ALLURA CIKIN RUWA BOOK 2 CHAPTER 15 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA

Aliyu bai dawo kwas ba sai da ina shirin barin

(mataki na biyu a jami’a, ina shirin shiga na. uku. Ranar laraba misalin goma da rabi na safe na yi wanka na kammala shafe-shafenmu na mata, sai kawai naji ina da sha’awar saka wata super fara mai ruwan ja wadda Mama Inki ta dinka mana ni da Zabra’u, dinkin mai bayyana surar dan Adam ne.

Ranar na yi niyyar zuwa gidan wata kawata da ke karatu a jami’ar Bayero ta Kano, amma da azuhur in na gama aiki saboda duk. ilahirinmu

‘ya’yan gidan muna nan muna hutu. Ita kuma Inna Aisha ta je yinin suna cikin gari, yayin da Yusuf yake aiki a ma’aikatar gona, shi kuma Yaya Abubakar yana tare da bankinsu in yazo hutu.

Muna zaune a dakina ina gayaran kaina sai wani yaro ya yi sallama ya ce, “Asiya an ce kin yi bako a zaure”. Na ce, “To, ka ce ina zuwa

Na yi mamaki, domin mun yi da Ibrahim zai yi sammakon zuwa Kano a wanna rana. Na dauki dankwalina na sagala shi a wuya na suri silifas din

‘Yar Zaina na nufi zaure, amma me zai birge ni har in ja da baya in jefas da dankavali? Sannan na fara shewa! Sai kawai na hango Aliyu Gadanga Kusar yaki yana tsaye a zaure ya goya hannayensa bisa kirjinsa.

Yana ganina ya fara murmushi, cikin kasaita da burgewa ya ware hannunsa ya bude mani su duka, na Kara da gudu na shige ya mai da ya sanya dan makullin soyayya ya kulle mu ruf, babu abin da nake ji a lokacin sai Kamshin jikinsa da taushin fatarsa, da kuma dumin jikinsa.

Mun dade rungume da juma babu wanda

Allah ya ba fasahar yin wani abu, ko tunanin a inda muke tsaye, har sai da muka ji tsayuwar na neman gagararmu sannan na nisa na bambare dan makullin da ya rufe ni a kirjinsa, na dago kai na dube shi na ce, “Aliyu”.Ya ce, “Asiyatu”

Na kamo hannunsa na ce, «Zo mu Karasa cikin gida saboda na farko Yaya Abubakar zai bukaci dakinsa anjima, na biyu Inna ba ta nan, sai na Karshe yanzu dakina a gefe yake babu matsi idan ka shigo

Ya zauna bisa kujera na tsaya a gabansa ina kallonsa, na ce, “Aliyu ka kara fari ka yi kyau”,

Ya ce, “Wallahi Asiya kin fini yin kyau, duk kin canza mani” Na yi murmushi, nasa hannu na cire gilas dinsa na ido na mayas a idona, na ce,”Da gaske dai

Aliyu ne”wannan lokacin Zainab ta yi sallama ta shigo, saboda na aike ta sayen magi, tana hada ido da Aliyu sai ta ce, “Lah! Sannu da zuwa Yaya Ali” Ya ce, “Yauwa Zainab” Ya dube ni ya ce, “Asiya Zainab ta yi girma” Na ce, “Babu laifi” Ya ce,

*Zainab zo nan in yi hutu da ke, amshi

makullin motar nan”. Ya nuna daya daga ciki ya ce,

“Ki sanya wannan ki bude but ki kwaso duk abin da kika gani”.

Bayan ta- fita Aliyu ya ci gaba da kallon kusurwa-kusurwa na dakina, yana kallon yadda na mamaye dukkan daki, ba a san ma kowa ba sai shi kadai, sai ko Zahra wanda take da Aminu.

Ya dube ni ya ce, “A gaishe ki da iya tsara hotuna”

Na yi masa wani irin kalle da lumshe ido, nace,

, “Har na fika?”

Ya ce, “Za ki fara ko daga zuwana”.

Na ce, “Kai Aliyu ni dai babu ruwana”.

Na fice da gudu na hado masa tea da biskit.

Bayan ya gama sha muka rike hannun juna yana -bayyana mani yadda kwas dinsa ya kammala cike da nasara, nima na ba shi labarin yadda karatuna ke gudana.Sannan ne ya jawo akwatuna guda biyu ya ce,

“Ga tsaraba”. Sai wata jakar leda mai dauke da bandir din shadda da turmin atamfa biyu, ya ce, “Na Babana ne, atamfofi na Inna Hafsatu”.

. Ita ma ‘Yar Zaina takalmi, Hadiza agogo da doguwar riga, Mama Inki saitin agogo mai kalar fuska goma. sha biyu da leda goma sha biyu.

Ni sai na rike baki kawai ina mamaki, kamar ni kadai da ‘yan ‘uwana Aliyu ya mallaka. Sai tunani ya zo mani ina ma a ce wadannan akwatunan Aliyu ya kai gidansu an kawo gidanmu a matsayin neman aure? Amma bari in ji manufarsa.

“Aliyu zan amshi na iyayena amma nawa ka bari sai nazo gidanka komi ka yi mani daidai ne”

Ya zabga mani harara ya ce,

“Kada ki maidani sakaran namiji mana Asiya, ko kin fara shakkar aurenmu ne? Ni duk abin da na baki da zuciya daya na baki, saboda so da kauna. Idan ina da abin da ya fi haka zan mallaka maki, ki amsa da zuciya daya ba rokona kika yi ba niyyar kaina ce.

Asiya duk duniya bani da abin da na fi so da in mallaka irinki, ke ce mace da bana hada ta da kowa a zuciyata, saboda haka ina da wani nema wanda ya zarce ya ke?”Na ce, “Aliyu na gode Allah ya saka da alhen

Ya ce, “Amin”

Sai ya jawo hannun akwatin ya bude ya fiddo mani rediyo da rikoda mai gidan kaset biyu, ya ce,

“Ga alkawari”Na amsa na yi murmushi, sai takalmi kala hudu kowanne da jaka mahadinsu, ga kayan gyaran gashi da sauran kayan shafawa.

Ya bude babban akwatin, shi kuma turmin atamfa biyar, shadda daya, leshi biyu, sai siket da riguna masu bala’in kyau kankana biyu da dogon wando da dogayen riguna kala biyu suma iri daya.

Sai na dubi fuskarsa ina neman bayani, ya ce,

“Ke da uwata Zahra’u’

Na ce, “Lah! Ya ya ka san girmanmu daya?” Ya ce, “Kin manta da hoton da kuka dauka a

Yola wanda kika aiko mani da shi?”

Na ce, “Okey haka ne”

Ya bude aljihun akwati ya fiddo wata ‘yar batta ya dauko wata sarka ta zinare tana ta walkiya wadda har daukar ido take, ina ganin zinare da daukar ido amma ban tada ganin irin wannan ba, a  tsakiya an rubuta A2  shi kuwa dan kunnen a kasa

Hmmm

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE