ALLURA CIKIN RUWA BOOK 2  CHAPTER 18 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA

Na ce, “Kawo in gani da koyo a kan iya”.

Ya bani tare da yi mani bayani, ina bin sa da

“To”. Zuwa can ya lura da yadda na ke tuki, sai ya ce, “Ke ban yarda ba, daman kin iya mota ba yau ne kika fara koyo ba”• “Na yi dariya na gaya masa daya daga cikin «aikin Mamansa Zahra’u ne. Ya ci gaba da karatun jaridarsa, ya bai wa Zainab ita ma suka barni da jin sauti da jan mota? Mun iso Kaduna na dauke hanyar gidan su Zalta’u.Ya ce, “Ina za ki kai mu?”

Mun shiga, tare da Zainab inda na sami

Gwaggo Karima tana tsame dan wake a kicin. Na ce,

“Sannu da aiki Gwaggo”Ta dawo cikin mamaki ta ce, “Asiya kune a garin yau?-Sañnun ku da zuwa”

‘Zainab ta durkusa suna gaisawa, ni kuma na tankwasa muryata na ce,Gwaggo ina mutuniyar

Tawant?, Ta-ce, “Tana nan kwance wai yau kuma da ciwon kai aka tashi, amma tunda kinzo ai kan ya warke yanzu. Shin Asiya ‘Yar Zainab autar Inna ce? Nace Itace Gwaggo” Na zauna bakin gado na rika ja mata *yan yatsai ta bude ido, haba tana arba dani ta

rungume ni muna kuwwa, ta dubi Zainab sannan da nan ta sake ni, ta je ta rungumi Zainab ta ce, “

ke ce bakuwata””Danki na can kofar gida”

*Ki bari don Annabi, Asiya shi ne za ki shigo

ki har mani da a waje?”Ta fita tana shaida ma Gwaggo, ta ce ta taryo

Aliyu zuwa dakinta, muka fito tsakar gida da abin

motsa haki, sai da muka kintsa ciki sannan na fiddo

mata tsarabarta.

Ta ce, “Kai! Kai!! Dana duk ni kadai ke da wannan? Na gode Allah ya nuna mani ran da zan

rako maka wannan takardar gidanka

Ya ce, “Amin Mamana Ta fice taje ta nuna ma Gwaggo, ita ko gwaggo batayi wata-wata ba ta shigo godiya.

Zahra’u ta saka ankon kayana, domin anko Aminunta

ya aiko mana da wandan boyel din, muka fito zuwa

gidan su Mama Inki inda za mu kai Zainab, su

Zahra na gidan baya ni da Aliyu a gaba.

Zabra’u ta dube ni ta ce,Yau har daurin

dankwalin fina mana Aliyu yayi dariya ya ce,

*Wallahi Mama nayi ta gaya mata amma taqi. To ga shi na ji kunya Na Kara rike sitiyari da kyau, na waiga na dube shi na yi murmushi, na ce, “Aliyu dan Mama” Muka kyalkyale da dariya.

Mun sami su Mama Inki lafiya lau, a wannan ranar “Yar Zainab ta amshe mani fadar yaran gidan, sun fi murma da zuwanta, ni daman tun da na sami sahibata ai shi ke nan, ga Karin jin dadi na samu muna da bikin wata Kawarmu Maimunat Said, saboda haka ni zuwa Kaduna ya yi riba ke nan, duk mun kosa mu tafi domin mun san bikin zai hadu irin namu ne.

Aliyu ya ce, “To ku yanzu ya ya za mu yi ke

nan?”Zahra’u ta ce, “Kada ka damu damu, abu daya nake so kai mana yanzu shi ne, ka aje mu gidan Yaya Ahmed zan dauki motar yaya amin zanyi amfani da ita

Ya dubi Zahra°u ya ce,”Af. Mama na manta

ban yi godiyar koya ma giwar tawa mota da kika yi ba

Ta ce, “Haba dana kamar ba surukata ba? Sai dai na sha “yar matsala a dalilin shegen tsoronta

Na taka birki da karfi har ya yi kugi da muka iso kofar gidan Ahmed. Dalili shi ne karen gidan ne ya fito a fusace, na ce, “To Zahra’a sai ki shiga ki fiddo motar kin dai san ni da tsoron kare”

Ta barni da Aliyu a mota wanda ban so ba,

saboda tun da muka baro gida bai samu mun kebe ba

sai yanzu, a nan ya dora mani kafarsa bisa tafin

Kafata yana murzawa a hankali, ni kuma na sanya hannu na rike nasa ina mai masa kallo na sha’ awa.

Na ce, “Mamanka fa na kallon ka”

Ya ce, “Ba za ta yi mani fada ba, domin ta san matata ce nake tare da ita”Na ce, “Matarka insha Allah”

Ya yi dariya ya ce, “Yarinya ki fa daina sa

shakka da maganar aurenmu”

Na ce, “Ai ba a shakka da al’amarin Ubangiji mai canza al’amarinsa duk lokacin da ya so”

Ya yi shiru, ya dubo ni ta gilashin mota a

Idonsa da alamar tunani mai zurfi ya dauke shi, domin Zahra’u nata danna mana hon bai kula ba, sai

da na taba sajensa sannan ya waigo ni ya yi ajiyar

zuciya ya ce, “Sai nazi da la’asar”

Na ce,Muna da liyafa a wannan lokacin

kamar yedda na gani a katin, kuma qilama zamu

kai amarya Ya ce, “Ban laminta ba” Na ce, “Hujja”

Ya ce, “Ina kishinka”*

Na harare shi zan yi magana ya rike mani

lebe, Zahra’u ta kara danna mana bon, nayi sauri na

saka takalmina tare da sagala jakata na fito, na dafa kafadarsa na ce, “Sai na ganka da daddare”

Ya fadi wasu kalmomi cikin harshen Turanci

wanda ya bani mamaki har na rike baki, yana Kyalkyala dariya.

Zahra’u ta fito daga unguwar su Yaya Ahmad

ta bulla unguwar Sarki, inda muka bi babban titin

Ahmadu Bello Way, sannan muka doshi Bakori

Road gidan su Maimunat.

Zahra’u ta ce, “Ke Asiya wannan da nawa

lalle dan rayuwa ne Kwarai da gaske, kuma gaskiya

kin iya kissa, wannan tun kafin ki je gidansa kin

gama da shi tsaf, ina kuma in ya zo hannu. Na lura kallon da kike masa ma daban ne”.

Nace da yazo hannu sai dai ki haifi wani,

kuma ma ke Zahra’o har za ki ce nafiki kissa? Mun dai zo daya, a waya in kina magana da Aminu abin

gwanin ban al’aiabi” Ta canza giya sannan ta dube ni ta ce, Wallahi yau da tunaninsa na kwana wanda shi ne musabbabio ciwon kaina, ma kosa azo, nida za a yardar mani sai in bar karatun nan idan da rabo nayi

a can gaba inbi Aminu, yau kin ga yadda kuke

burge ni ke da Aliyu, kada ki binciki zuciyata”

Na yi murmushi na ce, “Kinfi ni kwanciyar

hankali Zahra  saboda kefa yau baifi wata hudu ba

Hmmm

Related Articles

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE