ALLURA CIKIN RUWA BOOK 2 CHAPTER 1 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA
ALLURA CIKIN RUWA BOOK 2 CHAPTER 1 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA
Lokacin da jirgin su Aliyu ya mika, Umar ya tuka motar mu ya maido mu gida. Da muka kammala ‘yan kintsi-kintsenmu, muka shiga kasuwa muka sayi abin da ranmu ke so. Washegari Alhamis muka yi bankwana da su Mama Inki wadanda suka yi mana sha tara ta arziki,
Umar ya dauke mu zuwa Malumfashi.
Bayan mun isa gida lafiya, a daren wannan rana ina kwance bisa gadona ina juya al’amurana cikin zuciyata, abin nufi a nan kamar maganganun Aliyu da hidimomin da yake mini, sai Sarkin wayo Ibrahim wanda na iske dimbin sakonninsa a gida.
Na rinka kwatanta maganarsu, shi dai Aliyu mutum ne mai tsananin kishi, inda son sa da kishi yake hadawa.
Amma Ibrahim mutum ne mai saukin kai da iya barkwanci, yadda duk abu ya bata masa. rai da wuya ya bayyana a fuskarsa. Allah ya sani tun ranar da muka fara aduwa na ji ina kaunarsa kwarai, amma so daya sak Aliyu nake yi ma, saboda so daban kauna daban kamar a harshen Turanci ‘so’ shi ne love, kauna kuma likness, to haka wadannan bayin Allah suke a zuciyata.
Ina sha’awar yawaita yawan hira da Ibrahim a
bisa dalilin irin barkwancinsa, ina kuma son yawan tsokanarsa a kan matarsa ba, amman na lura ya dauka ko ina taba kishi ne, domin na ji yana kara jaddada mini lalle ba a gida daya zai hada mu ba. kowacce da
gidanta kamar yadda Allah ya ce idan mutum na da hali, kuma yana gudun tasowar fitina.
Yanzu kan na tsai da wa zuciyata shawara idan
har na gama makarantar jami’a ban ji wani bayani ba daga Aliyu ba, to insha Allah zan zama rabon Ibrahim, badon komi ba an ce idan za ka auri mai mata to ka rinka jin lafazin bakinsa, idan har yana yawaita zagin matarsa da kuma tona mata asiri, to lalle ka guje masa domin Hausawa sun ce dorinar uwargida tana nan an aje ma amarya tata. Ibrahim duk yadda ake son a rike
amanar uwargida, to ita kam Habiba an rike,nata haka nan wadda ta zamanto amarya ta yi sa’ ar miji. To fa, in ana dara fidda uwa ake, na san Aliyu
yafi kowa sona, saboda shi dai Ibrahim yanzu ana
kokarin kwace goruba a hannun kuturu ne, saboda haka ne yake nuna rashin damuwarsa a bisa korai na yi masa ko na gaya masa.
Ina dai kwance na kara juyawa gefe guda na yi ajiyar zuciya, na fada a fili, “Allah! Allah!! Ka ba ni Aliyu, in har na rasa Aliyu anya zan Kara dacen masoyi? Mun koma makaranta bayan hutunmu ya kare a wannan lokaci bamu. da wani abun yi sai karatu, domin ‘yan kwanaki suka rage mana mu fara jarrabawa. Wasikun Aliyu da ‘yan katuna da hotunansa ko da yaushe ne. A ranar ziyara ma, Mukhtar na Hadiza ya zo da Umar, da misalin Karfe biyar na maraice sai , ga Ibrahim, na same shi zaune bisa motarsa.
A gaskiya Ibrahim shigar da ya yi a wannan rana abin a yaba ne, watoboyel mai ruwan kwaiduwa da hula zanna bukar, sai agogonsa mai tsada idon mai kallo a kanta.
Na yi masa sallama muka kuma gaisa, sannan ya cire gilashin idonsa ya Kara kallo na na dube shi cikin rausaya na ce, “Kallon fa?”
Ya yi murmushi ya ce, “Asiya kin rame da yawa”
Na ce, “Wallahi Ibrahim idan ka ganmu da karfe uku na sulusin dare za ka tausaya mana
Ya amsa mani da cewa, “Ko da ban ganku ba, na tausaya muku, na san lalle karatu na matsa maku, dalilin kenan na matsa maki da son in ga an daura .mana aure, kuna karewa sai mu fita kasashen wajen kin ga sai ki huta, jinin jikinki ya dawo maki muna dawowa sai ki ji dadin karatunki na jami’ a Na yi murmushi na ce, “Don Allah Ibrahim ka daina kawo mani irin wadannan shawarwarin na riga na gaya maka gaskiya ta idan har na ga aurenmu da Aliyu ba mai yiwuwa ba ne, nice mai ba ka shawarar ka fito mu yi aure. Amma ni ba ka ba ni damar tambayar su Zubaida ba, ina fatan suna lafiya?” Ya ce,Lafiya lau suna maganar ki kullum,yanzu har mutanen Tsiga sun san labarinki a bakin su Zubaida, ban san abin da ki kai musu ba da har kika janye hankalinsu haka, saboda na ga na sha kai su gidan abokina ko gidan ‘yan ‘uwanmu amma basu taba nacin in mai da su ba kamar yadda suke. nacin in kawo su wajen ki”Na yi murmushi na ce, “Kila yanda jininka ke sona su ma haka jininsu yake so na
Sai ya kyalkyale da dariya ya ce, “Mu muna sonki amman ke ba ki damu damu ba ko “”
Na yi ‘yar dariya na ce, “Haba Ibrahim ba ni sonka har na zo inda kake, kuma in nuna na damu da ya’ yanka? Sai dai ka ce ban baka hadin kai ba kamar yadda ka bukata, ka san komi sha’anin duniya yana bukatar bi a hankali da kuma nutsuwa, saurin gaggawa a sha’anin rayuwa yana jawo dana sani, amma na fahimci halin juna ma yana daya daga cikin tsarin rayuwa ta gari”.
Ya ce,Asiya na kan ji dadin irin kalamanki
masu kwantar da hankali, wanna na daya daya cikin abin da ya sa make kara kwadayin sonki, mu maza muna alfahari da irin halayyar mata irin ki,. kin san babu abin da ya fi yi ma namiji dadi irin ya dawo aiki ko unguwa an bata masa rai. a can waje ya zo gida matarsa ta gyara masa. Har abada irinki Asiya ba ki gundurar namiji.
Irin ku ne ake cewa idan kun so da namiji babu wanda ya fishi jin dadin rayuwar duniya, idan kuma kunqi shi ya shiga uku muddin Allah ya hada shi
Na daga kai a hankali na dube shi muka yi ma juna murmushi, sannan muka yi sallama, ya ce sai maunzo gida ke nan, ya yi mana fatan nasarar jarrabawa, ya miko mani ambulan wadda ta ba ni tabbacin kudi ne a ciki, ya kuma ba ni wasu in bai wa su Hadiza da su-Rabi.Har ya shiga motarsà ya tayar da ita sai ya sake fitowa, na ce,
“Ya ya lafiya ko an yi mantuwa ne?”
Ya ce, “Na ji yau ba ki tambayen Habiba ba balle ki ce kina gai da ita”.Sai na kyalkyale da dariya na ce, “A’a, babu ruwana in yi maganarta ka ce na cika kishi? Rufa mini asiri, na dai tambayi “ya’ yana a kuma ce ina gai da su
ya isa”Ya yi dariya ya ce, “Idan har ba ki sani ba, na fi son kina mani maganarta a nan nake fahimtar irin kaunar da kike mata
Hmmm labari fa nata tafiya shin koya zataci gaba da KAYAWA KUDAI kuci gaba da kasancewa damu a koda yaushe