ALLURA CIKIN RUWA BOOK 2  CHAPTER 19 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA

a daura aure, to kin hada kanki dani wadda har yanzu babu wata magana kwakkwara”

Ta ce, “Haba Asiya duka-duka ba jiya kuka hadu ba, ai bai riga ya kintsa wurin zama ba balle ya fara maganar aure”

Mun isa inda ake zaman- lallan Maimunal, ganin mu ke da wuya ‘yammata suka fara kuwwa ta yan makaranta idan sun ga abokan su, gida kam ya cika da ‘yan boko sai al’adunma ke tashi, muka fada cikin ‘yan’uwa aka yita yi damu, kai mai kyau dai duk inda yake ya fita daban, nan da nan muka haske wurin ni da Zahra’u, wanda har ya sa na dan rika jin kunya saboda yadda ake kallon mu, babu ma kamar wadanda basu sanmu ba, ina jin wasu na tambaya wai mu ‘yan’uwa ne?

Da karfe uku ne muka koma gidan su Zahra’ u° don mu tafi Malumfashi tare gobe, daga nan mu wuce Katsina dubu Gwaggo Juma. Ta ce, matsalar ita ce wajen Baba Sule. Na ce, ni kuma ba na jin wannan domin muna shiri.

Riga da siket cikin irin tsarabar Aliyu su muka zuba masu ruwan kasa, yadin na walainiya tare da daukar ido, rigar daga Kugu an dan tsuke ta da roba, hannunta dogo, siket din ya wuce gwiwa.

Da farko da Zahra’u ta sanya nata rudewa nayi, na ce, “Zahra’u sun fi kyau da ke”. Ta ce, “Ni

kuma ina ganin idan yadda suka amshe ki nima hakan suka yi mani ai ko na ji dadi Asiya”

To daga ni har ita Zahra°u wajen maganar gashi ba a cewa komi, muka sake gyara fakin dinsa yadda zai yi tsari da kayan da muka saka.

Ta ce,Asiya zinaren nan mai harufa ya

dace da kirar jikinki, lalle dana ya mutu kanki”

Na ce, “In ya mutu a kaina ya aiko gobe a daura mana aure”

Ta yi murmushi ta ce, “Ki sa ranki a inuma kamar gobe ne”Wallahi Zahra’u har dabara na yi masa na ce ya bar wannan kayan sai mun yi aure wai don dai ya gane ina nafin ya ba da gidansu a kawo, amma sam ya ki maganar Mun fito tsakar gida Gwaggo tace

“Ga dai kwalliyar har kwalliya sai dai kun bata wajen rashin gyale ko dankwali”

Na dubi Zahra°u ta bata fuska na ce, “Ta fiddo mana gyaluluwanta saboda wanna fita a makaranta ta dace damu”

Motarma ta bi jerin gwanon motoci don zuwa wajen liyafa, a wajen liyafa hankalina ya tashi kwarai yadda maza suka matsa mana, na nemi Zahra’u damu koma gida, sai na tuna da Karin

Da Karfe bakwai muka baro wajen liyafa, sai da muka gama sallar isha sannan muka je gidan Baba Sule, inda babu wata tangarda ya amince mu tafi tare da Zahra’u.

Tara da minti shida Aliyu ya zo, na rufe idona na ce Zahra’ u ta ce masa na yi bacci. Sai na ji ya ce,

“Barni da ita Mamana na san abin da ba taso

Sai na yi zumbur na tashi, ya sanya Zahra’u ta dibar ma su Gwaggo wasu kaji da ya zo da su, ni da shi muka zauna muna ci ina mika masa, sai da muka gama ne ya kyalla ido ya dauko jakata ya ce, bari ya sami cingam raguwar biki.

Haba! Ban san lokacin da na haye cinyar

Aliyu ba muna kiciniya, harna fara gajiya sai Allah ya kawo mana Zahra’u.

Ta ce,

“Me ya faru kuma?”

Ya wurga mata jakar ita kuma sai ta fice da ita, sannan ya rungumo ni na harare shi, na ce, “Kai lafiya?”

Ya ce, “Ba ki da masaniya lokacin da kika haye ni?”

Na amshi kaina da kyar.

Zahra’u ta dawo da jaka a hannunta tana dariya tare da manne mani ido, ta mika masa. Yana

Mahaifin Zahra’u ya kwalla mata kira, sai

Aliyu ya Kura ma wani hoton Zahra’u da Aminu ido, nace,

“Wai kallon me kake masu ne haka?”

Ya ce,

“Hoton ne ya yi mani kyau, ina make

wayayyiya ce muma mu yi irinsa”.

Na ce, “Har ka manta na yi rantsuwa ba zan dauki hoto ba sai da mijin aurena”.

“To ni wane ne ba mijin naki ba? Idan har kina de shakkar hakan, ai dai aski ya zo gaban goshi.

Ba kin ce Yayanku Aminu zai dawo karshen shekarar nan ba, kuma shine ake jira kafin ayi bikin Hadiza? To insha Allah da namu za a hada, na riga na san da wuya a raba ku

Na yi murmushi annuri ya sauka a fuskata wanda har Aliyu ya lura da hakan.

Muka yi sallama da yarjejeniyar sai yazo da safe don tafiya Malumfashi. Na ce,

«Zahra’u ya yaki kai da wasikar Ibrahim?” Ta ce, “Yau kam Allah ya rufa maki asiri da ban san tashin hankalin da zakuyi da Aliyu ba, idan ya ga wasikar Ibrahim abinda zai kawo ma ransa kina yaudararsa

Ga abin da wasikar ta Kunsa.

Masoyiya ta hakika!

Ina kwana? Nayo miki wasikar ne don kawai in tabbatar maki da cewa naji dadin kalaman da kika yi mani jiya, wai saboda ni Asiya har a ki fasa zuwa Kaduna! Na ji dadi, kuma na san ina da matsayi mai girma a zuciyarki, sai dai matsalar kina gudun kada a ce kin ci amanar Aliyu, saboda Karfin imaninki. Sai nazo gobe idan kun dawo, ina gai da jama ‘ar gida.

Naki Ibrashim Tsiga

A bisa hanyarmu ta komowa gida na roki

Aliyu da mu biya gidan kakan su zahra’u a Funtuwa don su gaisa, mun sami Alhaji Amadu sai dai mai dakinsa ba ta gida ta je asibiti duba marasa lafiya.

Alhaji Amadu ya shiga dawainiya damu, ya alka daya daga cikin yarn gidansa ya sawo mana mama a wajen wani gwanin gasa nama wai shi Nasara Nama, duk da ba mu da yunwa domin mun biya Shagalinku da ke Zariya mun cika cikinmu.

Hmmm

Related Articles

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE