Trending

ALLURA CIKIN RUWA BOOK 2 CHAPTER 2 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA

ALLURA CIKIN RUWA BOOK 2  CHAPTER 2 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA

 

 

A kwana a tashi ti babu wuye a wajen Ubangli, an

Ace iyakar taku-tuka-tuk, Allah ya kaddare mu da ganin wannan rana mai cike da farin ciki a gare mu masu fitar karatun sakandire ta wannan shekara, a bisa dukkan alamu muna tare da nasara domin mun fahimci dukkan tambayoyi da a kai mana, haka nan sakamakon mu ya yi kyau matuka, idan makaranta ta yi amfani da shi wajen raba mana kyatuttuka.

A gaskiya a ture iyayena ma kawai hatta masoyana na Kara masu kwarjini na musamman a wannan rana, a dalilin bajintar da na nuna. Umar yayi amfani da kyamarar da Aliyu ya ba shi domin’ ya daukan hoto a wannan rana.

Shi Ibrahim ya sami wata kwana a baya yana rungúme da ‘yar karamar video camera, ya yi mani kaset na kaina ni kadai, na so in aika ma Aliyu shi amma saboda sanin “yan mazan nawa sai na fasa gudun kada mu yi fadan da zai tada masa hankali har kos dinsa ya raunana.

Bayan biki ya watse Mukhtar ya mai da Inna

Hafsatu da Hadiza gida, yayin da na bai wa

mahai fina Malam.Yusuf kyaututtukana Yaya

Abukabar ya goya shi bisa mashin dinsa suka nufi gida, shi Umar a lokacin. Zariya ya wuce, ni kuwa nayi amfani da wannan damar na sami Ibrahim kwance cikin motarsa ya lumshe ido, na tsaya daf da kofar motarsa na yi tafi da hannayena a hankali. Sai Ibrahim ya yi mika tare da bude idonsa, na ce, “Yallabai ba dai barci ba?”

Ya ce, “Tunani”

Na yi murmushi na zagaya na bude mota na zauna, shi ma ya tayar da kujerar da ya kwantar ya zauna sosai. Na ce,Manya kamar ku har akwai tunanin da zai shagaltar da ku?”

Ya ce, «Wallahi yau ko baccin kirki ban yi ba, a dalilin fuskantar wannan muhimmiyar rana kuma da zumudin yau gani ga sarauniyar zuciyata.

A gaskiya Asiya ina daya daga cikin masu alfahari da samun “ya kamar ki, ina ganin ‘yata ce ke ban san irin kyautar da zan baki ba”Na Ce,

• “Idan matarka ce fa?”Ya yi dariya ya ce ” Allah ya sa ki zamanto matar, amin. Amma a matsayinki na budurwata yau da za ki amshi duk irin kyautar da zan miki da na ji dadi” Na ce, “Kai ma ka san ta fi Karfina saboda haka kada ka sa ran zan amsa*Ya ce, “Kin san kuwa ‘yar karamar mota na yi niyyar saya miki”

Na ce, “Wai! Wai!! Kada ka Kara fasa wannan magana don Annabi”. Muka kyalkyale da dariya.

Ibrahim ya jawo mota muna tafe a hankali, bai tsaya ko ina ba sai a wani layi wanda na yi-mamaki ina cikin Malumfashi ban san da wannan unguwa ba, an tsara unguwar da gani ka san ba wajen zaman ya ku-bayi bane.

Ya kashe motar a daidai kofar wani katafaren gida maigadi Buzu ya mike da sauri zai bude get, amma Ibrahim ya dakatar da shi, ya dube ni yace,

“Ba ki tambayen inda zan kai ki ba?”

Na yi murmushi na ce, “Ko kusa ba ka yi mani kama da mai satar mutane ba

Ya kyalkyale da dariya ya ce, “To ga gidan su Zubaida, sai ki fito”.

Na yi masa fari da idona na ce, “Ni ko Ibrahim me zai sa kai mani haka, idan na shiga me zance ma matarka Habiba, kuma ma jama’ar gari su zagen a ce na cika zakewa daman dai ba ka da mata ne da sauki” Ya ce, “To kwantar da hankalinki babu kowa a gidan sai ‘yan aiki, su Habiba da yara suna Tsiga biki tun jiya, ba za su dawo ba sai gobe, saboda haka ki daure mu shiga”.

Na yi shiru tare da daurewar fuska, na jima a haka sannan na ce, “Yanzu kana ganin su ‘yan aiki ba za su gaya mata ba?”

Ya ce,Idan sun fada sai me zai faru tunda ba

matar banza na kawo ba, wadda zan aura ce fa, kafin ma su gaya mata ni zan gaya mata na kawo Asiya mene ne yake a rufe?”

Na dube shi duba na rashin jin dadi, na ce,

“Ni kuwa a gaskiya idan ni ka yi ma hakan wallahi ba zan so ba ko kadan, raina zai mugun baci, saboda al’adarmu ta Hausawa ina gain kamar da raini, daman ku maza halinku ke nan, idan kun ga mace na da hakuri komi kuka ga dama sai ku yi mata, amma ku nufin ku wai ba ta damuwa ke nan”.Shima a nan ya jima bai ba ni amsa ba, na san bai ji dadin rashin shiga ta gidansa ba, amma kuma ya san abin da na fada gaskiya ne, saboda haka ya juya muka nufi gida.

A bisa hanya ne ya rika ba ni labarin ya yi sallama da aikin gwamnati yanzu kasuwanci zai fara a halin da yake ciki ma zai je Western Germany zai sawo wa jihar Sokoto wasu injinan gidan ruwa,

Hmmm

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE