ALLURA CIKIN RUWA BOOK 1 CHAPTER 8 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA

ALLURA CIKIN RUWA BOOK 1 CHAPTER 8 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA

 

 

Aliyu ya yi mini wani kallo mai sauka zuciya, ya dan kanne ido ya ce,Bari ke ma in dora ki

bisa kwalekwale Asiya

Sai na ji gabana yana dar-dar, ina kakabin

dalilin da ya sa Aliyu ke mini shisshigi, ko dai ya gane ina son sane. Nan take na tsai da shawara bari in dake in daina jin kunyarsa da yawa, kila ya rage abin da yake mini

Nace Ni fa Aliyu ba yarinya ba ce

Sal ya fashe da dariya wadda har ya bani mamaki, ya ce,Manya- iyayen yara, yanzu ke za ki gaya mini ke babba co?’

Na yi murmushi na ce,Na ga kana dauka ta

kamar Abba”Ya girgiza kai ya ce, “Ni yadda nake ganinki kamar yarinyar goye

Muna cikin irin wannan maganganu sai Suraj

ya Kwala wa Aliyu kira, ya ce a kawo Abba a saka shi. a cikin Helikwafta, Sai na ji dadì, na yi sauri na sami su Hajara

Mun isa gida ana sallar magariba, suna sauke

mu suka nufi masallacin kusa da gidan su Mama Inki domin su sami jam’i, ni kuwa na yì sauri na shiga dakina don in yi sallah.

Bayan na gama na fara da sunan Allah dari

babu daya, da dukkan addu’o’in da suka saukaka a gare n, na ci gaba da rokon Allah yasa Aliyu shine mijina.

A lokacin da muka yi da masu dinkin kayana

Ya cika duk na Kosa in ga munjè ‘amsa, amma ba mu je da wuri ba sai da la asar sakaliya, da ni da Mama Inkida su hajaru muka je.

Na kara rudewa ainun ganin yadda aka tsara

mini riguna, kuma na ga Mama Inki ta mika musu Katuwar jakar leda da leshi kala biyu a ciki, tace

” A dinka mana zani da riga mai hannu kala bibbiyu dani da su Hajaru. Wani sabon dadi ya Kara kama ni. Da muka dawo gida na shiga daki ina ta kara duba sababbin dinkunan.

Bayan mun gana cin abincin dare a wannan

rana ta Juma’a da misalin karfe tara da kwata, sai ga Suraj, da muka gama gaisawa da shi ya cewa Mama Inki yana son magana da ita suka kebe a wani falo daban.

Zuwa wani loka ci Ummi ta zo ta ce;

« In zo ana kira na”

ina shiga na yi musu sallama, na sami kujera

na kame.Sai Mama Inki ta ce,

“Asiya ina son ki gaya

mini gaskiya, a Malumfashi cikin samarinki kin fidda wanda kike so ne?”

Na yi shiru, kaina ya yi mini gungurun na rasa

yadda zan bullo wa amsar wannan maganar, ga shi Suraj ya tsare ni da ido, gabana yana dakan uku-uku. Sai da Suraj ya ce, “Haba Asiya mufa iyaye ne gare ki, kada ki ji kunya ki gaya mana gaskiya

Na kara sunkuyar da kaina a cikin murya mai

ladabi na ce, “A’a” Suka yi murmushi, sannan Suraj ya ce,

«TO Aliyu ya aiko ni in gaya miki yana cikin masoya, muna fatan za mu sami masauki a zuciyarki” Na yi sauri na hada kaina da gwiwata, ban ce

uffan ba, ya shaida mini mu shirya gobe da wuri za su zo su kai mu yawo. Na ce,

“To, Allah ya kai mu”Ina cikin daki na fiddo sababbin dinkunana ina

tunanin wanne zan fara yiwa Aliyu kwalliya da shi? Sai na tsai da shawara bari in fara saka shadda saboda na ga dinkin ya fi amsata.

Na shiga tunanin idan har Allah ya bani Aliyu

na aura ba karamar sa’a na yi ba ga yadda yake cikakken namiji son kowa kin wanda ya rasa. A bisa alamu, kuma addini ya kama jikinsa Kwarai ainun, na kuma lura mutum me mai son nishadi, sabdoa haka ina ganin idan. mun yi aure za mu yi zaman kut da kut kullum kuma cikin raha, da alamu kuma zai nuna wa mace jin dadì yadda na ga yana

nuna mini a farkon haduwarmu, da irin wannan tunani barci mai dadi ya dauke ni.

Da karfe goma na saliyar Asabar muka shirya

tsab, yadda Mama Inki ta ga na yi kyau, sai ta dauko yan kunnayen zinari da sarka

‘Yan kanana ta bani, tace

“In sanya, idan sun je Ummara ta sayo mini

manya A wannan lokaci su Aliyu suna zaune a falo* suna jiranmu, da muka fito muka gai da su. A wannan marra Suraj shi ke jan motar, yayin da Aliyu ya rike Ummi, dani da Maryam da Hajaru muna gidan baya, nice zaune daidai saitin Aliyu.Sai ya juyo gefena yana ce mini,

“Amarya yaya zaman Kadunan tamu?”

Na ja dan Karamin gyalena mai walkiya na rufe fuskata ba tare da na ce uffan ba.

Ya ce, “Wai ke ba ki gajiya da lullubi, Maryam

amshe gyalen nan?”

Na yi sauri na kara makale jikina, a haka har

muka isa Miziyam wajen aje kayan tarihi. Su Maryam suna biye da Baba Suraj har sun shige, ni kuwa ina takawa a hankali kamar wadda Kwai ya fashe wa a ciki.

Daidai bakin kofar sai Aliyu ya tsaya ya rike

kugu, ya daga kai ya ce,Allah Asiya kamar in aure ki, in ganki a tsakiyar hannuwana, idan na ga kina tafiya kina rausaya gani nake kamar kin gaji Asiya ta farko”

Na yi murmushi yayin da na yi masa wani irin

kallo na nuna amincewa da jin dadin abin da yake fadi, amma kuma kunya ta hanani in taya shi. Na daure na ce, “Aliyu don Allah muje kada su gaji da jiranmu a ciki”

Muka shiga muna kallon kayan mutanen da,

amma duk sanda na daga kaina idon Aliyu na bisa kaina, ga ‘yar karamar wushiryarsa ko da yaushe yana yi mini murmushi.

Bayan mun bar Mizyam sai Suraj ya ce,

“Gara mu tsaya a Hamdala Hotel mu ci abinci”

Sai gabana ya fara dar-dar, na ga ni kuwa ya yazan yi na ci abinci a gaban jama’a kuma ga Aliyu na kallo na. da muka isa na ce,

“Ai ni atabau ba zan iya shiga ba«

Suraj ya ce,Ba ga su Hajara ba “

A zuciyata na ce,

“Su Hajaru babu mai tsare su da kallo, kuma kallon da biyu ake mini”A nan dai aka dinga ban magana, amma Aliyu

bai ce uffan ba, har dai ya kare ya ce,

*Suraj ku ci abincinku, nima na zauna a mota , daman ina ganin

nine ba ta son in ci abincin

Sai Suraj ya ce,Ba haka za ayi ba, bari mu dasu Maryam mu shiga mu ci, idan mun gama za mu wurin wanka a swimming poo/ ko ba mu yi wanka ba mun zauna a cikin lema mu sha iska mu yi kallon

masu wanka. Kai da Asiya kuma sai ka je ka sawo wa kanku abincin, ka kai ta wurin hutawa ku ci a can kudan zanta, sannan ku zo ku same mu, ko ya ya ka gani?”

HMmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE