ALLURA CIKIN RUWA BOOK 2 CHAPTER 17 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA

ALLURA CIKIN RUWA BOOK 2  CHAPTER 17 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA

sukutum da shi a wanna ranar, sai da misalin karfe bakwai da rabi na dare ya tafi da son ya ga mahaifina da aminin mahaifinsa, sannan ya wuce masaukin sa wato na mijin yayarsa.

Bayan sallar isha’l ne na fiddo ma su Inna da tsarabar da Aliyu ya kawo mana, na ce ma Inna ta aiki Zainab ta kai wa Inna hafsatu nata. Tace A’a. ba haka za ayi ba, a dai ce tazo

Hakan aka yi kuwa, muna cikin kallon kayan wanda ita dai Inna hafsatu ta kame haki tana jinjinawa, sannan tace , “Wannan yara Allah ya fidda mu kunyarsu, irin wanna hidimar ta fara bani tsoro, sun riga sun sakankance a kan basu da mata sai ku”

Inna Aisha ta ce, “Ni wallahi wannan hidimar ta fara gundurata, yanzu dai ya dawo lafiya abin da ya dace ya fito kai tsaye a daura musu aure, alabasshi ko a gidansa ne ta gama karatun”.

Inna hafsatu tace, “Abin da ya dace ke nan, kin ga ni ran nan da Mukhtar yazo da hadiza har tausayi ya rinka bani, na ce ya dai ci gaba da hakuri dan Bature ya yowa Baban ‘Yar Zaina wasika yana nan zuwa karshen shekara, kin ga idan yazo sai ya danka ma Mukhtar hadiza kowa ya huta”

Ana cikin wannan hira mai dadin sauraro a gare ni, sai Yusuf ya shigo ya ce, “Yaya Asiya ga mijinki na boko nan ya zo”

Aka kyalkyale da dariya, domin a gidanmu

Yusuf shi mai ban dariya ne, inda har Inna Hafsatu ta sa mana suna da hana wuri maraici.

Sai Inna Hafsatu ta ce, “Kai Yusuf baka rabo da abin ban dariya, wane ne bokon wane ne na gaskiyar, sanin gaibu ai sai Allah, ita ‘ya mace ta mai rabo ce”

Inna Aisha ta ce, “Hala Ibrahim ne”

Ya ce, “Shine”

Na yi shiru. Zan fita sai Inna Hafsatu ta daka mani tsawa ta ce, “Maza ki cire wannan sarkar ba yanzu kika gama yi mana bayaninta ba, ai cin fuska ba shi da amfani, shi sai ya dauka da niyya kika yi”.Na ce,

“Inna shima ai ya san wahalar da kansa yake”. Na dai cire na fita.Bayan mun gama gaisawa tare da tambayarsa iyalinsa, sai ya ce, “Habiba ta je kai yara hutu gidan wani abokinsa Lagos, saboda da ita zai fita Ingila, wai ta dame shi da Korafi, kullum shi kadai yake fita bai gayyatarta ko sai na je”. Ya dubeni yana ‘yar dariya. Na ce, “Ita wasa take maka ba ka je da ita ba ka fara zuwa da ni?” Sai ya ci gaba da irin surutansa, a lokacin daga kaina sama ina tunanin abin da ya gudana tsakanina da Aliyu, ina rikon Allah yasa nan da sati biyu ina gidansa.

Sai can daga nesa na ji muryar Alhaji Ibrahim ya ce, “Haba Asiya tunanin Kanin nawa ne yau har ba ki da lokacin saurarona? Na san yazo kuma a nan ya yini yau.Banyi mamaki ba don ba ki da lokaci na

Sai wannan ranar na ga dan bacin ran Ibrahim kadan, na ba shi hakuri na ce, “Lalle mutane ba su da dama, yanzu har an kai ma labarin”

Ya ce, “An gaya maki mu na wasa ne, abu sai dai idan ba ayi ba, amma a kunnenmu zai kwana”

Na yi murmushi na ce, “Daman ina son in gaya maka gobe ina son zuwa Kaduna wajen

Zahra’ u amma jibi zan dawo

Ya yi shiru sannan ya ce, “Ki dai gaya mani za ki raka masoyi Kaduna, amma babu ruwan Zahra’u tunda mun je da ko, in ba haka ba sai da hutunku yazo Karshe zaki tafi Kaduna”Na lura ya fusata ainun, sai kuma na ji rashin jin dadi da ganin fuskarsa. A nan take na ce, “To shi ke nan na bar tafiyar na fasa tunda dai ranka bai so ba Ibrahim” Ya yi wata irin dariya ta jin dadi. Ni kuma da na ga ya fara saukowa sai na Kara fifita shi da nuna masa abin da yake so hakan za ayi.

Ya ce, “Shi ke nan Asiya kin dai tabbata jibi za ki dawo ko?”

Na ce, “Insha Allah kada ka yi shakkar hakan a ranka

Da za mu yi sallama ya bani ambulan da kudi a ciki, ya ce, “Ga wannan a sai wa Zahra’u lemu a bisa hanya”. Na amsa na yi godiya.

Kwaliyar da na shirya da safe

Aliyu, ko ni na yi sha’ awar kaina, wani boye-les ne mai hasken sararin’ samaniya, a Zariya wajen

‘yan Ghana aka mana dinkin, an sha taguwar daga baya, yayin da a baya aka bude ta sosai.

Na gyara gashina kai ka ce wata ‘yar Baturiya ce, na yi wani daurin dankwali wanda da shi da babu duk daya ne, saboda tsakiyar kan mutum a bude yake. Haka nan baya, ‘yan jami’ ar Zariya na kiran wannan dauri first lady. Ga takalmana masu tsinin gaske, wanda Inna Hafsatu ke cewa ba ta amince ta sanya su gudun ta fadi ta karye a banza a wofi.

Sai na yi ma Inna sallama na fito zaure, sannan na fiddo tabarau na na saka. Aliyu ne zaune a mota ya yi sauri ya fito, ya amshi kayan hannun Zainab ya saka booths , ya bude mani mota na shiga ya mayar ya rufe, ya ce, “Ranki shi dade gimbiya”. Na ce, “Wannan  yallabai”.

Munzo Funtuwa ya tsaya sayan jarida, a nan ne ya ce mani, “Kin ga da kin iya mota da na dan huta”

Hmmm

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE