ALLURA CIKIN RUWA BOOK 2 CHAPTER 7 BY BILKISU S. AHMAD FUNTUA

Na ce, “Domin Aliyu idan akwai abin da ya fi aiki a shirye nake in maki”.

Da ta gama kallo na fiddo dan farin gyalena tare da turaren Beauty fair na fesa, na kuma fesa ma Zahra’u, sannan muka doshi sashen maza wajen Yaya Abubakar.

A nan muka yi karo da wani abokinsa ya shaida mana Abubakar ya sami sauki yana can filin wasa suna kallon kwallo. Muka yi godiya muka nufi inda ya yi mana kwatance.

Su Yaya Abubakar na kwance bisa ciyawa,

• abokansa na zaune muka yi musu sallama hade da gaisuwa, sannan muka zauna.

Zahra’u ta ce, «Yaya Abubakar ya ya jikin naka? Ko da yake da alama yanzu lafiya lau”

Ya yi murmushi ya ce, “A’a, yanzu kam jiki ya yi kyau, bai da wata matsala sai ta karatu da aka barni a baya, amma insha Allah komi zai daidaita”.

Sai ni Asiya na ce, “Yaya Abubakar ga fa

“Zahra’u, ita ce Kawar da nake ji a jilkina tafiyarmu za ta zo daya in Allah ya yarda”

Sai ya dan waiga ya dubi Zahra’u, ya ce, “To Allah ya barku tare, sai dai shi zaman abota dan hakuri ne da kuma Kin daukar jita-jita, in kun biya ma ‘yan gulma yanzu Kauna ta koma fada, saboda haka ku ji ki dauka sai ku ga an saka maku ido, Allah ya raba mu da

‘yan tsegumi, amin A nan dai muka kai lokaci mai tsawo muna hira da abokan Yaya Abubakar har sai da aka tashi kwallo muka yi sallama.

Ita kam Zahra’ u ta yi sa’ar abokiyar zama wata

Bayeraba mai suna Musuli Shehu, akwai ta da son ban dariya. Ganin haka fa na ji bani da sha’awar komawa dakinmu, na saki jikina sosai, in ka ganni a dakin su

Zahra’u kai ka dauka mun shekara fiye da daya.

Kwanci tashi yanzu ni da Zahra’°u sai ka ce ‘yan biyu, babu abin da ke raba mu daga barci sai shiga aji, mun kasance ba mu iya komai sai tare da junanmu, sunanmu ya fara fice a mazauninmu na Amina Hall.

Na tattara duk abubuwana na mai da dakin su Zahra’u.A cikin watanmu na hudu a makaranta aka fara jarabamu a bisa abin da aka koya mana, sai da muka gama ana gobe za mu gda muna kwance bisa gadon Zahra’u da rana bacci na kokarin dauke mu kafafuwanmu na harde da juna, sai na ji Zahra’u ta ce,

“Asiya kin yi bacci ne? Na ce,

“A’a, Zahra’u wani abu ne?”

Ta ce, “Asiya ban taba yin wata kawar da nake kauna a zuciyata daya irin ki ba, wallahi yadda nake jin ki a jikina har ba na son zuwa gida gobe, kin kuma san ko banza na dade rabona da iyayena”

Sai na sa hannuna na rufe mata baki na ce,

“Haba Zahra’u ke ma kin san ina Kaunarki fiye da yadda ba ki zato, yadda kika ce ba ki son zuwa gida domin ni, to nima hakan. Na san na shaku da Hadiza ainun, sai dai ita Hadiza kin ga mun zama “yan’ uwa ni da ita ba kawai kawance ba, saboda uwata ba za ta zartar da komi in ba yardar mahaifiyarta ba, ita ma kuma haka.

‘Ina ganin tun da wannan hutun mai sati biyu ne zan yi sati daya a Malumfashi in taho Kaduna domin na san dole Aliyu zai matsa ma su Mama Inki da kira”.

Sai Zahra’u ta nuna min jin dadin ta a game da abin da na fada. Ta gyara kwanciya ta juyo muna mai fuskantar juna, ta ce,

“Asiya na ga hotunan

‘yan’uwanki da samarinki, ke ma kin ga nawa da na mijina in Allah ya so wato Aminunlah, sai dai kuma Kawancen namu har yanzu cikin duhu yake, saboda ba mu san cikakken tarihin juna ba, ko ba mu yarda da zukatanmu ba ne?”

Na dube ta na yi dariya na ce, “No, no, ba haka ba ne, kin san a kullum ba mu da lokacin kanmu in ban da jiya da yau da muka kammala karatu, amma kakkabe kunnuwanki ki san yau ko wa ce ce Asiya Yusuf haifaffiyar Malumfashi ‘yar asalin Galadanci”.

Na kwance mata labarina kaf, tun daga kan mahaifina har zuwa rayuwar da Mama Inki ta fara tsoma, haka da al’amarina da Aliyu da yadda muke da Ibrahim, na rika neman amsa daga fuskarta a kan al’amarina da Aliyu. Muka yi shiru daga ni har ita ba tare da mun ce uffan ba, har na tashi na bude dirowar kayan abincinmu na dauko kwalbar tree top na bude na zuba mana a kofuna, na debo mana kilishi cikin faranti- irin kilishin da Ibrahim ya kawo mana, muna ci muna shan lemu.

Bayan mun gama sai Zahra’u ta dube ni ta ce,

“Yadda Aliyu ke nuna maki masifar so a wasikunsa wadanda na karanta, amma a ce har ya tafi bai aiko wa iyayenki da magabatansa ba, saboda mazan yau ‘yan zafin nema ne a wajen neman aure, ko da yake ina ganin ya yarda da ke, ya san Kila ba za ki taba sauraron kowa ba. Amma bari ya dawo mu ga yadda zai bullo wa sha’ anin

Na ce, “Ai fa sai dai mu sa idon, amma kamar yadda na gaya maki idan har na kammala wannan jami’ ar babu wata magana zan bar Ibrahim ya fito, kin ga a lokacin ai shi ba yaro ba ne zai dauki ganuwa, ni dai na ba shi hakkinsa har ga Allah. To, Zahra’ u ya ya zan yi da shi?”

A daidai wannan lokaci sai na ji idanuwana sun kawo Kwalla. Zahra’u ta ce, “Ke ma kin yi tunani, na san ma kafin mu gama zai yi mai yiwuwa”

Daga nan zaharau ta gyara zama tace ni kuwa asiya tsaya kiji yaddah tarihina yake da kikaji ana kirana zahrau ahmad wannan sunan kakana ne wanda ya haifi mahaifina sunansa malam amadu mai gini yana zaune a garin funtuwa tsoho ne wanda Allah ya albarkace shi da mata daya mai suna binta da yaya biyu rak

Baba sule shine babba daga nan sai babana mai suna musa dagasu bai sake haihuwa ba bashi da wani sana,a illa wannan ginin da noma kamar yaddah kikace ne asiya boko a zamanin iyayenmu sai wanda Allah yasa yanada rabon arziki da wannan hanyar ake sakawa makaranta boko to nima haka abin yake wajen iyayena basu da ilmin boko saina mahammadiyyah

Kwanci tashi da karfi ya kawo musu sai suka fantsama cikin neman na kansu inda babana ya doshi kano baba sule kuma ya doshi kaduna ya eika siyar da yan kunne a irin akwatinnan na gilashi har jarinsa yayi karfi ya kama hayar shago yana saye da sayarwa yana nan har Allah ya hadashi da abokiyar rayuwa wata yar fulanin yola ce su

Hmmm

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE