar jama’a a kan ranki ke kadai, yanka ki za mu yi, muba komi Gare mu ba, gaskiya gara Malam ya yi maganin abin tun da wuri a yiwa hanci tulka”

Nace To Inna ya ya zan yi da shi, wallahi ki

tambay; Hadiza babu yadda ban yi ha na nuna masa ina da wanda zan aura amma ya ki ya fahimta, kuma na ga bai dace ba n yi wa Aliyu magana ya aiko gida, shine ya kamata ya yi mani maganar. Amma idan kunga ya dace in yi masa to, idan ya z0 sai in yi masa Ta ce A kul naji wannan maganar ta fito daga bakinki, kamar ana neman kai da ke, duk lokacin da yaga ya dace sun aiko, yanzu haka wata hidimar ce ta tsai

da shi”‘A wanna zamanin damina ta soma daukewa yayin da shi kuma sanyi bai kunno kai ba, ana dan buga zafi-zafi jefi-jefi, irin zafin da ake kira zafin dawa. A wannan rana ta ranar Juma’a an samu dan ban iska, saboda tun da misalin hiyar da rabi hadari ya hadu kamar za a yi ruwa, amma ina, sai hadarin nan ya

kada ya yi yamma, aka bar mana iska mai sanyi ya sa da daddare aka rinka yin dan sanyi-sanyi, amma ba mai hana sakewa ba, sai dai ya sanya dadin barci.Haka na fito ina takawa dai-dai iska na kada mini ygalena mai shara-shara, yayin nan kuma Ibrahim na cikin mota zaune inda ya fiddo kafarsa daya waje, dayar kuma na cikin mota. Ga kaset din wakar Dan-Kwairo na tashi a cikin wakar Hassan Katsina. Ciroman Da Ibrahim ya ga na kusan isowa inda yake, sai ya danna fitilar motarsa ya hasko ni. Na yi sauri na sa

habar galena na rufe fuskata, ya yi sauri ya kashe fitilar motar. Na isa na yi masa sallama, sannan muka gaisa. Sai ya ce,In zaga in zauna bisa kujerar da ke kusa da shi”. Sai na yi dan jinkiri, sannan na je na bude na zauna kamar yadda shi ma ya zauna. Ya dan rage karar rediyon

sannan yace

“Sarauniyar mata yau dai tafiyar ta ki har tafi ta jiya yanga Sai na ce,Ibrahim ba yanga nake yi ba, wallahi yau da kyar na fito saboda azumin nan ya gajiyar dani. har na sanya rigar barci sai ga shi ka aiko Ya ce,Asiya raguwa, duk yau na san yini kika

yi a kwance, amma shine kike taliya kamar za ki kwanta a kasa kina rausaya kamar iska na kada reshe”Na yi murmushi na sanya hannu wajen aljihun motarsa ina wasa, sai na dan waiwaya kadan na kalle shi, na ce, “Af? Ya ya su Zubaida da Mamansu? Ya yi dariya ya ce, Suna nan lafiya, sunce suna gai da ke Na cè,A’a, ka dai ari bakinsu kaci musu albasa, amma ni ba su sanni ba’ Yace

“Ai sun kusan sanin naki, ba ki san wani abu ba, Habiba ta saba ba ni fita yawon dare, to jiya na

filo yau ma taga na fito, shine abin ya daure mata

kai, yanzu da ta ga zan fito sai ta ce mini,

“Baban Momy ko in shirya in raka ka ne?”

Ta kuma ci gaba da fadin cewa, “Na yi zaton ko

an samo mini kanwa ne” wallahi sai abin ya daure mini Kai na ga kamar wani ya gaya mata halin da nake ciki. Sai na gyara zama na kara fuskantarsa sosai na sanya hannu na yi tagumi, nace masa,

“To kai ya ka ba ta amsa?” Ya yi murmushi ya ce,

“Abin da na ce mata,Allah ya biye bakinki ta zamanto kanwar taki”. Sai tace,In dan kara mata haske don Allah” Na Ce,Ta yi hakuri sai nan gaba. Kin ji yadda muka yi da ita, amma

ina ganin gobe zan gaya mata tsakanina da ke gudun kada ta ji a bakin ‘yan hana ruwa gudu”

Na ce, Wai Ibrahim haka ake yi, na gaya maka

akwai wanda na yiwa alkawari, amma kana nema ka sanya ni cikin wani hali. Yanzu ka ga kayan da ka aiko mini dazun, wallahi mahaifiyata ta nuna mini ba ta ji dadi ba, saboda muna gudun rigima nan gaba. Don Allah Ibrahim ka daina yi mini

irin wadannan hidimomin, kuma don Allah kada ka dagula mini lissafi”.Sai ya yi shiru har na zuwa tsawon lokaci, sannan ya ce,

“Asiya ni ba zan dagula miki lissafi ba, amma idan

har reshe ya juye da mujiya, ina murnar rushewar lissafinki, kuma Asiya idan har kin san baki son gani na Ina zuwa wajen ki, to ki gaya mini.

Ni dai abin da nafi so ki Kyale ni ina zuwa muna

hira, shi sha’anin aure ai na Allah ne, kada ki zaafa wa kanki, Allah kadai ya san mijinki.Saboda haka ba ni nan kawai ba, duk wanda ya zo wajenki ki saurare shi ba a san inda rana za ta fadi ba Baki ji kirarin da ake yi muku bane, ana cewa sambaleliyar budurwa kamar ki”

Na girgiza kai na yi murmushi. Ya karasa zancensa da cewa,Ai irin ku ake nufi da

ALLURA CIKIN RUWA mai rabo ka dauka. Yanzu duk wanda yake neman ki lalube zai yi cikin duba, wanda Allah ya bai wa sai ya ji sulub ya café ki, muna nan muna rokon Rabbana ya sa mu za mu ca beki” Ya ci gaba da cewa,Ya ya ban ji kin ce amin ba Na ce,Ibrahim ba ga shi nan kai ka ce ba?”Na dube shi na yi murmushi na ce,

“Allah dai ya tabbatar da abin da zai zama alheri a gare mu baki daya, amin, ka san mutum sai ya so abu idan ba alheri ne gare shi ba, sai ka ga Allah ya hana shi. To idan mutum yana yawan addu’à sai ka ga Allah ya canza masa da abin da

yafi zama alheri a gare shi, to shine ake cewa wani hani ga Allah baiwa ne’ Ya yi dariya ya ce,

“Eh, haka abin ya ke kamantowa, amma ni ba ki san wani abu ba Asiya, wallahi jiya har nafila na yi na roki Ubangiji ya ba ni ke ko da ido a rufe

Na ce,Ka yi kuskure Ibrahim, ina amfanin inzo

in zama maka sharri, Allah ya kyauta

Ya ce,Insha Allah akwai alheri a tare da duk

wanda Allah ya baiwa ke” Nace Wallah maza al’amarinku na da ban mamaki, idan kun so mace kamar danda yaso fitowa cikin mahaitiyarsa, dan kun sanya mana kahon zuka na Kiyayya, abin bai ko da dadin ba da labari. Saboda haka

ni dai kallon ku nake kurum, Allah ya yi mini zabin mali alheri kawai” Ya ce,Asiya sai ka ce goyon kakanni don iya magana, idan kina magana har mamaki nake yi, ko da yake halitta ce iya magana

Bayan na duba agogon jikin motarsa naCe,

“Ibrahim gara ka je gida cikin iyalinka ni ma in je in kwanta ko?” Ya yi dariya ya ce,Koke kika rada mini sunan nan kin ci a yaba miki don tsananin iya kiran sunan, kada ki so ki ji irin dadin da ke kama ni cikin raina idan kika kira sunana. Wai da kika ce in je cikin iyalina, ai ke ma rabin iyalina ce, saboda haka ba aibu don na kashe lokaci

mai tsawo da amarya ta Da irin wadannan surutan muka yi sallama, muka rabu a kan gobe Asabar za shi Katsina, idan ya dawo da

wuri zan gan shi, idan bai dawo ba in sanya ido Lahadi.

Hmmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE