ALLURA CIKIN RUWA BOOK 1 CHAPTER 35 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA

ALLURA CIKIN RUWA BOOK 1 CHAPTER 35 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA

 

 

Ya co, “Ai na san yadda zan ce masa, ai ga shi can tare da mutane a Kofar gida zan je yanzu in yi masa bayani” Da safe ne Zainab ke ce mini “Yaya Asiya sakon ki na nan Karkashin gadonki jiya Alhaji Ibrahim ya aiko lokacin kina wajen Aliyu, shi ne na fita ya ce mini ga shi in ba ki har da wasika ya rubuta, sai dai yace kada in ba ki a gaban Aliyu, in bari sai in kin shigo

“gida” Na shiga na fiddo kayan da ya kawo na ga dabino ne da kilishi da aya da lemo da ayaba, sannan na duba dan Karamin katinsa, a baya ya yi rubutu kamar haka:

Ranki ya dade, Da faían kin yi buda baki lafiya, na zo don mau sha hira, amma na samu mutanen Kaduna sun riga ni, saboda haka sai gobe, a gai da mutan gida Mai Kaunarki, Ibrahim Tsiga.

Na karanta na yi murmushi, nace Allah sarki

Ibrahim shi dai mutum ne mai saurin fahimta, ga kuma rashin fushi. Na zauna na shirya masa maganganu masu dadi da fahimtarwa, na ce idan ya zo zainab ta bashi.

Da misalin sha biyu saura kwata da ni da

Madiza da Aliyu da Umar muka bar Malumfashi, a kan hanyarmu ta zuwa Kaduna, na yi kokarin nuna wa Aliyu Bacin raina a kan rashin daukar wani mataki a bisa. maganar aurenmu, duk wata magana ta barkwanci ko makamancin haka, idan ya yi mini sai in dauke kaina ko kuma in amsa masa a dakile, har dai na lura da Hadiza ta fara bata rai da ni. Haka shi ma Aliyu tun yana kallo na ta madubi yana yi mini murmushi ina dauke kaina har sai da ya rika yawaita kallo na fuskarsa a murtuke, kuma ya kasa dauke idonsa a kaina, har Hadiza ta ce, “Kina da biro a jakar ki?” Na ce”Eh”. Na mika mata. Sai ta dan rubuto ‘yar wasika ta miko mini, ga abin da ta rubuta.

Asiya Don Allah ki rufa asini ki dan

rangwantawa Aliyu ko murmushinki ya gani, kada ki sa mu yi hatsari. Hadiza Mukhtar: Da na karanta sai na dubo ta. na yi murmushi, ita kuwa sai ta kau da kai, na sunkuyar da kaina kasa, sannan zuwa wani lokaci na daga kai na dubi mudubin motar Aliyu, sai muka yi ido hudu da shi, na ga idanuwansa sun. yi jawur kamar garwashin wuta, ya daure fuska. Sai na. Kara kashe ido na yi masa sansanyar murmushi, sai nan. da nan ya yi ajiyar ruciya ya ja dogon lumfashi ya mai do mini martanin murmushina.. A lokacin ne Umar yace”Na. fara jin yuwa Aliyu’

Sai muka kyalkyale da dariya da ni da Hadiza, na ce Kai wannan maigida da raki kake, idan azumi ya zo ya ya kake yi”.Sai ya ce, “Kin san kuwa azumi bakwai na yi cikin wannan watan azumin tso faffi”. Nace “Lalle ka yi kokari” Na ci gaba da cewa, “Aliyu, mu tsaya a Zaria ya ci abinci”

Sai ya ce, “Ke rabu da shi so ya ke mu Bata lokaci kawai Na dai matsa masa, har saida muka iso Zariya, Muka karya kana muka isa Tudun Wada, ya taka birkin motarsa a gidan cin abincin Shagalinku muka haye bisa bene. Aliyu ya yi odar sakwarar doya da farfesun kifi, shi kuma Umar ya nemi tuwon shinkafa. da farfesun bindin sa, ni da Hadiza kuwa farfesun kaji da salad Mun isa Kofar gidan Aliyu da karfe hudu, a nan

na ce, “Aliyu ina zaton sai kun aje mu gidan su Mama Inki tukunna ku iso gida?”

Ya ce, “Na ce miki ba zan kai ku ba ne, ke dai komi sai kin kawo wani sanabe, ko ni mai satar

kawuna ne, ina ganin kanki ba zai yi tsada ba gara ma na Hadiza Kila ya yi”

Muka kyalkyale da dariya. Muna shiga falo sai .na ga komi ya canza mini, saboda hotuna na ne inda

duk ka wulkita manya-manya kamar ka kira ni in

amsa.Ni da Hadiza bayan mun yi sallar la’asar mun* zanta kan wannan magana, amma babu wanda ta gano~bakin zaren.

Bayan mun yi sallar magariba ya yi wanka ya

dauke mu zuwa gidan su Mama Inki, haba maganar murna da tsalle wajen su Hajaru da su Maryam abin sai ka ce sabuwar haihuwa aka yi a gidan. Haka suka yayyabe mu a dakin Mama Inki,

wanda ya sa Alhaji ya shigo har dakin Mama don yaga abin da ake yi wa murna. A nan muka samu muka gai da shi. Ya ce, “Ina fatan za ku kwana biyu”Na ce, “A’a, ranar Laraba za mu koma saboda hutunmu ya kare” Aka gyara mana daki, muka yi wanka muka ci abinci, muna zaune a dakin da a kai mana masauki. Hadiza tace”Asiya wanna gida ya shiryu, ga masu gidan har da ‘ya’ yan gidan masu karamci, idan ka zo wannan gida ba ka so ka bar shi ba”

Ta ci gaba da cowa, “Asiya ya kamata ki canza irin halin da kike nunawa Aliyu, domin ba ki san irin shirin da yake yi ba”Na ce, “Hadiza ai kin fi kowa sanin halin da nake ciki, kin ga ya kyauta ya yi shiru babu wata magana mai karfi, kina kallon yadda nake. fama da mutane, kin san halin iyayenmu Hausawa ba su cika son irin kowanne ya kira ka babu wata magana mai Karfi ba’

A daidai wannan lokaci su Hajaru da Ummi suka shigo da kaset din Video a hannunsu, Hadiza ta fara murna saboda za ta sha kallo, da na ga hankalinsu ya raja’a bisa kallo sai na tashi na je na sami Mama Inki a daki muka fara hira.

A wannan rana ba mu yi barci ba sai wajen karfe daya da rabi. A tsakanin litinin da Talata Aliyu yayi zirga-zirga da mu a cikin garin Kaduna. Haka nan ya yi jagoranci muka ziyarci manyan wurare na soyayya. Na lura da hankalin Aliyu ya tashi ainun, ga tafiyar da ke gabansa ga rashin hadin kan da yake samu daga gare ni, duk wani abu da ya san zai faranta mini rai sai yaga ya yi mini.

Hmmm LABARI fa nata tafiya shin KOYA ZATACI gaba da kayawaaaa kudai kuci gaba da kasancewa damu a koda yaushe

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE