ALLURA CIKIN RUWA BOOK 1 CHAPTER 7 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA
ALLURA CIKIN RUWA BOOK 1 CHAPTER 7 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA
muku ba wa zan yi mawa?” Na yi murmushi nace, To Mama Inki” Sai na ga ta fa ra dauko turmin atamfa yar
Holland guda biyu, English guda daya, sai ta dauko wata tsaleliyar shadda mai ruwan Kwai, da wani na gani na fada mai ruwan bula da duwatsu a jikinsa, ta yi ciniki ta biya. Sai muka zagaya wajen yan kayan
barci, ta ce in zabi kala uku. Sannan sai wajen
‘yan takalma, ta sai mini masu rufi kala biyu, sai sukol guda daya da agogon hannu mai zaiba yana walkiya da wata yar karamar jaka baqa mai kyau, duk dai muka yi
ciniki ta biya.
Ni a nawa nufin wadannan kayan ba nawa ba
ne ni kadai, ashe wai duk nawa ne, ban san haka ba sai da muka je wajen masu yi mata dinki. Tace su auna ni ayi mini dunkuna masu kyau. Aka fiddo mini dunkuna
kala-kala na yayi, na zabi kalar da nake so. Ta ce tana so a yi mini nan da kwana uku a gama. Suka ce,Hajiya babu damuwa idan ma gobe da yamma kike so a zo a karba”
tace A’a, a yi a hankali nan da
kwana uku saboda su yi kyau”.
Ba mu isa gida ba rannan sai da karfe biyu da
rabi. Muna shiga ciki muka sami wani saurayi mai suna Suraj, yana zaune yana cin abinci
Mama Inki ta ce, *A’a, maigida ana nan ne?”
Ya yi dariya ya ce,
“Nima ban dade da zuwa ba”. Sai na durkusa na gai da shi, Ya ce,
“Hajiya wannan ba dai Asiya ba ce?” Tace,
“Eh, ita ce ba ka gane ta bane?” Ya ce,
“Kin san rabona da ganinta tun kafin in
tafi Japan, wato lokacin da na taba kai ki Malumfashi Suraj dai Kanin mijin Mama Inki ne, a nan gidan yake zaune kafin ya je karatun shekara biyu Japan, yanzu yana aiki a ma’aikatar jiragen sama, an yi
masa baiko da wata yarinya
‘yar Funtuwa; muna aji daya da ita, amma ita W.T.C Katsina take karatu.
Na shiga dakina na yi sallah na yiwa su Mama
Inki addu ‘a a kan Allah ya saka musu da alheri, amin. An shirya mana abinci muka ci. Yaran gida da ganin Suraj da sabuwar mota suka rufe shi a kan sai ya
kai su yawo a cikinta. Ya ce,
‘”‘To ku shirya da la’asar zan zo in dauke ku”
Muka zauna muna ta kallon video, zuwa can
muka yi wanka. Mama Inki ta, ba ni wasu kaya dinkin Pakistan wandon murgujeje, amma daga kasa an tsuke shi, kayan farare ne sol, tace in sanya ta bani. Lokacin da na sanya na dauki takalma rufaffu bakake na saka, sai ga Hajara ta shigo ta ce,Kai Anti Asiya kada ki daura dan kwali, gaskiya-gyaran
gashinki ya dace da kwalliyar kayanki. Dani ke da koda rabin gashinki Anti Asiya da na more”.
Na yi dariya na duba madubi, na san lalle gyara da sutura su ke fitar da mace. Cikin dan lokaci duk na canza. Hajara ta miko mini gyalen kayana na bude na rufe kaina, amma ana ganin ga shina saboda gyalen,
shara-sharane. Hajara ita ce babba a jerin mata na gidan tana bima Anas, shekarunta ba su kAi sha uku ba. Muka
shirya muka fita inda Suraj da abakinsa Aliyu suke jiran mu. Suraj ya zauna a kujerar mai zaman banza, Aliyu ya ja motar. Suraj ya zauna ya rungume Ummi, ni kuma na rungume Abba, ita Hajara da Maryam suka
zauna haka nan. Tunda muka fara tafiyar nan Aliyu ke satar kallona ta madubi, duk yayin dana daga kaina zan ga idonsa na kaina, ga sauti yana tashi naga samari masu kyau, amma ban taba ganin kamar aliyu ba saurayin da panam keso a cikin kaset din da na kalla jiya idan aka bar ni sai in ce shine, don dai kawai Aliyu na jin Hausa. Na yi tunanin
cewa, da samarin da suke a
Malumfashi kamar Aliyu suke, me zai hana ni son su? Amma na tuna yadda na tsani a ce ana sallama da* Asiya a kofar gida, sai da kuka nake fita.Ni idan Aliyu ya so ni ai na yi miji, me zai hanani auren sa? Sai na ji zuciyata na bugawa a hankali, na daga kaina a hankali na dubi madubin gaban motar, sai
na ga har ya Kara saitinsa sosai a fuskata, muka yi ido hudu da shi nayi sauri na Kara sunkuyar da kaina. A zuciyata na ce Asiya Aliyu, ai ko sunan da
dadi, sai na yi firgigit na dubi su Maryam, na ji kamar sun ji abin da nake fadi.
A haka muka isa Amiziyan fak muka firfito.
‘Abba ya ce in dora shi a kan lilo, su Maryam da Hajara suka nufi kallon ruwa, inda Aliyu da Suraj suka riqe hannun Ummi suka nufi wajen masu sayar da Iyskirim. Lokacin da muka je wajen lilo sai na dora Abba ina tura shi a hankali zuwa wani dan lokaci, sai na ji
zuciyata ta yi min kunci da tunanin Aliyu.
A nan na sauke Abba na sami wani lilo mai
fadi na hau na rungume Abba
muna ta lulawa a hanlali, sai zuwa can na ji an sanya lyiskirim a bakina,
na yi sauri na daga kaina, sai na ga Aliyu tsaye akaina. Na dan kau da fuskata gefe guda ina nuna alamun jin kunya a gare shi. Ya ce,
“Abba amshi naka”
• Ya amsa yana sha. Ya ce, “Asiya baki so in
baki a baki ne?” Na yi shiru ina mai jin kunya, sannan ya dai lura ba zan yarda ya bani ba sai ya miko mini, ya rika tura mu bisa lilo ina mai langabe kaina.
A nan dai na sauka muka jera muna tafiya, inda ya dauki Abba ya saba shi a wuya, muka nemi wajen ciyawa mai lub-lub sai ka ce an shimûda kafet, a nan Aliyu ya zaunar da Abba shi kuma ya dan kishingida,
ni kuma na koma gefe na tsuguna.
Aliyu ya ce, “Ki zauna mana sosai Asiya
Na yi murmushi na dan zauna a takure. Sai
Aliyu ya yi murmushi ya ce,Asiya na ga kina jin
tsorona, bari in tashi muje wajen Suraj Qila idan kingan ni tare dasu kin fi sakin jikinki”
Sai ya mike tsaye ya kama hannun Abba, muka tafi neman su Maryam, muka
same su bisa
Hmmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe