ALLURA CIKIN RUWA BOOK 2 CHAPTER 13 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA

fassara mani so har sai da ya tabbatar wa kansa bana iya son kowa in ba shi ba. To me zai sa ya yi mani haka?

Aminu ya kasa shawo kaina a wannan karon, sai ya shirya tafiyarsa Ingila, tafiyarsa da kwana biyu Yaya Ahmed ya kawo mani wasikarsa. Ya ce mani, “Zahra’ u sai ki zuba ruwa Kasa ki sha Aminu ya bar maki kasar”

. Wannan wasikar ta bi layin

‘yan ‘uwanta na bude akwati na saka ba tare da na

karanta ba.

Kamar ko ina ranar fitarmu makaranta tazo na fito da sakamako mai kyau da kyaututtuka kamar.• guda biyar.

Ranar farin cikinmu ke nan noda Aminu, amma Allah bai yarda da hakan ba. Ina gida ina ta tunanin makarantar da zani wadda zan sami kwanciyar hankali, saboda ciwon son Aminu kullum

Kara tsananta yake yi a zuciyata.

Muna zaune da Gwaggo Karima a dakinta a wani dare muna sauraron B.B.C LONDON, sai wani yaro ya shigo ya ce, “Wai ana nemana a kofar gida”.

Na ce, “Ka ce bana nan”

Haba Gwaggo kamar tana jira ta hau ni da fada, ta ce, “Fita ta zama dole, tunda na kare karatu dole in kawo miji  aure yanzu” Na lura ran Gwaggo ya baci, sai na dauki gyale na fita. Na sami mutum biyu a jikin mota, a nan take sai na gano Sani ne wanda ya yi naci har ya gaji.

Muka gaisa yana ci gaba da son kutso kai don ya turo gidanmu, sai na ji kamar ya watsa mani ruwan zafi. Sannan ya fara mani zancen ya ji rashin mutuncin da dan’uwana Aminu ya yi mani wanda ba su yi mamaki ba, nice bakuwa a kan rashin sanin halinsa.

Na dai lura ba shi da niyyar tsayawa, sai na daga masa hannu na ce, “Look Sani, bani da lokacin tsegumi, kuma magana ta da Aminu ba ta shafe ka ba, domin ba a raba hanta da jini, saboda haka kun

-ga shigata gida sai da safen ku”

Ina kwance ina tunani lalle ina son Aminu, domin lokacin muna tsaye da Sani sai na ji kamar bisa kaya nake, maganarsa kuwa ta rika mani Kuna a zuciya, amma in Aminu na magana wallahi har bana son ya daina don taushi, idan yana cikin dakin nan yana kusa dani yana magana, to wallahi da wuya ki ji abin da yake fadi domin sassaukar muryarsa.

Ina mamakin irin kamewa ta Magaji Asiya, amma har ya yarda ya saki jiki da Asabe, suka kai ga halin da na same su? Yaya Ahmed ya yi ma yaron godiya ya tashi ya debo ‘yan sanda a motarsa sai wajen Asabe, tana wallahi babu ruwana makircin Sani ne. babu wanda ya saurare ta. Sannan Yaya Ahmed ya zarce gidan kangararrun yara ya yi duk abin da ya dace ya danka Abdullahi a hannunsu a hora shi har tsawon shekara daya, amma Baba Sule ya ce a mai da shekara uku.

Bayan an gama wannan kwamacala, ran nan sai ga Ahmed da motarsa suka hadu tare da Gwaggo Karima a kai mani fada, inda aka dora lefi a kaina, domin da ma bai wa Aminu goyon baya da mun bincika gaskiyar lamarin da wurwuri.

Washegari Yaya Ahmed ya aiko direbansa aka dauki ni zuwa gidansa, ina isa ya ce,’

“In shiga

dakin Zainabu in jira wayar Aminu daga Ingila”

Gabana ya yanke ya fadi ina tunanin da wacce murya zan yi ma Aminu magana? Bugun farko Zainab ce ta dauka suka gaisa, tare da tsokanarsa cewa na ki zuwa, sannan dai ta bani na kasa magana.

Ya ce, “Haba Lami ki yi magana mana ko na ji dadi”

Na ce, “Don Allah ka yi hakuri da abubuwan da suka faru a bisa kuskure”

Ya ce, “Wallahi har ga Allah babu komai, ni kam da baki yi abin da kika yi ba, to da na zarge ki a zuciyata in ce son da kike mani bai kai zuci ba, saboda so ke kawo kishi”

Haba dama abin da nake bege ainun, na sakar masa fuska muna magana tiryan-tiryan.

To kin ji inda muka tsaya da al’amarinmu

Asiya, idan ya shekara zai zo ayi mana biki kamar yadda Baba Sule ya ce. Wannan shi ne dan takaitaccen tarihina, abin da ya sa na ce miki duk yarnyar da kika gani akwai ‘yan matsaloli a tare da ita, kuma Asiya na yi imani da duk wanda Allah ya yi ma bai wa ta kyau, to yana da dan abin da zai kokamawa

Na yi ajiyar zuciya na ce, “Haka ne, amma ke ma wata birkitatta ce, bai dace ki zartar da hukunci ba nan da nan. Idan da Aminu mai son ‘yan mata ne ke ya dace ki zama shaida, tun kina yar

mitsitsiyarki kuke tare. Ni kam gaskiya ya ba ni tausayi, sai Alhaji Amadu kakanku, na yi imani ya fi ku rashin kwanciyar hankali a dalilin batawarku.

Ubangiji Allah ya dora mu bisa mahassada, kai duniya dai ta lalace, ko kuma in ce mutanen cikinta,

Allah shi kyauta, amin

Mun rabu da Zahra u ranar hutu, inda Umar Kanin Aliyu ya zo daukata, yayin da Zahra’ u Ahmed ya turo direbansa. Na, isa gida cike da tunanin

Hmmm

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE