ALLURA CIKIN RUWA BOOK 2 CHAPTER 3 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA

ALLURA CIKIN RUWA BOOK 2  CHAPTER 3 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA

 

 

 

amma ba zai fi sati biyu ba. A nan na yi masa fatan alheri.

A gida Inna ta nuna mani farin cikinta ainun, ta sa mani albarka tare da kyakkyawar addu’ar Allah ya hada ni da miji na gari. A zuciyata na ce, amin.

A wata rana muna hira da Hadiza, sai ta ce mani, “A bisa gaskiya Asiya na fara jin tsoron Baban nan nawa, ta wani gefe kuma ina jin tausayinsa”

Na dube ta na ce, “Tsoro kamar ya ya?”

Ta ce, “Na ga ya yi zurfi da al’amarin soyayyarku, kuma na lura mutumin yana da wayewar kai da yawa, ina tsoron kada. ya yi ma Aliyu barna saboda ya iya jan hankalin “ya mace kwarai ainun, haka kuma ina tausaya masa yadda ya dauki son duniya ya dora maki, a yau aka wayi gari an’ daura aurenku da Aliyu ban san irin yanayin damuwar da zai shiga ba, sai dai a ce Allah shi kyauta”

Muka ce, “Amin”.

Na yi shiru ina tunanin abin da Hadiza ta fada wanda na san lalle gaskiya ne, na nisa na ce, «To ni yanzu ya ya zan yi ba tare da na batawa dayansu rai ba?”

Azumin matan Ramadan ya Kama da  kwana

.shida sai ga Baba Suraj da su Hajara sun zo

tafiya da ni Kaduna. Baba Suraj ya ce, “Asiya wannan aike tun daga Amerika aka ce inz in dauke

ki zuwa Kaduna in ji Oga”.

Na ce, “A’a, Baba ni dai zan zo saboda su Hajara da sauran yara”. Ya ce,, “To na sanar da shi yadda kika ce, ince ya sake damara kila wani ya yi masa over

taking”Na ce, “Lah! Baba rufa mani asiri ina tsoron fushin Aliyu”

A wannan dare da misalin tara da rabi Baba

Suraj ya buga ma Aliyu waya, amma ba shi a gida sai wani mutumin Jos da suke zaune tare da shi ya

dauka ya shaida mana ya fita, amma in ya dawo zai

shaida masa.

Raina ya baci, na yi tunanin ko hidimar me

Aliyu ya fita yi? Nan da nan kishi ya turnike ni na shiga daki na kwanta, kaina ya rinka sara mani.

Ina nan kwance sai misalin sha daya da rabi

Mama Inki ta leko ta ce, in je karamin falo in dauki wayar Aliyu. Na yi zumbur na mike na nufi falo na dauka muka gaisa, na yi masa barka da shan ruwa, shima ya yi mani tambayar ya sakamakon da na samu na jarrabawa.

Da na ba shi bayani ya ji dadi Kwarai, yace

“Ya ya nake jin muryar taki kamar marar lafiya? Ko dai azumin ne?”

Na ce, “Wallahi babu ko daya”.

Ya ce, “To da magana ke nan, ko na yi lai fin da bani da masaniya ne?”

Na yi shiru. Sai ya gaji ya ce, “Asiya” Na ce, “Na’am”

Ya ce, “Me ya faru don Allah?”

Sai na tuna a waya muke kuma daga can kololuwar duniya, sai na daure na ce, “Aliyu ina ka je dazu ba mu same ka a gida ba?”

Ya Kyalkyale da dariya kamar zai bare wayar, ya ce,

“To daga yau kada ki Kara cewa na fi ki kishi

Asiya tace, “Har yanzu ba ka amsa mani tambaya ta ba” Ya ce, “Kin san dai azumi muke yi ko?”

Na ce, “Eh”

• Ya ce, “To wallahi asibiti na je gai da wani abokina mutumin kasar Masar ba shi da lafiya, abin da ya sa abokin zamana bai maki bayani ba, ba shi gida lokacin da na fita, kin yarda ko?”

Na yi ‘yar dariya na ce, “Na yarda Aliyu, da har na damu na yi zaton an fita rawar dare ne da sabuwar masoyiya”

Ya yi dariya ya ce, “Wai ni me kika dauke ni ne, ba ki san ni Uszat ba ne?”

Na yi dariya na ce, “A garin da Ustazai suka yi kadan ko, kamar nan America?

Ya ce,Kin dau bashin wannan, , za mu hadu

kin san wanda kika gaya ma haka Na ce, “Ina jiranka anjima cikin baccina’ Ya kyalkyale da dariya ya ce, “Kin san ba ayi mani gatse fa”

Na ce, “Sai ka zo amma kafin a yi sahur kada ka makara don Allah”Ya nisa ya ce, “Eye!”

Kwanci rashi har an fara hidimomin sallah, idan har na zayyana muku irin suturar da su Mama Inki suka dinka mani abin sai ya zama kamar ina tsari, ni kam a wannan zamani sai hamdala don ina cikin jerin ‘yan mata masu Koshin sutura, suturar kuma ta gani ta fada. Hatta Kanwata Zainab an yi mata dinki kala uku masu tsada.

Amma cikin ikon Allah duk da yawan suturan da na samu ga abincin sallah kala-kala, ga uwa uba wayar Aliyu a kullum, sai na sami kaina na fi kwadayin gida, a bisa yadda muka saba shagalin sallarmu, za mu kasance a kicin da ni da Inna muna tuyar funkasu, yayin da Zainab ke mika ma makwabta, su Yusuf da. Yaya Abubakar suna shigo mana da labarin abin da ke faruwa cikin gari, idan azuhur ta yi Inna Hafsatu da Hadiza su zagayo zuwa cikin gidanmu kowanne ya yi ado daidai shi, mu kan zauna tare da su ana hira tare da ban dariya, saboda Inna Hafsatu mace ce mai son ban dariya, don haka muka fi sakin jiki da ita, sai ya zamanto Hadiza ce kuma auta.

Ranar wata Laraba a cikin doki da zumudi na buga ma Aliyu waya, bayan mun gama gaisawa na shaida masa yanzu zan tafi Malumfashi domin jarrabawarmu ta shiga jami’a ta fito. Ya tambayan wace jami’ ar za ni? Na shaida masa zan yi shawara da mahaifina, amma ina jin dai Zariya za ni, saboda su ne suka ba ni kos din da nake so wato lauya: Ya ce, “Sauran me suka ba ki?”

Na ce,Jami’ ar Sokoto sun ba ni a fannin

famasi, a jami’ar Bayero ta Kano sun ba ni a fannin

Mass: Communucation

“A takaice dai Zariyan za ki?” In ji Aliyu.

Na amsa da cewa,Ina kyautata zaton

hakan”

•Ya ce, “Asiya ba ni da rabi abin da kike shi nake so, sai dai yaushe zan sami bayanin in kika je ke nan?”

Na ce, “Idan Zariyan ne bayan sati daya da fara karatu na zanzo in gaya maka

Sai ya fara ba ni shawarwarin karatun  jami’a ba irin na sakandire ba ne, yanzu kina da ‘yanci fiye da yadda ba kya tsammani, ki yi taka tsantsan da

‘yan matan jami’a da samari kada su juyar maki da ra’ayi, za ki same su masu saukin kai da taimako.

Don Allah ki kama kanki kamar yadda na san ki, kada ki yarda wani saurayi ya canja maki tsarin rayuwar da muke ta shiryawa.

Na ce masa, “In Allah ya yarda hakan ba za ta faru ba, kada ka ji shakkar komi”. Na yi murmushi bayan na aje wayar, nace Aliyu da kishi kake,

‘ wannan shawarar da yake ba ni ai da ya bi ta abin dake zuciyata da duk bai jawo wa zuciyarsa rashin yardar ba, amma Allah ya mai do shi lafiya

Hmmm

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE