ALLURA CIKIN RUWA BOOK 2 CHAPTER 5 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA
Ina rungume da Zubaida bisa cinyata ina girgiza ta a hankali har bacci ya dauke ta cikin minti sha tara, sai Ibrahim ya ce, “Bari in amshe ta kada cinyarki ta yi sanyi”Na ce, “Babu komai
Ya dai nace na kiya, har ya taso ya zo inda nake ya sunkuyo zai dauke ta fuskokinmu suka yi daf da juna, hucin numfashinsa ya rinka sauka mani a jiki, yayin da hannayensa suka ratsa sassan jikina.
Sai na ji ya dauki rawar jiki, ni kuwa sai na
Kara makale Zubaida, a lokacin ne muka hada ido da shi, na yi masa wani irin kallo, shi kuma ya yi mani wanda ya nuna mani ya shiga wani rikici wanda ban so ba ya koma ya zauna.
Daga ni har shi mun dauki lokaci mai tsawo babu wanda ya ce uffan, zuwa can ya nisa ya ce,
“Asiya”. Cikin wata irin murya mara nutsuwa na amsa,
“Na’am Ibrahim”
Ya sa hannu ya dafe kansa sannan ya ce, “Me yasa kike kashe masu kudi haka? Haba Asiya ki daina wahala haka, kaunar da kika nuna masu ma ta isa”
Na ce, “Ibrahim babu maganar wahala, idan ban da hali da ban yi ba”
Ya ce, “To Allah ya saka da alheri. Asiya na so kin ban dama in fito a yi mana baiko kamar Hadiza da Mukhtar, zan iya jira har ki kare jami’ a Sai na yi murmushi na nisa na ce, “Wai yaushe ne tafiyar ka Japan?’ Ya ce,
«Sati mai zuwa in Allah ya yarda”
Na ce, “Lallai kasuwanci ya mika, Allah ya yi taimako”
Mun yi hira mai tsawo,amma bai sami hadin kai na ba, ya gaji ya hakura, ya ce,Zan saka maki ido
Asiya inga iyakar gudunki”
Washegari da misalin sha daya na safe na gama wanke ma Zubaida Kunshi ina gyara mata akaifa, sai muka ji sallama daga bakin kofa, na juya na amsa muka yi ido hudu da wata doguwar mata fara irin matan nan wanda fari ya rufa ma muninsu asiri.
Sai na ji Zubaida ta ce,Lah! Mamana” . Sai na fahimci
lallai na gane Habiba ce, na tashi da sauri na shigar da ita dakin Inna suka gaisa, sannan na kaita dakina, na kawo mata kayan motsa baki. Ta ce,Asiya uwar ‘ya’ya kin sha bari dai”.Na ce,Kai ai ba su matsala wallah;*
Ta saka biskit a baki ta fara kallon album, sai ta daga kai ta dube ni ta ce, “Wane ne wannan kuma Asiya?” Na duba na yi murmushi na ce, “Yayana ne”
Ina dariya. Ta ce, “Kai wannan Yaya naki kina dai ji da shi, ina sunan shi?”Na ce, “Aliyu”. Ta ce, “To ina na maigidan namu?”Na ce, “A’a, wannan kuma ai manya ne, sai kin kawo naki sai in hada ku
Na lura tana jin dadin irin hirar da muke yi, gaskiyar Ibrahim kishin Habiba da sauki, ni a lokacin sai ta rika ba ni tausayi.Bayan mun gama hira na shirya Zubaida za su tafi, a nan ne Habiba ta miko mani wata jakar leda ta ce, “Asiya Ibrahim ya ce mani za ki tafi Zariya makaranta, to ga wanna ki yi tsaraba, kuma muna Kara godiya a bisa hidimar da kike ma yara, Allah ya barmu tare, Allah kuma ya sa rakiya ta yi nisa”
Na ce, “Amin Na rakata dakin Inna don su yi sallama, Inna ta bai wa Zubaida gyada soyayya da aya. Na yi masu rakiya Har gindin mota, abin mamaki sai na sami wata yar Honda Civic a madadin ta Ibrahim, Habiba ta fiddo ‘yan makulle ta bude motarta ta tayar ta yi ribas gwanin ban sha’awa, muna daga ma juna hannu har suka bace. Na duba kayan da Habiba ta kawo mani, sai na ga saitin kayan shafe-shafe ba Beauty fair dasu under wear zuwa agogon hannu.
Ran dana sauka a Zariye naje jami,ar Ahmadu
Bello na sami ‘yan matsaloli kadan, amma
cikin ikon Allah a kwana na biyu komi ya
daidaitu. Gidanmu Amina Hall daki na shida tare muke da wata Mary John ba ta ko jin Hausa, kuma
halayyarmu ba ta zo daya ba, saboda ta yi tsauri
wajen rikon addininta kamar yadda nake ji da nawa
addinin. Har ma ba ni samun isasshen bacci. saboda
yawan wakokin da take yi cikin dare na addininta, ba ta da son magana, kusan ma in ce gaisuwa kawai
kan hada mu da ita.Ban sami zuwa Kaduna ba sai da na yi sati uku cur, shima din ran Asabar na je na dawo ranar Lahadi. A motar da na shiga Allah ya hada ni da
wata tsaleliyar yarinya wadda saboda kyawunta da
irin shigar da ta yi har sai na riga jin ko hira ban isa
ta yi dani ba, bayan gaisuwa da muka yi sai ta koma
bisa karatunta na wani Novel mai suna ‘ if tomorrow
come”, ni kuma ina karatun wata mujalla mai suna
Hotline da na saya a nan tashar motar Zariya.
Zuwa wani lokaci sai wannan kyakkyawar
yarinyar wadda ke zaune gefena ta dan rufe littafinta ta mai da fuskarta jikin taga tana kallon wata mota da ke kokarin shige mu, daga nan ta dan juyo wajena kadan sai wani labari ya dauke mata hankali a mujallar da ke hannuna, muka dubi juna muka yi murmushi, ta roke ni idan na gama za ta dan duba.
Na ce, “Babu damuwa”
Bayan ta gama ne muka fada ma juna sunayenmu, tace,Sunana Zahra’ u Ahmad”. Nima na gaya mata nawa.Cikin dan lokaci sai kauna ta shiga tsakaninmu, muka sami kanmu da bai wa junanmu labarai.
Ta ce, “Kaduna za ta gidan iyayenta”. A nan muka gane gida daya muke a Amina Hall, ita shigar
• bana ce kamar ni. Na bude jaka na fiddo mata ledar aya muka rika ci muna hira.
Zuwa can yaron mota ya nemi mu biya kudinmu, Zahra’u ce ta biya mana, na yi mata godiya. Mun isa Kaduna muka yi sallama da kulla alkawarin za mu nemi juna a makaranta, muka nemi tasi wadda za ta kai mu inda za mu.
Na isa gidan su Mama Inki bayan sallar azuhur, su Ummi suka fara tsalle da murna da ganina, na tambaye su ina Mama Inki, suka ce tana bacci. Nima sai na watsa ruwa na yi sallah.
Hmmm