ALLURA CIKIN RUWA BOOK 2 CHAPTER 11 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA

a tsakaninmu, kuma ga maganar addini daya hanar damu .

Ina cikin wannan tunani ban ji sallamar

Aminu ba sai dai na ganshi tsaye bisa kaina yana murmushi, ya ce, “Tunanin me kike yi haka wanda ya hana ki amsa sallama ta?” Na ce, “Tunaninka” Ya ce, “To ai gani na iso”

Aminu yana sanye da ‘yar ciki da wando na kafi shadda mai ruwan Kasa, amma mai hasken ruwa. Ya sha wankansa ya gyara sumarsa, yana ta zabga kamshin turaren Poinson.

Ya zagaya kusa da kaina ya zauna, yayin da ya jingina da bango ya mike kafarsa guda ya kuma tsayar da gudar, yana mai rike da hannuna, daya hannun nashi ya zagayo shi bayan kaina bisa filo.

Mun dade muna murza juna har ya kai ga jan dogon numfashi tare da sanyayyar ajiyar zuciya, sannan na kira sumansa a hankali ya amsa, bayan na yi gyaran murya na ce, “Bari in shimfida maka wata tabarma kada Baba ya same mu a haka ko?”

Ya ce, “Gaskiya ni fa Lami na fara gajiya da yadda su Baba suka zuba mana ido, wai mene ne aibun daurin aure ana karatu?”

Na ce, “Wallahi Aminu idan alwai hanyar da zan taimaka don a daura mana aure a shirye nake”Ya yi shiru sannan ya ce, “To ki shirya mu je

Funtuwa gobe wajen kakanninmu, wanda na san har ya fi mu kaguwa ya ga an daura aurenmu, mu kai

Karar Baba Sule ko ya kika ce?”

Na ce, “Eh, hakan ya yi daidai”

Da safe na sheka kwalliya, ita kuwa Gwaggo Karima babu abin da take illa duk inda na bi idonta na kaina, wanda na riga na saba da kallon ta, ni har na kan tunani wai shin da Gwaggo da Aminu inna mutu wa zai fi damuwa ne? Tabbas bani iya bai wa kaina wannan amsar. Na dauko

daya daga cikin manyan hotunanmu mu kai wa kakanninmu a Funtuwa.

Aminu ya iso, muka tsaya bisa hanya ya yi masu tsaraba kamar doya da kayan miya da busasshen kifi.

Kukanmu kam ya karbu wajer wadannan tsofaffi, sai dai ba a nan take ba, washegari Alhaji Amadu da kansa ya zo ya tsare iyayena, amma wallahi Asiya ba a shawo kan Baba Sule ba, saboda mutum ne mai fada da tsattsauran ra’ayi, ya same muni da Magaji ya zage tas. Asiya ba ki tambayen labarin samari ‘yan

hana ruwa gudu ba? Na ce,Na san kun sha artabu

dasu, sai dai dan gutsura mani”. Na mika mata cingam bayan na bare mata. Sai ta dora da zancenta da ceva, a makaranta wata rana na je kwanar su Amira kawata, sai ta ce,Ni kuwa Zahra’u zan baki amana”

mene fa?”Na ce,Ta ce,

, “A bisa sharadi in ba zan yi ma yarinyar magana ba”

Na ce, “Na amince”

Ta je kwanar wata yarinya mai suna Asabe ta dauko mani album din Asaben, ta ce, “Insha kallo lafiya, amma ita ta nuna mani ne saboda yarda”.

Na ce, “To”

.Na bude shafin farko sai ga hoton Aminu an lika tare da na Asabe, inda duk na bude sai Aminu

da Asabe. Wallahi! Wallahi!! Asiya sai na dauka ko

a mafarki hakan ba mai yiwuwa ba ne, har na gama

ban yarda wai Aminu ba nè, sai da wannan kawar tawa ta ce mini, “Wai Asabe ta gaya mata shi za ta aura, wai ma bikin ku ake so a fara sannan nata,

domin Baban shi ba zai yardar masa ya fara auren ta

ba, shi ne dalilin da ya matsu ayi naki alabashi in kin ga dama ki zauna, ya dai rage naki”.

A lokacin ne zufa ta fara karyo mani, na nemi yawu a bakina na rasa, ba tare da na ce uffan ba na

nufi dakinmu, kafin in shiga sai juya ta dauke ni ta

kada ni kasa rikica na fadi warwas. Mutanen dakinmu suka dauke ni suka zarce dani dakin da ake kwantar da marasa lafiya, aka nemo Nurse. Ni duk a wannan lokacin ina sume, da aka samu na farko na yi kokari in yi kuka amma ya gagara, sai na ce a ba ni ruwa in sha.

Na sha kuwa har sai da aka amshe, sannan na fara amai. Bayan na gama aka bani maganin barci, na sami barci har na tsawon lokaci.

Can tsakar dare na farko, na daga kaina sama ina kallon silin, sai hotunan Aminu da Asabe nake ganin ana likawa bisa silin din, kuma wannan hoton yana tuna mani lokacin da aka dauka babu ko shakka yawanci ma duk nice na dauke shi, wani a dakina wani a kasaitaccen falon Baba Sule, sauran kuwa a lanbun shakatawa ne da mukan je duk sati.

Na tuno irin halin Asabe, ba wata yarinyar kirki ba ce, ba ta kame kanta, unguwarsu daya da su gida,biyu ne tsakaninsu, ba ya so ko kadan ya ga ina magana da it, saboda halin ta na banza da nake zato, to ashe da biyu yake hana ni.

Na ce, “Yanzu ai da Aminu shi ke nan duk burin da nake da shi a kanse ya kau? Duk abubuwan da yake gaya mani karyar mamiji ne, shi ne fe ya ce,

“Ko mutuwa na yi shi da ‘ya mace, sai dai ya ganta da ido”. To ya ga ni da raina tun ma kafin ya cimma burinsa a kaina har ya alkawartawa wata

• Sai na ji tausayin kaina ya tsamanta a zuciyata tare da tausayin mahaifiyata, yadda na san bata son abin da zai bata mini rai, yau ga abin da na fi so a duniya ya kuduce mani, sai nan da nan na ji hawaye sun cika mani ido, na fara kuka ba ji ba gani, na yi kuka na koshi, sannan na sanyaya wa zuciyata dangana.

Na ce, “Komi ya yi zafi maganinsa Allah, kuma an ce in so cuta ne to hakuri ma magani ne” Nan take na dukufa rokon Allah ba dare ba rana, a lokacin na yi sa’a mun kammala jarrabawar Mock dinmu.

Ranar hutuna ne na roki arziki wajen su Rabi kawata suka aje ni gida. Yadda mahaifiyata ta ganni na yi baki ga rama sai ta san Ialle babu lafiya, na lura hankalinta ya tashi. Na ce mata rashin lafiya na yi ga jarrabawa. Kuma shima mahaifina bai ji dadin yadda ya ganni ba, amma sai suka sa mani ido kawai.

Da azuhur ina kwance ina taunar cingam irin na masifar nan, sai Aminu ya daga mani labule ransa a bace, ya ce mani, “Yau kuma me ya faru da har kika zubar dani a makarantarku?”

Hmmm

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE