ALLURA CIKIN RUWA BOOK 2 CHAPTER 14 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA

Zahra’u da Aminunta, domin labarinta ya tsaya mani a zuciya.

Na yi sa’a Hadiza ta zo ita ma ta sami hutun kwana biyar, duk dare muna tare da Ibrahim har ya fara nuna man rashin amincewarsa da zuwa na Kaduna.

Na ce,

“Wallahi wannan zuwan saboda

Zahra’u za ni

Ya ce, “Kai wannan Zahra’ u ta shiga ranki da yawa, ko da yake lokacin da na zo makarantarku na lura ita ma ta damu da ke kwarai da gaske”

•Na ce, “To ai shine nima ka ga na damu da

ita Ya yi dariya ya ce,

“Amma ba a damu da

Ibrahim dan marayan Allah ba ko?”

Na yi wal da idona na dan kada harshena nace, “Lah-la-la! Kai Ibrahim sau nawa za mu yi wannan maganar ne don Allah?”

Ya dan girgiza kansa tare da murmushi yace

“Wannan yarinyar! Wannan yarinyar!! Wanda duk

Allah ya bai wake ya gama burin ya mace a duniya”

Kwana bakwai na yi a Malumfashi, Umar ya tuka ni zuwa Kaduna. A bisa hanya na biya Zariya na duba mana jarrabawarmu, daga ni har ita Zahra’u mun yi abin kirki. Cike da murna na isa gidan su Mama Inki,

wallahi ban cika awa biyu ba da zuwa sai ga

Zahra’u, muka makale juna muna murna.

Ta ce, “Sai in tashi mu tafi gidansu”

Na ce, “Wai ma kwananki nawa kuna magana

da Aminu, ni ko ban ji sautin muryar danki ba, na

buga ba shi gida amma darajar uwa kina kusa kila in

dace ya dawo

Bugu daya shi ne ya dauka, muka fara hira

sannan ya ce, “Ba ni uwa da magani”. Na ba shi,

idan kun ji yadda suke hira za a ce sun san juna.

A nan ta roki arziki za mu gidan su na kwana, ya ce, “Na yarda da ke

Na yiwa su Mama Inki sallama, Zahra’u ta fisge mu a mota, na ce,Ke bani son sakarci sauke ni

Ta kyalkyale da dariya ta ce, “Ke dai ki yi ta

addu’ a amma ba zan fasa gudu ba, kuma daga yau zan fara koyar da ke mota”

Mun sami Gwaggo Karima tare da mahaifiyar

Gwaggo Badijo suna hira. To fa! Na tabbatar ni ‘yar

gata ce a gidanmu, domin nice mowar ‘ya ya wajen

Baba da Inna.

Amma Zahra’u ma abin ba dama, domin

yadda ta fifita ni a gidansu haka nan iyayenta da sauran danginta. Gwaggo Karima ta ce, “Yau Lami za a yi kwanan zaune ga ki ga Asiya”

Muka Kyalkyale da dariya, inda duk muka je

gidan danginta basu nuna mani bambanci da

Zahra°u.

Na haddace tukin mota cikin *yan kwanaki, duk da dai Umar ya fara koya mani a Malumfashi.

Aminu in muna hira a waya za ka dauka mun saba, domin ya san labarina na san nasa.

Alhaji Sule ya bamu turamen atamfa ni da

Zahra’u da na boyel. Ita ma Mama Inki ta yo mana dinki, iyayen Zahra’u kuwa ba a cewa komi sai

Allah ya saka masu da alheri.

Ayyukan makaranta suna neman rikice mana saboda yanzu komi ya kankama, wanna ya bamu rashin sukuni kowanne lokaci muna da abin yi, mun kafa kungiya domin bita, Kungiyar ta Kunshi maza da mata.

Mun shiga mataki na biyu, mun yi sa’a a wanna shekarar Musuli abokiyar zaman Zahra’u ta fita, sai na kwashe ‘yan sauran kayana na koma can.

Ni da Zahra’u komi namu ya zama daya, hatta suturar sawa bamu bambantawa muna amfani da na juna, kamar wajen takalma, agogon hannu ko kudinmu duk a hade suke, tare muke komi da komi da ita. Mun zama abin sha’awa ga masoyanmu a cikin makaranta, inda aka sanya mana sunaye kala-kala, yawanci sun fi kiran mu da ‘yanmatan aljanna, wasu kuma da sun hango mu sai ka ji sun ce in ka ga (Zahra ka ga Asiya). Kai sunaye dai barkatai suka sanya mana.

Inda na Kara imani da lalle wanda Allah ya bai wa kyau ya yi masa babbar baiwa, ina ganin saboda kyawun da Allah ya bamu ya Kara mana fice a jami’ar ta Ahmadu Bello Zariya, ba wai ta fannin ilimi ba ma kawai.

A lokuta da dama mutane na son magana damu ko su yi mana wasa, ko a nemi abota damu da dai makamantansu, Allah ya sani na san kyauna ya yi fice tun ina sakandire, amma lokacin da muke jami’a komi namu ya canza, har da karin zama da jama’a kala-kala da Karin wayewar kai, komi ya bambanta. Nan na Kara tabbatar da cewa, zama da

Jama”a shi ne babban ilimi ga dan Adam.

Idan mun sami hutun kwana biyu ko na karshen mako, idan bamu da ayyuka mu kan je Malumfashi, ta wanna hanyar ne Zahra°u ta san dangina, har Kuka-Sheka dangin mahaifiyata na kaita, inda idan kuma hutunmu mai yawa ne, to a Kaduna muke zuwa mu sha shi. Akwai wani hutu da muka samu na je

Malumfashi na yi amfani da kudin da gwamnatin jiha ke biyanmu na sayen kayan aikin makaranta da na abinci, na sayi saitin gado da doguwar kujera da madubi da ledar tsakar daki da makamantansu na gyara dakina.

Bani da wata lalura da kudin da gwamnati ke bani na sikolashif, Alhaji mijin Mama Inki ya dauke mani nauyin karatuna.

To a wannan hutun na sami canjin daki, inda mahaifina ya koma nawa na cikin falo, ni kuma na koma na tsakar gida, na gyara dakina har ya zama abin sha’awa ga mutane. ‘Yar Zainab autarmu na makarantar ‘yanmata ta Sabo aji daya.

Hmmm

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE