ALLURA CIKIN RUWA BOOK 2  CHAPTER 20 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA

Sai da muka yi sallar la’asar sannan muka bar

•Funtuwa dauke da sakon Alhaji Amadu zuwa ga Aminun Zahra’u a can London, domin jirgin farko da Aliyu zai tuka mai zuwa Ingila ne.

Mun idar da sallar isha’i muna jarraba rikodar da Aliyu ya kawo mani, sai na ce, “Zahra’u yanzu kin ga wahalallan mutumin nan Alhaji Ibrahim”

Ta yi-tsaki tace, “Bana son gulma ki rika sakarwa “bawan Allah fuska a bayan idonsa kina tsanarsa. Ni ko yazo ba zan raka ki ba gara in zauna mu yi hira da Inna Aisha. Ke na manta ina da aikin yi zan fara rubutawa Darling Aminu wasika har sai ranar da Aliyu zai tafi zan gama, ba ni takarda da

“biro na fara’

Na ba ta sannan na nufi dakin Inna, na same su suna duba dawainiyar da su Mama Inki su kai ma Zainab.

Kwana uku da muka yi a Malumfashi kafin mu wuce Katsina suna cikin ranakun da bamu iya mantawa dasu, ka’ida ne duk maraice Aliyu yazo mu fita yawon yada rana, ko mu yi Kwallon tebur, duk dare kuma muna tare da Ibrahim, yayin da Ibrahim ke ta kai kawon tafiya Ingila da habiba, mu kuma Aliyu ya debe mu zuwa Katsina.

To da yake iyayen mahaifina sun rasu, amma akwai dangi,daga dan wa da dan Kani sai ‘ya’ya

Saita dubi Zahra’u ta ce, “Kin san Uwani hidimar da dan uwanki keyi duk saboda wannan kawar taki ne fa”

Na ce, “tab! Gwaggo don Allah ya rufa mana asiri tana da miji dan ‘uwanta ne ma”.

Gwaggo ta ce, “Gara da kika gaya mani da an yi danyen aiki”

Na ci gaba da cewa, “Kin sani ma Gwaggo tun ranar da aka haife ta ya nuna yana sonta aka ce an ba shi, amma sai in ta girma ta amince”

Sai Gwaggo ta yi murmushi ta ce, “Ai ke ma

Uwani ina ganin da alama kin dace da masoyi na kwarai, domin na ga fuskar nan tasa cike take da kaunarki, Allah ya sa ayi a sa’a”

Zahra’u ta ce, “Amin”

Ni kuwa na sunkuyar da kai kasa na nuna alamun jin kunya.

Hadiza ta sami hutun kwana biyu sai ta kasance tare damu a Galadanci, cikin kwana biyu mun kai ziyara wurare da dama, har Maradi mun je da Hadiza, Zahra’u da Aliyu da Mukhtar dani, haka nan mun je Daura Rijiyar Kusugu.

Bani mantawa ana gobe za mu gama hutunmu a Katsina da la’asar lis na yi baccin rana, yayin nan Zahra’u ta bi Hadiza aikin yamma asibiti, sai na ji Gwaggo Juma na tadani a hankali.

“Ke Uwani ki tashi mana tun hudu da rabi yaron nan Aliyu yake jiranki”

Na tashi na ce, “Gwaggo ban san zai zo ba, na dauka sai da daddare yadda ya saba”.

Ta ce, “Ga shi can Kofar gida shigowarsa ta yi uku, idan ya leko ya ga ba ki tashi ba sai ya koma”

Na zauna bakin gado ina susar kai irin na

Ya ce, “A’a, babu komi, ai ba ki da laifin don ba mu yi zan zo ba, yanzu ma wani abokina ne wanda na taba baki labari Lawal Soja, shi ne yazo hutu tare da iyalinsa daga Legos, amma jibi za su wuce Indiya, shine na ga ya dace ku gaisa”Na ce, “Oh-ni-‘yasu! Ga su Zahra’u basu

Sai nan da nan ransa ya baci, a bisa abin da na fada, sai ya yi mani wani irin kallo yace Uhm!

Abin da kika ga ya dace shi za ki za6a, ina cikin mota ina sauraron ki nan da minti goma”.

•Ya duba agogon hannunsa sannan ya ce,

“Idan minti sha biyu ya yi ba ki fito ba zan ta fi*

Na yi shiru ina tunanin wai ni ba fitar daga ni sai shi ne bani so ba, illa ina gudun bata sunan mahaifina a cikin danginmu na nan Galadanci, saboda yawancinsu suna zargin Babana a kan ya ki mani aure alhali ina da masoya birjik, kuma a wannan lokaci yanzu duk ‘yan dattawan unguwarmu suna nan zaune bisa siminti, yayin da wasu ke kishingide bisa dakali suna shan iskar yammaci.

Gwaggo Juma ta shigo tace, “Ya ya na ga fuskar yaron nan kamar a bace, ya shigo da fara’arsa ya fita a fusace?”Na ce; “*gwaggo rabu da shi kullum shi sai ya rika kawo mani wasu salo kamar na Turawa, kuma kin san halinmu da al’adunmu na Hausawa, wai yanzu gidan abokinsa zai kai ni don na jira isowar su Zahra’u shine ya yi fushi”.

Ta ce, “A ‘a, Uwani ba ayin haka, mutumin da ke sonka da aure da an ganshi za a gane, mai sonka da aikin banza kuwa ba zai yiwu ya shige ma iyayenka ba. Kuma idan don maganar dattawan

unguwar nan ne sai dai ki yi ta yi, ki tashi ki shirya ku tafi”. Na shirya na fita sanye da leshi mai ruwan hoda, na yafe kaina da dan shara-sharan gyale shima mai ruwan hoda, daga bakinsa an yi cin bakin leshi, sai jaka da takalmi wadanda suka ciza. Na riska takawa a hankali kamar hawainiya.

A lokacin har ya tayar da motarsa sai ya hango ni ta madubin mota, ya yi ribas yazo daidai inda nake, sai na kama kofar baya zan bude, ya danna mani harara ya ce, “Ke idan ba kya shiga gaba a bar tafiyar”

Na dan yi jinkiri sannan na shiga gaban, na yi tagumi na Kura ma hanya ido ta gilashi, shi kuma ya mayar da hankalinsa ga tukin mota. Haka muka yi tafiyar kowanne zuciyarsa a kule.

Maigadin gidan Lawal Soja ya taso da sauri ya danna karfe get ya bude, mun shiga ya tsayar da motarsa, ya zagayo ya bude mani yayin da ya amshi jakar hannuna ya rataya, sannan ya riko mani hannu amma duk abin nan da Aliyu ke yi bai dube ni ba.

Sai na rika Kokarin amshe hannuna, ya dubi fuskata a cikin hikima da dabara yadda za a dauka duba ne na soyayya, amma a fakaice ni na san duba ne na gargadi, ya nuna mani idan na yi wani abu zai yi abin da ya fi hakan.

Hmmmm

Related Articles

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE