ALLURA CIKIN RUWA BOOK 1 CHAPTER 36 KARSHE BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA

ALLURA CIKIN RUWA BOOK 1 CHAPTER 36 KARSHE BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA

 

 

Sai na yi tunani babu wanda ya san abin da ke

‘boye sai Allah,a duk yadda na so a daura mini aure da Aliyu in tafi jami’a sai Allah ya yi. Saboda haka sai na saki jikina kuma na saki raina, na mai da komi ba komai ba, tun da komi na da lokacinsa. A daren Talata ana gobe zai tafi na nuna wa Aliyu so da yarda yadda ya kamata. Lokacin da ya shigo dakin da muke zaune bayan sun gaisa da yara da su Hadiza, sai suka koma falo, yayin da aka barni ni da shi.

Ya zauna ya yi zugum ya dafe kansa, da gani ka san yana tattare da damuwa. Ya dauki lokaci mai tsawo kafin ya fara mini magana. Ni dai ina zaune ina wasa da abin hannuna, sai na ji yace Asiya na san dole ki damu a kan al ‘amarinmu, amma babu komi tun da muna son juna, kuma iyayenki su ne masu ba da wa, to insha Allah za mu cimma burinmu. Ni kuma yanzu na gode Allah tunda na san na samu karbuwa wajen mahaifinki, saboda haka kamar yadda nake gaya miki tun jiya ki kwantar da hankalinki, idan Allah ya yarda kuma ya dawo dani lafiya za mu yi aure. Na riga na gaya miki na fi ki damuwa”Na daga kai na dube shi, nace Shi ke nan na sha ruwan dangana Aliyu, abin da duk Allah ya yi mai kyau ne, Allah dai ya shiryar da mu bisa abin da ya fi zamar mana alheri, amin Sai yace Na ji dadi tun da na sami kwanciyar hankalinki, a cikin wadannan kwanaki sai yau na sami sanyin zuciyata”

Muka yi murmushi, a bisa kafet yake zaune ni kuma ina zaune bakin gado, sai ya miko mini hannayensa bibbiyu ya ce, “Don Allah Asiya zonan, kin ga kafin mu ga juna za mu dade”

Sai na yi shiru ina tunani ko in nuna masa yadda yake a zuciyata, sai kuma wata zuciyar ta rika. yi mini fada a kul Asiya kada ki biye masa shaidan na nan a tsakani.

Sai na ji ya Kara kiran sunana cikin murya mai ban tausayi, sai na yi tunanin shin ko Aliyu mutuwa zai yi ne a wannan tafiyar, sai kawai na sami kaina na nufi inda Aliyu yake zaune.

Na zauna kusa da shi ya rike hannuna ya hada yatsuna cikin nasa, yayin da na dora kaina bisa kafadarsa. A yayin da na ji dumin jikinsa na sauka bisa jinin jikina, yatsunmu sun hade sun manne, tafukanmu sun Kame gam, kai ka ce domin hannuna aka halicci na Aliyu.

Muna makale a haka Aliyu ya kira ni, “Asiya”

‘Na juyo muka hada ido, sai na lura kwalla ta cika masa ido, bayan na amsa sai yace Ko za ki yarda a daura mana aure mu tafi tare in daga tafiyar sai nan da sati daya, alabashi idan mun dawo sai ki maimaita shekarar karatunki?” Na yi ajiyar zuciya na ce, “Ka daure Aliyu, da wannan shekarar da mai zuwa duk daya ne wajen Allah

Sai ya sake ni ya dafe kansa ya yi shiru, sannan ya ce,Amma abin da ya faru yanzu a tsakaninmu gaskiya zan kasance cikin rudani da Kara tsumuwa da kwadaita a gare ki”

Na ce, “Abin da nake nuna maka ke nan tuntuni, amma sai ka dauka ina nuna maka Kiyayya ne, idan aka dangana sai ka ga komi ya zo daidai idan muna raye Haka na dinga lallashin Aliyu, ya koma kamar yaro Karami, na yi mamaki na san lalle so daban yake, amma idan ba don son da yake yi mini ba, ya ya za ayi wanda za shi wannan kasa har ya damu da ni, idan yan matan ne kyawawa ga su nan, jin dadin rayuwa wa ya fi wannan Kasa. Muka tashi zai tafi gida muka yi sallama mai wuya, har ya kai bakin kofa ina biye da shi a baya, sai na ji ya juyo ya Kara rungumo ni, na dora kaina bisa kirjinsa, sai.na ji hawayensa na diga bisa gashina.Ni ma nan take na ji hawaye sun cika mini ido, da Aliyu ya ji hawayena bisa Kirjinsa sai ya daga kaina sama fuskata na fuskantar tasa, sai na ji harshensa na lashe hawayena, ya rika kokarin neman bakina sai na sulle.  A dole ya hakura ya Kyaleni,na kira Nadia muka raka shi har gindin motarsa. Nan ya tsare ni don in gaya, masa, abin da zai sawo, mini. Nace kasai min”Komi inaso Sai ya ce, “Daman wannan yana cikin lissafinsa”. Na dai rasa yadda zan yin ga shi, yace idan ban fadi ba saidai mu keana a nan kuma suk wani abin sanyawa idan nace sai yace wannan zabinsa ne sai nace to redio mai rikoda Ya ce, Yauwa yanzu na ji magana. Sai ku shirya gobe. Karfe sha daya zanzo ku raka ni filin jirgi, inda za mu tashi ruwa Lagos”. Muka amsa “To, Allah ya kai mu”. Washegari Mama Inki ta ce, “Mu yi hakuri tafiyarmu sai ranar Alhamis, saboda ta bayar mana da dunkuna da za a karbo ranar Laraba” Karfe sha daya daidai Aliyu da Umar suka iso, muka fito muka nufi. filin jirgi. Da muka isa muka kebe ni da Aliyu ya kama mini yatsu sannan ya, yi murmushi, ya dan sassauta yace

«Don Allah Asiya ki rike alkawari, kada ki yarda a yaudare ki a raba mu. Don Allah ki rufa mini asiri kada wani ya rinjaye ki, kinji ko?”Na ce, “Na ji Aliyu, insha Allah babu abin da zai faru a wajena, sai dai idan kai ka ce ka fasa”.Ya ce.:

“To shike nan mun ga wanda zai saba

alkawari tsakanina dake, kuma zan bar wa Umar motata inda duk kike son zuwa ko hidimar zuwa biki wani gari, ko ‘yan’uwanki ko Kawayenki sai ki aiki Yusuf ya shaida. masa ya zo ya kai ki, ko dai wace lalura ta samu ga motar nan na barta saboda ke”Na ce,To zan rinka aika masa”

Muna nan zaune a cikin wani katon falo, muna shan lemu sai mukaji a cikin lasifika ana neman su Aliyu jirginsu ya shirya zai tashi. Na raka shi har suka shige ciki, jirgi ya daga ya tashi sama da su suka ci gaba da tafiya cikin sararin samaniya zuwa Amerika.

Mu hadu a littafi na biyu don jin ci  gaban

Hmmm

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE