ALLURA CIKIN RUWA BOOK 2  CHAPTER 22 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA

Saida kika gama yangarki kika fito sai ma kika Kara neman wani dalilin da zaki bata mani don dai in ji haushi a fasa tafiyar, sai kika yi mani abin da baki tada yi mani ba, inda kika bude gidan baya za ki shiga. Na uku wai don cin fuska har za ki ce direba ya kai ki, alhalin nine na kawo ki, me kike nufi in ban da son ki bata mani rai.

Amma’ duk da haka maimakon ki tambayi dalilin bacin ran da nayi sai ma kika tsiri fushi”

Sai ya yi shiru da yin magana, nima ban daga kai ba, kazalika tunda ya fara maganarsa ban ce uffan ba, domin na san a yau Aliyu yafi ni gaskiya, sai dai kuma ya ya zan yi ke nan? Can ya ja dogon numfashi ya ce,

“Kin yi shiru?”

Na ce, “To Aliyu me kake so in ce? Laifi ne na riga na yi, babu abin da zan ce illa ka yi hakuri, tunda da ku maza da hakuri aka sanku, kuma ance ma mata ba a biye mana, idan aka nemi a mikar damu, karshe mu karye gaba ki daya. Ina mai Kara maimaita. maka ka yi hakuri”

na yi masa wani irin kallo cikin rangwada

*Ka hakura ko Aliyu?”

Kyalkyalewa da dariya yayi  ya ce, “Na daure  kin riga kin karance ni bana son in,, wallahi duk da kinyi ado na azo a gani a yaba kada ki so ki ji yadda zuciyata tayi bakikkirin ganin kin fito cikin fushi ba kamar yadda kika saba mani ba. Don Allah a rika rangwanta mani”

Sai ya nemo hannuna yana sumbatar tsakiya, tare da ‘yan surutansa yana Kara gargadina da kada in saka rayuwarsa cikin wani hali. Wannan ya rinka ba ni tausayi a kan son da yake mani, daga nan na tabbatar wa kaina cewa lalle son da Aliyu ke mai kishi hudu na dauka a cikin kashi goma sha biyu

Ya yi kwana muka koma shagon sayar da littattafai na zabi wadanda za mu yi arofani daso a wannan shekaras, Aliyu ya biya kudin muka fito, sai kuma ya ce mani, yanzu ne suhadiza ke tashi aiki bari mu je mu taho da Zahr a’u. Na ce, “To

Muka hango su Hadiza da kawayenta suna ma Zahra’u rakiya, domin tsakanin Galadanci da asibiti babu nisa, muka dauki Zahra’u, Hadiza tace, tananan zuwa da safe tunda ba aikin safe take yi ba.

Muna shirin bacci ne Zahra’u ke ce mani,

“Amma gaskiya Asiya tunda na shiga jami’ a ban taba hutu mai dadi irin wannan ba, na kuma yadda Yan karin magana da suka ce, Katsina dakin to lalle na ya kara da karamci”

Na ce, “Ni kaina ban taba hutu mai dadi ba

Irin wannan, amma nasan ni har da karin abu biyu,

wato ga Aliyu masoyi ga Zahra’u babbar aminiyata”

Na dube ta ina dariya ita kuma ta dube ni ta

ce, “Kuma Gwaggo Juma tana da zumunci, dubi irin

dawainiyar da take damu ita da ‘ya’ yanta, kamar za

su bamu naman jikinsu domin tsananin kulawa,

kuma yadda ta rike hadiza garin kai ka ce uwa daya

uha daya 

Na ce, “Ai Gwaggo Juma tayi zarra wajen

Zumunci. Kin san wani abu kuwa, su Babangida da

Bilkisu da Mauwa ba ‘ya’yanta ba ne rike su tayi nima taso ta rike ni na ki zama, wallahi Allah bai taba ba ta dan kanta ba, al’amarin na su Gwaggo

yana da ban sha’awa, Allah bai basu dan kansu ba

amma ya hore musu zuciya mai kyau su rike da

tamkar su suka haife shi

Zahra’u abin ya dade mata a zuciya don nace

su Babangida ba ‘ya’yan Gwaggo ba ne,

Mun iso Malumfashi da misalin karfe shida

. Kwananmu biyu da dawowa, Zahr a’u ta

Shirya

komawa Kaduna, Babana ya sai mata zabbi da man shanu, ita kuma Inna ta sai wa Gwaggo

Karima kuka da kubewa zuwa daddawa. Ita kuma

GwaggoJuma daman ta saya mata su tandu da

mafici da ‘yan tarkace irin na Katsina, sai dabino da kilishi. Aliyu ya bai wa mota ya mai da ita

“Yar Zaina ta yi rakiya.

Washegari Aliyu ya nufi Kano inda zai fara

aikinsa, har ya yi ma Zahra’u alkawarin zai yi ma

Aminunta waya su hadu a filin jirgi na Ingila domin

amsar sakon ta da na Alhaji Amadu.

Haka dai al’amura su kai ta gudana cikin jin

dadi da kwanciyar hankali a gida da kuma

makaranta, mun zama son kowa kin wanda ya rasa.

Wata tara kacal ya rago mani in kammala

karatuna, cikin nasara da sa’a da kuma koshin lafiya dukkan abin da dan Adam ke so a wannan matsayi da nakarance na samu, domin tun da Aliyu ya fara fita kasashen waje bisa aikinsa komi na amfanin dan Adam a kasashen waje yake sawo mana, hatta maganin wanke hakora bama amfani da na wannan kasar sai na waje.Ita ma Zahra’u tunda Aminunta ya gane

•Aliyu ya rinka yo mata aike a kai a kai, na sutura zuwa abin amfani, komi kam sai dai a Cara ganinsa a wajenmu, in dai na yayi ne.

•Yaya Abubakar a wannan lokaci ya gama hidimar kasa a inda aka tura shi jihar Legos, daga nan ya komo aiki a Funtawa a bankin da yake aiki tun kafin ya shiga jami a wato U B.A. Suna bashi albashi daidai yadda ya kamaci ma’aikaci Kumadaidai gwargwado ya dauke ma iyayenmu yawancin nauyinsu kasancewar bashi da iyali balle dogon buri abin nufi anan ansan dan zamani da shaye shaye da makamantansu to shi kam Allah ya shirye shi

Hmmmm

Related Articles

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE