ALLURA CIKIN RUWA BOOK 2 CHAPTER 23 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA
Aminun Zahra’u ya dawo gida, amma kafin ya taho sai da Baba Sule ya aika masa da kudi wadanda aka ce ya yo odar abin da yake so a sa masa a gidansu shi da Zahra’u, kamar su gado da kujeru da tarkacen kicin da kayan kyale-Kyalenmu na mata.
Muna samun hutu wanda daga shi sauranmu wata shida mu gama karatun jami’ a, daga nan muka nufi Kaduna saboda dokin auren Zahra’ u.
Daga ni har Zahra’u babu wadda ta huta domin dai mu ga mun Kayayar da wannan biki. An daura aure ran daya ga watan yuni na ranar wata asabar a kofar gidan Baba Sule.
Mun shirya gagarumar liyafa bayan daurin aure. Mama Inki ta shirya mana abinci iri-iri wanda ta bai wa wani Kasaitatten hotel mai suna NANEL kwangilar dafa shi. Ma’aikatan hotel din su ne ta sake hayarsu don su shirya su gabatar da komi ta fannin raba abinci da tamaka wa jama’ar da ta halarci liyafa jin dadinsu.
Idan ka ga tsarin kwalliyar da muka yi ma wannan liyafa gaskiya za ku yaba. A nan mai daukar bidiyo ya ce, “Kowa ya ga kura ya san ta ci akuya wace ce amaryar a cikinku?” Zahra’u ta tsagalgale ta ce, “Mu duka”. Farin leshi ne muka zuba mai cike da adon kananan dutwasu masu daukar ido, tare da ratsin zare mai ruwan gwal, sannan an manna masa wani yadi siliki mai kalar baki. Takalmansu sun kasance masu ruwan gwal amman rufaffu, hade da jaka ita ma mai ruwan gwal, mun je wajen gyaran gashi inda a kai mana komi iri daya.
Daurin dankwali shima abin a tsaya ayi kallo ne. An shirya mana tebur na musamman daga ni sai Zahra’u da Aliyu da Aminu. ‘Yan makarantarmu sun hallara har da na wasu makarantu, inda duk ka gilma ko ka yi wani motsi mai karfi masu daukar hoto ne.
An kammala wannan liyafa misalin shida da rabi, mun isa gida shi ma a shake da jama’a. Da kuma misalin Karfe goma na dare muka nufi Dubar Hotel inda abokan ango suka shirya mana liyafa.
A nan ne Aminu ya tashi ya yi jawabi, inda ya dauki alkawari zama da matarsa bisa sharuddan da suka rataya ga ma’aurata. Ni kuma aka nemi da in kara dan gajeran bayani a bisa alkawarin da ango ya уi
Na ce, Na yi imani ya sami mata mai cika
alkawari da rikon amana, wanda ina tabbatar masa ba zai tada dana sani ba a rayuwarsa. Zahra”u tasa ce ba na tsammanin akwai wanda zai sami dan masauki komi kankantarsa a zuciyarta
Sai aka dauki tafi gaba daya raf-raf-raf.
Bayan an yi tsit na ci gaba da jawabina ina mai cewa, “Kuma daman Annabi Muhammadu (S.A.W) ya ce, ana auren mace don abubuwa hudu, na farko don iliminta, wato na addini. Na biyu don kyawunta, sai na uku don dukiyarta, na hudu don darajar da
Allah ya yiwa iyayenta.
To a takaice dai jama’a duk wanda ya dubi
Zahra’u ya san ta mallaki duk wadannan abubuwa da ake so ga mace za a aura.
Annabi Muhammad (S.A.W) a wata ruwayar ya karfafa cewa, a auri mace wadda ta fi ilimi da hali mai kyau, saboda ana zaton albarka a yin hakan.
To a zaman da nayi da Zahra’u tana da iliminta na addini daidai wanda ya kamata matar kwarai ta samu”
Sai na dubi sashen abokan ango, sannan na dubi Aminu na yi dan murmushi na ci gaba da cewa,
“Kila ma sai Zahra’u ta koyar da Aminu
Duk wurin aka dauki sowa da dariya ana a°a, ba su yarda da wannan ba saboda shima Aminu malami ne a iya saninsu.
Shi kuma Aminu ya waiwaya yana duban
Zahra’u, amma ba zan iya tabbatar da tsokanar da
– yake mata ba kan hadin da na yi musu. Da kura ta nace, “To Zahra’u daga yau
Aminu dai ya mallake ki, abin da nake mai Kara ba ki shawara ki tareraye shi da kyau kada in ji an ce, wata mace daban ta sami hanya ta shigo cikin gidanku wai da sunan an yi miki kishiya, idan har haka ta faru ke zan ba laifi ba Aminu ba, saboda abin da zan dauka ba kya kula da shi, tunda duk wanda ya dubi tsawon lokacin da Aminu ke son ki ba zai yiwu ba a ce daga baya zai iya canza ra ‘ayinsa, in dai ba ke kika bullo masa da wani hali na daban ba.
Kai kuma Aminu na baka amanar Zahra’ u,
Allah ya ba da zaman lafiya, amin.”. Wannan jawabi muna yinsa ne cikin harshen Turanci, saboda falon ya Kunshi tantagaryar ‘yan boko ne maza da mata.
Bayan an gama ‘yan tande-tande da tsotse-tsose sai aka bai wa shahararren makadin nan Garba®
Wazirin Sufa fili don ya cashe, sannan makadan Yarabawa da haka dare ya tsala wajen misalin uku na sulusin dare sai aka umarci Mukhtar din Hadiza da ya rufe taron da addu’ a.
Da muka yi sallar asubahi bamu tashi bacci ba sai sha biyu na rana. Sannan da la’asar aka fara watsewa.
Direban su Mama Inki ya mai da su Inna
Malumfashi, ni da Hadiza Mukhtar ne ya dauke mu shi Aliyu Kano ya koma. Ibrahim yazo muna hira na yi riga malam masallaci, domin na yi masa laifi na kin yarda ya je wajen daurin auren Zahra’u, abin da nake gudu ya faru, wato Ibrahim ya matsa mani sai in raka shi Zariya in hada shi da telolina domin ya kai dinkin Habiba da yaransa, na nuna masa bana son zuwa, amma sai ya nuna mani bacin ransa.
A bisa dole na hakura na raka shi ni da
Zainab. Mun dawowa bayan la’asar na sanya kafa zan fito daga motar Ibrahim sai muka ji tsayuwar motar Aliyu.
Ibrahim ya fito da sauri ya mika ma Aliyu,hannu amma shi Aliyu ya ki sai ma ya shige cikin zauren gidanmu abinsa. Na rude na rikice tare da zullumin me zai faru, Ibrahim ya rifa mani dariya, ya ce, “Yau ina tausayin wata yarinya, domin Gadanga Kusar yaki ya hau taken nasa” Nidai na rasa abin yi, na dafa kan mota na yi shiru, da dai na san babu sarki sai Allah na yi sallama da Ibrahim na shiga zaure, Aliyu na ta cika yana batsewa.Zainab ta gai da shi ya amsa mata ta shiga gida, nima na gai da shi kallo ma ban ishe shi ba, muka yi shiru na tsawon lokaci.
Hmmm