ALLURA CIKIN RUWA BOOK 2 CHAPTER 16 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA
a sama aka sa A, abin hannu an rubuta kamar sarkar A2, sai zoben A2.
-Na ce, “Wai Aliyu ya ya a kai aka yi maka wadannan saitin?’
„Ya yi murmushi ya ce, “A Amerika aka Kera mini su, abin da duk kake bukata shi za a rubuta maka, da kuma abin da kake so. Abin nufi a nan, ana amfani da danyen zinare kamar wannan kin ga kuma
“ana iya amfani da daiman idan kana bukata. Da yake farkon sunayenmu sun zo da “A’ wato Aliyu da Asiya, shi ne na yi amfani da su ya zama A sau biyu ke nan”
Na ce, “To abin da ya dace ka aje wadannan a hannunka ran da Allah ya nufe mu da aure sai ka fito a wajen liyafa ka sanya mani abin zai burge kowa
Aliyu”
•Ya yi tsaki yà ce, “Ke idan kin aje a hannunki me zai ci su? Kuma ma wai har yaushe za ki aje sai ranar liyafa ki yi amfani dasu, Allah zai bayar da na ranar liyafar. Wanna na so sanya maki kwana biyar da suka shude, wato ranar taya ki munar cika shekara goma sha takwas da haihuwa, amma Allah bai yarda na iso a daidai ranar ba”.
Na yi dariya na ce, “Ashe baka manta ba”
Ya ce, “Abin kamar ke ce? Shin wai yaushe
Zaki Kaduna ne?”Na ce, “Ba lokaci”.
.Ya ce, “Ga shi ina da bukatar ki raka ni, saboda rana ita yau hutuna zai Kare, zan fara aiki a Kano, kin san yanzu zan fara fila Kasashen waje”.
Na ce, “Eh haka ne, Allah ya tabbatar da alheri kuma ya kare. Amma ga wani hanzari ba gudu ba”
Ya ce, “Kamar mene ne fa?”
Na ce, “Ina son zuwa Katsina galadanci dubo Gwaggo Juma, ta sha rashin lafiya. Ina kuma son ganin Hadiza duk dai a can Katsina”
Ya ce, “Abin da za ayi inda kike son tafiya nan za a fara zuwa, Kaduna ai hidimar da zan yi ta yini daya ce, Asiya ina mamakin yadda kika canza mani, da a ce da ke na yi wannan tafiyar ban san irin kyan da za ki yi ba”.
Na yi masa wani irin kallo na dushe ido, na rika wasa da ‘yan yatsunsa na ce, “Mu fara zuwa
Kaduna gobe ko?”
Ya ce, “Asiya wanna kallo da kike mani kina tsunduma ni cikin wani hali, idan na mai da martani ko dan ya ya ki fara mani korafi saboda ni Ali sarkin laifi ne”.
A nan muka ji maganar Inna Hafsatu, na saki hannum Aliyu na fita, nace, “Inna kina da labarin zuwan Aliyu?”
Ta ce,Haba’ saukar yaushe?”
Sai ya fito ya durkusa har Kasa ya gai da ita, gaisuwa cikin nutsuwa da nuna surukuta. Ta miko mani dan makullio gidanta tAce mani, “Zata gaisuwa gidan Malam Sallau jikansa aka yaye shi ne
Allah ya yi masa rasuwa” Na ce, Ayi musu gaisuwa Inna sai kin dawo”. Na komo zan zauna Aliyu ya ce, “Zo nan zauna bisa cinyata
Na ce, “Aliyu akwai zunubi fa, idan ka yi hakuri har kwanciya sai na yi karewar zama”.
Ya ce, “To zo in sanya miki wannan sarkar” Na ce, “Ka bari zan sanya da kaina
Ya ce, “Wallahi! Wallahi!! Idan baki tsaya na sanya maki ba zan zuba su a masai”.
Na ce, “Yallabai ayi hakuri”.
“Na zauna daf da shi ya fidda ‘yan kunne da ke hannunsa ya saka mani su haruffan sunamu, na juya bayana ya saka mani sarkar, a nan na ji ya kwantar da hannayensa bisa wuyana yana shafawa a hankali.
Ya ce, “A duniya babu jikin da nake so irin wannan amma ba a yardar mani in taba”
Na juyo na kamo hannunsa na rike, na ce,
“Ba ni da laifi dokar Ubangiji ce, Aliyu me yasa
kake son mantawa ne a ko da yaushe idan tare?”
Ya dauko zoben zai sanya mani, sai ya tareni da ido na neman bayanin yadda aka yi na mallaki rubba uku a yatsuna, kuma duk na zinare.
Na ce masa, “Wannan dai wanda yake a yatsan alkawari kai ne ka sanya mani, sauran biyun kuwa Mama Inki ta sawo mani da ta je Umara saiti ne ma”
Ya yi na’am, sannan ya nemi yatsan da ake sa zoben aure ya saka mani, ya sagala mani abin hannu, ya rika wara mani yatsuna yana saka kowane yatsan a baki, ni dai ina kallonsa cike da sha’awar abin da yake yi.
Ya ce, “Asiya wallahi ban tada ganin yatsu masu ban sha’awa haka ba. Ga Kumbunan ki masu tsari, randa na mallake ki wanna hannu zai sha aiki, amma ba wai na tukin two ba ko damun fura ba, a’a, na.
“Kai Aliyu”
Na rufe fuskata saboda kunyar abin da Aliyu ke fadi.
Na ce, “Aliyu bari in je in maka abinci ko za ka iya cin girkin Zainab?”
Ya ce, “Ke ‘yanmata ba inda zaki ki barni, daman can ba ki da niyyar shiga kicin irin wannan
ado da kika tsala, idan dai ba wani aka yiwa alkawari zai zo ba”.
Na ce, “Idan na yi ma wani saurayi alkawarin zuwa ai nan za ka wuni za ka ganshi ke nan ko?”
Bayan Zainab ta gama abinci na je ina rabawa, lokacin ne Aliyu ya je masallaci. Zainab ta ce, “Yaya Asiya sai walkiya kike yi wannan sarka fa?”
Na ce, “Cikin tsarabar da Aliyu ya kawo mani
ne” Ta ce, “lye, Yayar ba”
Na ce, “Ki shirya ‘Yar Zaina gobe da ke za mu Kaduna
Ta yi dariya ta ce, “Yaya don Allah kada ki zolayen da gaske kike?”
Na ce, “Allah da gaske nake yi Zainab”.
Sai na ji yaringa ta makale ni tun karfinta tana rawa tana shewa, na ce, “To ya isa ‘Yar Zainab kada ki ka dani”.
Da la’asar sansanya Inna ta dawo, sai da ta shiga falo ta kintsa sannan Aliyu ya bi ta suka gaisa tare da hira a bisa tafiyarsa, Aliyu ya nuna mani ya ji dadin yadda Inna ta fara sakin jikinta da shi ta rage Jin kunyarsa.
Shima Babana ya dawo aiki ya sami Aliyu, haka nan Yusuf da Yaya Abubakar. Aliyu mun yini
Hmmm