ALLURA CIKIN RUWA BOOK 2 CHAPTER 10 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA

kira mú Shuwa’arab, ince a’a, rabi fulanin Yola,

rabi fulanin Katsina.

Daga wajen hoto sai muka zarce gidan Yaya

Ahmed, in ba ki manta ba shi Aminu ke bi yana da mata yaya Zainab da ‘ya’ya biyu Fesal da Fahad.

Na gai da Yaya Ahmed yana zaune a falo tare da yaran, ita kuma Yaya Zainab na kicin na shiga kicin din ina taya ta aiki muna hira.

Bayan mun yi sallar magariba Faisal ya shigo ya ce, “Aunty Baba Magaji ya ce kizo

Na ce, “Kai jama’a Yaya Ahmed fa na falon, ni kam kunya nake ji”

Zainab ta kyalkyale da dariya, sai ga Aminu ya shigo yana mani magana, sai Zainab ta ce, “Tana nan tana gulma wai kunyar Ahmed take it°

.

Yayi murmushi ya ce, “Nima yau haka nake fada da ita wai kunya take ji bayan har gaban su

‘Gwaggo take fadawa bisa kaina, amma yau girma ya.zo

Ya ci gaba da cewa, “Sai in tashi in hada masa salad

Na ce, “Kai Magaji mene ne laifin sakwarar doya miyar agushi?”

Ya ce, “Shan koko daukar rai, kin san bana son abinci mai nauyi da daddare” Na yi masa wani irin kallo, sai kawai na ji ya

rungumo ni ga- Yaya Zainab, sai ta ce, “Kai

Magaji baku da kunya’

Muna tafe bisa hanyarmu ta zuwa gida ne

yake ce mani kwanan baya ma’aikatarmu ta yi

niyyar tura ni gidan Rediyon B.B.C LONDON da ke

Ingila in yi aiki na tsawon shekaru hudu, amma sai

na nemi arzikin a bari nan da wata tara lokacin kin

kammala karatunki, kin ga da an daura aure sai ta

fiya a can kina iya ci gaba da karatunki, ko ya ya

kika gani?

Na ce, “Da ka yi shawara dani da sai in ce ka

tafi abinka alabasshi idan na gama sai ka zo mu tafi,

gudun kar nan gaba a hana ka”

Ya ce, “Bana zaton za su hanani saboda sun matsu inje, yanzu haka in na ce zan tafi a wannan watan za su amince mani, amma idan ba kya son

gani na sai in shirya i-nawa-in-nawa in yi gaba”.

Na ce, “‘a,a ka yi hakuri ba nufina ke nanba”

Sai ya dauke hannunsa guda daya bisa

sitiyarin mota ya riko hannuna, muna tafiya a

hankali muka nufi wajen telansa, ya murza mani

yatsu ya ce, “Ki bani minti biyar ina zuwa

gimbiyata” Ya ce, “Ke tukin mota fa aiki ne, tunda haka ne gobe zan fara koya miki, inda duk za mu ke za ki tufa Na ce, “Allah ya nuna mana”

Na fara matsa masa kafa a hankali zuwa hannayensa, sai nan da nan ya fara canzawa, kin dai san irin yanayin Asiya.

Na yi murmushi na mika mata kwalin kafirison. Daga nan sai ya tashi zaune ya sagalo hannayensa a bayana yana wasu irin abubuwa, yayin nan na rika wasa da gashin kansa.

Sai na ce, “Haba Yayana wannan ai bai dace da tsarin rayuwar musulmi ba, yana daya daga cikin rudin shaidan, kada mu biye ma sha’awarmu ta kai mu ga halaka, gara mu yi nesa-nesa da juna”.

Ya ce, “Eh, kema kin yi magana

Daga nan ya tashi zaune ya ce, “Zahra’u ni fa abin da nake son yi yanzu shine, Kokarin a daura mana aure, kin ga duk abin da zai wanzu ya wanzu da tushe”

Na ce, “Ba ka tsoron fadan Baba Sule kada ya ce mun yi rashin kunya?”

Ya ce, “Ai shi ne fa dalili ke nan na ce zan yi tunani a bisa lamarin ko wacce shawara na yanke za ki ji”. Na yi masa rakiya dakin Gwaggo, sannan na raka shi gindin motarsa.

Cikin sati biyu kacal na kware da iya tukin mota, ya hada ni da jami an ba da lasin din yarda ka tuka mota, ya yankar mani lasi na shaida. To kun ji wannan ke nan.

Saura wata shida in gama Queen Amina ba ni manta wannan daren na Juma’a muna hutu, a wannan zamanin bazara ne na yi wanka da dare na zuba wata bala’ in rigar bacci mai hawa biyu, a ranar Gwaggo ta je unguwa, sai na yi shimfida a kofar dakina, na kashe wutar tsakar gida na rika amfani da mai fitowa dakina, ina karanta wani littafi na Milss and Boon, sai na kifa littafin bisa cikina ina tunanin irin maganganun da yaron ke gaya ma yarinyar, na rinka kamantawa da wanda Aminu ya gaya mani a daren shekaran jiya, ina Kara jaddada son dan uwana rabin jikina Al-Amin, wanda na zaku kwarai da in ga an mallaka mana junanmu, amma Baba Sule ya fi yarda, wai shi dole sai na gama sakandire.

Ni ko a wannan lokaci na fi jin dadi da samun nutsuwa idan, ina makaranta, tun ina yarinya na saba hada jikina da Aminu a gaban kowa ba tare da damuwa ba, amma yanzu saboda soyayya ta tsananta

Hmmm

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE